bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:21:30
Tabbas batun haxin kan al’ummar musulmi wajen tun karar maqiya abu ne mai kyau matuqa, amma hakan kuma ba yana nufin a jefar da Aqidar asali ta addinin ba, munsamman tunda mun yarda cewa ta hanyar ladabi da magana mai kyau zamu iya tabbatar da alaqa mai kyau tsanin mu za kuma mu iya tattauna savanin da ke sakanin mu, amma bata hanyar watsar da aqidun mu ba
Lambar Labari: 117
Da sunan Allah mai Rahama mai jin qai!!
                                                 
Tun Bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) Musulmi suka kasu gida biyu. Da vangaren da suke da aqidar cewa Manzon Allah (s.a.w) kafin rasuwarsa bai naxa wanda zai gajeshi ba, wato sunna. Da kuma vangaren da suke cewa lamarin bahaka yake ba, lallai Manzon Allah (s.a.w) ya sanar da al’ummarsa wanda zai gaje shi. Duk da cewa a duk waxanan vangarorin kowa ya ruwaito ruwayoyi daban-daban akan wannan lamarin.
      Wannan savani ya samo asali ne tun bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w), kuma haryanzu yana ci gaba a wannan zamani namu, tsakanin vangarori biyun na al’ummar musulmai, wato shi’a da sunna. A inda Waxansu ke ganin miyasa al’ummar musulmi ba zasu aje wannan savanin ba wanda yake tsawun tarihin Musulunci kusan qarni sha huxu zuwa sha biyar, mai makon haka su haxa kansu wajen tunkarar maqiyansu da suka sako su a gaba. Shin ba zaifi kyau ba  al’ummar musulmi su watsar da wannan savanin mai makon haka su rungumi juna su maida hankali kan matsalar da tasawu su gaba a yau ba? Bayanin wannan ishkalin za a iya bada amsa biyu:
   Na farko: Haqiqanin gaskiya savani tsakanin Ahlussuna da shi’a bai ta qaita ga matsalar shugabancin al’ummar musulmai ba kawai, akwai wasu batutuwa da suka haxa da Fiqihu, kalam da Tafsiri da zamu iya kaiwa kansu. Zamu iya yin tambaya kamar haka: Shin Ubangiji zai zavawa mutane wanda zai shugabance su? Ko kuwa mutane ne zasu zavawa kansu wanda zai Jagorance su? A wani bayanin na daban kuma zamu ga cewa lokacin da ake da savanin fahimtar addini tsakanin vangarori biyu ko wane vangare yana da’awar cewa shi ne kan dai dai tofa babu makawa tsananin waxannan vangarorin akwai wanda yake akan gaskiya da shiriya akwai kuma wanda yake akan savanin haka tsakanin vangare biyun, wanda hakan yana yin nuni da dole a  samu vangaren da yake kan gaskiya ya kuma xoro akan shiriya da sa’ada. Ga misalin wannan sanan nan hadisin, wanda Abdullahi xan Amru ya ruwaito, ga hadisin kamar haka:عن عبدالله بن عمر وقال: قال رسول الله(ص) ليأتين علي أمتي ماأتي علي بني إسرائيل حذوالنعل,...وإن بني إسرائيل تفرقت علي نثنتين وسبعين ملة وتفترق أمتي علي ثلاث وسبعين ملة كلهم في النار إلاملة واحدة...)) (An kanrvo daga Abdullahi xan Amru yace: Mazon Allah (s.a.w) yace: Da sannu al’umata zata zo da irin abinda Bani isra’ila suka zo da shi na qungiyoyi daban daban…. Tabbas Banu isra’ila sun rabu gida saba’in da biyu, kuma al’ummata zata rabu kaso saba’in da uku, dukkan su yan wuta ne sai ungiya xaya ce kawai zata tsira)(1) .
      Kaga a she kenan duk lokacin da kaga mutane suna da savanin fahimtar wani abu musamman lamarin addini ya zama dole a samu wanda yake akan dai dai da kuma wanda ya kauce hanya.
