bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:23:30
atan ramadan daya ne daga cikin watanni masu alfarma wadanda Allah mdaukaki ya kebance su da wasu fifice- fifice, wanda daga ciki akwai cewa: shi wata ne da aka haramta zubda jinni a cikinsa (yaki)
Lambar Labari: 118
  Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Watan Azumin Ramadhan Watan Gafara Da Rahama
Allah Ta’ala Ya Kira Ku zuwa Liyafa Ta Musamman

Watan ramadan daya ne daga cikin watanni masu alfarma wadanda Allah mdaukaki ya kebance su da wasu fifice- fifice, wanda daga ciki akwai cewa: shi wata ne da aka haramta zubda jinni a cikinsa (yaki), dss.
Ruwayoyi masu yawa sun zo a kan falalar wannan watan mai albarka, hakika Allah Ta`ala ya cika shi da dumbin falaloli domin ya zama cikakkiyar dama a gare mu, mu masu  zunubai, shi ne watan da dararen sa suka  fi kowane dare, awoyin sa suka fi kowace awa, hakika Allah ya kira mu zuwa liyafarsa a cikin sa, kuma an sanya mu a cikin sa daga cikin ma`abota karamcin ubangiji. Numfashinmu a cikinsa tasbihi ne, barcinmu kuma ibada ne, ayyukanmu ababbna karba ne, kuma addu`o`in mu ababn amsawa ne.

)هو عند الله أفضل الشهور وأيامه أفضل الايام ولياليه أفضل الليالي وساعاته أفضل الساعات هو شهر دعيتم فيه إلى ضيافة الله وجعلتم فيه من أهل كرامة الله أنفاسكم فيه تسبيح ونومكم فيه عبادة وعملكم فيه مقبول ودعاكم فيه مستجاب(

Hakika na ga ya dace in fitar da hukunce-hukuncen azumi a dunkule, duk da karancin lokacin. Amma wanda yake neman Karin bayani ya nemi: (fassarar littafin (احكا م الاسلام ),  zuwa hausa ko ya koma zuwa karatuttuka da jawaban Allama Shekh Hafiz Muhammad wanda yake turawa ta hanyar sadarwar telegram ko kuma site don samun karin bayani.

Azumi da hukuncen-hukuncensa.
Za`a iya kasa su magana kan azumi da hukunce- hukuncensa da abubuwan da suke bata shi
zuwa kashi biyar:-
1. Kashe-kashen azumi
2. Sharadan sa.
3. Masu bata shi.
4. Ramuwa.
5. Fatawoyi, duk da cewa wannan kason na karshe zai yi wahala mu samu yin Magana a kan sa saboda karanci lokaci.

1->Na farko kashe-kashen azumi.
Azumin ya kasu zuwa kaso hudu.
I. Wajibi, ko dai ya zama, mai zaman kamar azumin watan Ramadan, ko kuma ya zamo wanda wani abu ke sa ya zama wajibi kamar Azumin bakance, da na kaffara dss.
ii. Mustahabbi, shi ma, ko dai ya zama ayyanan ne kamar na alhamis da juma`a da rajab dss, ko wanda ba ayyanan ne ba, shi ne dukkanin azumin da ba na wajibi ko mustahabnbi ko makruhi, ko kuma wanda aka haramta ba.
iii. Makruhi, kamar bako ya yi azumi ba tare da izinin wanda ya sauke shi ba.
ib. Haramtacce, kamar yin azumi ranar idoji guda biyu, (Sallar cin abinci da ta layya).
2-> Sharadan azumi sun kasu zuwa kaso biyu, akwai na wajibci da na inganci.
Amma sharadan wajabcin sun hada da,
i.    Balaga da hankali
ii.    wofinta daga haila da na biki.
iii.    Rashin cutuwa da kuma rashin lafiya.
iv.    Rashin yin tafiyar da take wajabta yin kasaru.
Sharadan ingancin sun hada da
i.    kari a kan sharadan da suka gabata akwai
ii.    musulunci da imani
iii.    Niya, kuma lokacin ta yana zarce wa har zuwa karkatar rana, idan har a kwai uzurin da ya hana shi yin ta da wuri.
3-> Abubuwan da suke bata azumi
1-2 Ci da sha 3- fitar da maniyyi 4- yin alura ta ruwa 5- ganganta yin amai, 6-ganganta wanzuwa da janaba har zuwa alfilir 7- nutsar da kai a cikin ruwa bisa itayadi 8- shakar kura mai kauri har ya isa makogwaro 6- jima’i wanda ya yi da wanda aka yiwa. kuma baya baci ta hanyar mantuwa da kuma fin karfi, amma yana baci ta hanyar tilastawa, 10 ganganta yiwa Allah Ta’ala da manzo (saw) karya da imamai da sauran manzanni [A. S.]
4->Ramuwar azumi
Ramuwar azumi nau’o’i uku ne,
1) Wannan ramuwa ta kasu zuwa kashi bakwai
A. Ramuwar da ba kaffara
i] Da mai janaba zai yi barci na biyu ko na uku kuma barcin nasa