   Jawabi na biyu: Tabbas batun haxin kan al’ummar musulmi wajen tun karar maqiya abu ne mai kyau matuqa, amma hakan kuma ba yana nufin a jefar da Aqidar asali ta addinin ba, munsamman tunda mun yarda cewa ta hanyar ladabi da magana mai kyau zamu iya tabbatar da alaqa mai kyau tsanin mu za kuma mu iya tattauna  savanin da ke sakanin  mu, amma bata hanyar watsar da aqidun mu ba.
      Ala ayya halin mafi kyawun hanyar sanin Ubangiji itace hanyar Iyalan gidan Annabi (s.a.w) wato Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar wilaya garesu da sallama masu wanda  ba inda zamu iya samun wannan sai a makaranta ta shi’a kawai, wacce itace take koyar  da sanin Allah da Manzonsa tare da  Iyalen gidan Annabi da  tabbatar da wilayarsu (a.s).
          Imamanci
Imamanci a wajen yan shi’a yana daga cikin shika-shikan musulunci kamar Annabci, shi ma ci gaba ne na aikin Annabci. Imamanci yana daga cikin wajibai na addini sakamakon wasu abubuwa da suke tattare da shi da ba za a iya wadatuwa  daga gare su ba kamar shiryar da mutane da tsarkake ayyukansu da kuma tsara tsarin rayuwa ta duniya da lahira. A nan za mu yi  taqaitaccen bayani kan wasu lamura da suke da alaqa da Imamanci kamar yadda ‘yan shi’a suke gani.
  Wannan kalma ta Imama a luga tanada ma’anar shugabanci,  Imam shine wanda yake shugabantar mutane ko dai mai shiryarwa ko kuma akasin haka. Misali a wannan ayar ta surar isra’i aya ta:71, in da Allah maxaukakin sarki yake cewa:(((يوم ندعوا كل أناس بإمامهم))(2) .{ A ranar da muke kiran ko wanne mutane da Imaminsu} saboda haka ita wannan kalma ta Imam ma’anarta zata iya zama shugana na kirki ko kuma savaninsa, ga wani misalin duk dai daga Alqur’ani mai girma, inda Allah yake cewa: وجعلنا منهم أئمة يهدون بأمرنا))))(3) .{ kuma mun sanya shugabanni cikinsu, suna shiryarwa da umarninmu, surar sajada aya ta: 24}. Da kuma :    وجعلنا هم أئمة يدعون إلي النار))))(4) .{ kuma mun sanya musu shuganni masu suna kira zuwa  ga wuta, qasas: aya ta: 41} saboda haka idan muka kula da  waxannan ma’anonin daban daban zamu ga cewa akwai shugaba mai shiryarwa akwai kuma wanda zaija muttane  zuwa vata.
     Saboda haka Imamanci da Nassi ake tabbatar da shi. ‘yan shi’a sun yi imani cewa Imami ba ya zama Imami sai da nassi daga Allah maxaukakin sarki. Shi ne ke zavan wanda ya so daga cikin bayinsa salihai ya xora shi a wannan matsayi, ba wai zavi ne na mutane ba, wanda a mafi yawan lokuta baya ma la’akari  da maslahar al’umma ta gaba xaya, wanda a mafiya yawan lokuta yana karkata kan kwalayi da son rai da kuma savawa maslahar al’umma. A haqiqanin gaskiya matsalolin da Duniyar musulmai ke muskanta a yau sun samo asali ne sakamakon raba halifanci da nassi da aka yi  tun a farko.
                          Savanin shi’a da sunna akan ma’anar Imama a Isxilahi.
     A wajen bayyana ma’anar Imam tsakanin shi’a da sunna akwai matuqar savani, shi’a dai sunada Aqidar cewa Imam yana nufin magajin Manzon Allah (s.a.w) bayan wafatinsa, shine zai ci gaba da gudanar da al’amuran da Annabi yake gudanarwa bayan Rasuwarsa kamar shiryar da mutane da hukunci tsakanin su. Saboda haka gaba xaya ayukan Annabi Imami ne zai ci gaba da gudanar dasu, saboda haka ne ma Imami zai zama yana da sifa irinta Annabi, wato kamar yadda Annabawa Allah suke tsarkakakku shima zai zama kamar haka kenan, sannan kamar yadda Allahne ya zave su shi ma Imami zai zama wanda Allah ya zava,  ban bancinsa da Annabi kawai Annabi ana yi masa wahayi shi kuma Imami ba’a yi masa wahayi, sai dai Ubangiji yana bashi wani Ilimin na musamman, sannan kuma ya kare shi daga dukka nin wani savo, kamar yadda Allah ya kare Annabawansa daga aikata dukkanin wani savo, wato dole Imami zai kasance yana da cikakkiyar kariya kamar yadda Annabawa sukeda cikakkiyar kariya daga Allah maxaukakin sarki daga aikata duk wani savo.
Wasu qungiyoyin musulmi suna zargin ‘yan shi’a saboda Imanin da suka yi kan Ismar Imami (wato kauce wa ai kata savo) harma a na ganin ‘yan shi’a suna wuce gona da iri wajen tsarkake Imamansu (a.s), magana ta gaskiya batun tsarkin Imamai abu ne wanda yake a fili duk mai cikakken hankali zai iya fuskantar hakan koda babu nassi.
   Amma a wajen Ahlussunna abin ba haka yake ba, su suna ganin cewa Imami shi ne wanda yake jagorantar al’amuran mutane ko dai na addini ko kuma na Duniya, sannan al’amarin  Imami ba daga vangaren Ubangiji yake ba, Imami zai kasance ne wanda yasamu mulki ta ko wacee hanya, mutane ne suka haxu suka zave shi ko kuwa ta qarfi da yaji ta hanyar makirci ya samu mulki to yazama shugaba (Imami). Saboda  haka ne ma suke cewa Imami bashi da wasu siffofi ayyanannu, ko wace irin akida ce dashi sannan ko tawa ce hanya ya samu shugabancin shugabane na musulmi ko waninsa, muhimmi a wurin su shine kafa hukuma, hukumar kuma kota wane iri  hali ya kafata wannan shine Imami a wujen  Ahlussunna.
Ismar Imami
A wajen ‘yan shi’a Imami dole ya zama wanda baya ai taka savo da yin kuskure a cikin ayyukan sa da maganganunsa kamar yadda Annabawa suke, ‘yan shi’a nada  hanya biyu  ne wajen tabbatar da Ismar Imami ko dai ta hanayar dalili na hanakali ko kuma ta hanayar ruwaya.
  Dalili na hankali akan Ismar Imami: mutum yana da muqatar zuwa ga cikar kamala da shiriya da zata kai shi zuwa ga sa’ada, saboda haka dole yana da  buqatar samun wanda zai taimake shi  zuwa ga wannan kamala din, ma’asumi shi ksxsi wanda zai  iya yin wannan aikin shiryar da shi zuwa ga wannan matsayin, wannan aikin ma’asumi ne akwai zai iya yin shi. Na farko: Dole wanda zai shiryar da mutane ya zama  yana da shiriya wato shiryayye ne. Na biyu: Wanda yake ba  shi da shiriya ba zai iya shiryar da mutane ba. Na uku: Dole Imami ya zama mai shiriya ne wato ma’asumi ( wanda baya savo ). Idan muka kula da kyau da waxanan bayanan zamu ga cewa tabbas ba wanda zai iya kai mutane zuwa ga shiriya da sa’ada sai wanda yake yana da shiriyar a hannunsa, ma’anar shiriya a hannunsa shine wanda shiriyarsa daga Allah maxaukakin sarki take shine ya zave shi saboda wannan aikin.
Bayani ba biyu wato dalili na ruwaya.
Ayoyi da hadisai da dama sun tabbatar da Ismar Imamai (a.s), a nan zamu taqaita da aya xaya ko biyu kawai domin tabbatar da waannan maganar. A cikin Alqur’ani mai tsarki Allah yana cewa:
ياأيهاالذين ءامنواأطيعواالله وأطيعواالرسول وأولي لأمرمنكم)) )) { Ya ku waxanda suka yi Imani ku yi wa Allah xa’a  kuma ku yi wa Manzonsa xa’a da kuma shuganni daga cikin ku}(5) . Idan muka lura da bayanin wannan ayar mai girma Ubangiji maxaukakin sarki ya cakuxa yi masa xa’a da manzonsa da kuma shugabanni wanda hakan yana nufin ba ko wanne irin shugaba Allah yake umarni  da yi masa biyayya ba, tunda har Allah yayi umarni da ayi musu xa’a tofa dole su zama wanda basa savawa Allah da dukkanin ma’ana wato dole su zama ma’asumai. Idan kuwa waxannan shuwagabannin basu zma ma’asumai ba, hakan yana nufin Ubangiji da kan shi ya umarci mutane da su yi biyayya akan savo da kuskure kenan, wanan kuma tabbas yana nufin Ubangiji ya xora mutane akan hanyar vata kenan (wa’a yazu billah), mu kuma munsan cewa Allah mai Hikima ne ba zai tava yin wani aiki wanda babu hikima a cikinsa ba. Ubangiji mai hakima tunda yayi umarni da ayi musu xa’a cikakkiya to ba makawa ma’asumai ne ( wanxanda basa savo), a nan hankulin mu zai hukunta cewa Imamai ma’asumai ne, kaga wannan dalili ne na hankali da yazo a cikin  qur’ani mai girma. A ya ta biyu kuma akan batun jarabawar da Allah maxauki yayiwa Annabinsa Ibrahim (a.s) ne inda Allah yake cewa:
{{ وإابتلي إبراهيم ربه  بكلمات فأتمهن قال إني جاعلك للناس إماما قال ومن ذريتي قال لا ينال عهدي الظالمين))
(( Kuma ka ambaci lokacin da Ubangijin Ibrahim ya jarrabe shi da wasu kalmomi sai ya cika su, sai yace: Ni zan saka Imami ga mutane (shugaba), sai yace: hadda zuriya ta? Sai yace: Alqawarina baya riskar azzalumai))(6) . Wato a nan zamu iya fahimtar cewa a she bayan Annabta ma akwai wani matsyin kenan, wanda har Annabi Ibrahim yayi burin Ubangiji ya bawa zuriyar sa wanan matsayi amma Allah maxauki yace alqawarin sa baya irkar azzalumai. Saboda haka al’amari na shugabanci lamari wanda yake daga Allah ne bata wata hanya ta ban ba, Allah ne ke zavan wanda yaso ya kuma ba shi matsayin.
Wajabcin riqo da Imamai
 Shi’a sunye imani da wajabcin riqo da kuma qaunar Imamai (Ahlulbait (a.s) ) saboda Nassi da yazo daga Alqur’ani mai girma kamar faxin Allah maxaukakin sarki inda yake cewa:{{ قل لا أسألكم عليه أجرا إلاالموة في القربي}} [ Bana tambayar ku wata lada a kansa face soyayya ga makusanta](7) . Da makamantan irin wanann aya daga cikin sunna ( hadisai) kuwa akwai ingantattun hadisai irin su hadisin (nauyaya biyu), wato faxin Manzon Allah (s.a.w) cewa: Ya ku mutane! Ni zan barku ku kuma za ku same ni a bakin tafki, zan tambaye ku idan kuka haxu da ni kan saqalaini, don haka ku kula da yadda za ku halifance ni kansu. Sai kuka ce: mene ne saqalaini ya Manzon Allah? Sai ya ce: Babban mai nauyi shi ne Littafin Allah wanda vangarensa guda yana hannun Allah xaya vangaren kuma yana hannunku, ku yi riqo da shi ba za ku vace ba sai kuma zuriyata mutanen gidana(8) .
       A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w) ya lamuncewa duk wanda yayi riqo da Alqur’ani mai girma da kuma iyalan gidansa tsarkaka waxanda basa aikata savo ko wanne iri cewar ba zai vata daga hanyar shiriya ba har abada, ya sanya su tamkar abu guda a matsayin masdarin shiriyar al’umma da sa’adarta a duk tsawun rayuwa. A she kenan riqo dasu da qaunar su ya zama waje bi a gare mu musamman idan muna son tsira duniya da Lahira, saboda sune zasu kai mu zuwa ga tsira da sa’ada.
                                       AYYUKAN IMAMAI
  Munyi bayani a baya cewa a Akidar shi’anci Imami shine wanda zai gaji Annabi kuma gaba xaya ayyukan Annabi na shiryar da al’umma yanzu sun xuro kan Imami, wannan bayanin baya buqatar wani dalili, a yanzu zamu shiga bayani akan ayyukan da suka hau kan Imami ne.
           MUHIMMAN  AYYUKAN  DA SUKA HAU KAN  IMAMI
                     Na farko: koyar da addini da kuma kariya gare shi.
Manzon Allah (s.a.w) shine cikamakon Annabawa da Allah ya aiko da addinin  musulunci wanda hukunce-hukuncen shi zai ci gaba da kasance har ranar sakamako. Kamar yadda Imam Sadiq yace:
{{حلال محمد حلال إلي يومالقيامة وحرامه وحرامه حرام إلي يومالقيامة }} [ Abin da Annabi (s.a.w) ya halatta halal ne harzuwa ranar qiyama, haka kuma abin da Annabi ya haramta haramne har zuwa ranar qiyama]. Haqiqannin gaskiya Manzon Allah (s.a.w)  shine cika makon Annabawan Allah kuma yayi shekaro ishirin da biyar (25) ne  kawai tsakanin aiko shi zuwa wafatinsa, wanda a wannan shekarun ne aka kammala addinin musulunci, musulunci da hukunce-hukuncensa koda yaushe akwai buqatuwan bayani saboda canzawar zamani, wato musulmai  suna buqatar wanda zai yi musu bayinin irin wanda yayi dai dai da zamanin su, saboda maganar gaskiya lokacin da manzon Allah (s.a.w) yayi domin koyar da  mutane tabbatas ba zai gamsar ba, wajen game ko wane zamani , bugu da qari kuma har bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) addinin musulunci ba zamu iya cewa ya shi ga ko wane lungu na wannan Duniyar ba. Saboda haka xaya daga cikin abinda yake da matuqar mahimmanci daga cikin ayyukan Imami shine koyar da hukunce-hukunce  da tarbiyantar da mutane domin su kai zuwa  ga sa’ada da kamala.
     Tunda dai addinin musulunci shine qarshen  addinan wanda Ubangiji ya aiko kuma wannan addinin shine zai kasance har zuwa ranar qiyama, to yana buqatuwa da koyar da Xan Adam  akansa kuma wanda  zai koyar  da shi xin  dole ya zama wanda baya savo ne, wanda kuma baya savo ba kuwa bane sai ma’asumi shine zai ci gaba da kare addinin da umar nin Allah maxaukakin sarki.
                                   Na biyu: yiwa mutane tarbiya.
 Munsan cewa Ubangijin mai hikima ne wannan xaya daga cikin siffofin Allah maxaukakin sarki shi ne hikima, ma’ana Allah mai hikima bayayin wani aiki wanda bashi da hadafi akansa. Xaya daga cikin hikamar Ubangiji shine halittar xan Adam da yayi, saboda haka a cikin halittar xan Adam akwai manufa da yake da ita. A littafi mai tsarki Allah yayi bayinin manufar da tasa ya halicci xan Adam shine domin xan Adam ya kai ga kamala. Manufar kaiwa ga kamala anan shine mutum yayi quqari duk wani aiki mai kyau yayi shi.
     To haka yake kafin ma ace munyi qarin bayani a fili yake  xan Adam shi kaxai ba zai yiwu ya kai ga wannan sa’ada da kamalar da Ubangiji yake nufin ya kai ba tare da luxufi daga Allah ba. Da wannan dalilin ne Allah maxaukakin sarki ya aiko Annabawa domin su koyar da xan Adam su kuma shiryar da shi zuwa ga hanyar sa’ada, duk da haka wasu daga cikin mutane sakamakon sha’awance-sha’awance irin na xan Adam suna kau cewa daga kan hanyar sa’ada kuma su kasa isa ga waccan kamalar. Saboda haka ne ma xaya daga cikin muhimmin aikin Imami shi ne ci gaba da yiwa mutum tarbiyya da kuma dawu da su kan hanyar sa’ada da hana su karkacewa  zuwa vata.
       Imami domin yiwa mutune tarbiyya hanya biyu yake da ita: 1 koyar da addinin yanda yake da  Bayani a kan dokokin Musulunci da Aklaqi, da kuma yiwa mutane nasiha domin su kai ga waccan kamalar. 2- Imami zai zamo yana aikata dokokin musulunci kamar yadda suke domin mutane su gani suyi koyi dasu, wannan itace mafi muhimmancin hanayar  koyarwa zuwa ga sa’ada da kamala.
                        Na uku: Jagorantar al’ummar musulmai.
    Mutum halitttace wacce take buqatuwa  da wata halittar kwatan kwacinta domin rayuwa, wanda da yawa wasu daga cikin halittu basu da irin wannan siffar irin ta xan Adam, zai yiwu suyi rayuwar su batare da buqatuwa zuwa ga xayan su ba. Misali Bishiya ba dole bane saita rayu a daji cikin yan uwanta Bishiyoyi, sannan hakan ba zai cutar da ita ba don bata rayuwa cikin daji ba, zai yiwu taci gaba da rayuwarta a ko ina. Amma mutum yana muqatuwa zuwa ga mutum xan uwansa wato irin nau’insa.
     Ta wani vangaren domin aikin juna yayi dai dai mutum yana buqatar shugabanci ta yadda mutum ba tare da shugaba ba ba zai yiwu yaci gaba da kasancewa ba, tambaya anan itace shin waye ya kamata ya zama shugaba? Shin ko wane irin  mutum zai iya zama shugaba kenan? Ko kuwa sai wanda yake Adali mai kamala Jarumi wanda yake ba shi da tsoro, sannan wanda yake a kan hanya miqaqqqiya? Ko kuwa ko wane Ja’iri fasiqi Azzalumi Matsoraci karkatacce zai iya zama shugaba? Ba shakka nasan a nan amsar zata kasance akan waxancan siffofin na farko, saboda dole a yayin da shugaba ke shugabanci ana buqatar ya zama mai irin waxan can siffofin na farko da muka ambata, saboda da wannane mutane zasu natsu da shi sannan kuma suyi masa biyayya, domin yi masa biyayya yiwa Allah biyayya ne. shiyasa ma Allah maxaukakin sarki a littafinsa mai girma yake cewa:{{ Ya ku waxanda sukayi Imani kuyiwa Allah Xa’a da Manzonsa da kuma shugabanni daga cikin ku}}(2) .
      Bugu da qari musulunci yana da Dokuki wasu daga ciki xai xai kun mutane wasu kuma gaba xaya abin da ya shifi mutane xin. Wannan a fili yake cewar dokukin da suka shafi mutane gaba xaya abu ne da yake da buqatar hukuma, saboda wannan dalilan shugaba ga musulmai ya kamata ya kasance Annabi ko kuma magajinsa ta yadda waxannan dokukin zasu tafi dai dai, domin wanda ya kamata a yiwa biyayya da umar nin Allah dole ya kasance mutum ne na musamman ba wai ko wane irin mutum ba. Wannan mutumin kuma dole ya kasance wanda baya savo tsarkakakke ne daga Allah maxaukakin sarki wanda ba kowa bane sai ma’asumi wanda baya savo.
   Dodiya ta tabbata ga Allah Ubangijn da ya aiko wa Xan Adam da shiriya, tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Fiyayen halitta Annabi Muhammad (s.a.w) da Iyalan gidansa tsarkaka waxanda Allah ya kare su daga dukkanin datti. A minci ya tabbata ga muninai waxanda suka bi shiriya.

Aliyu Abdullahi Yusuf.
Whatsapp, telegram instagram Number: +2348037493872.
    s

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: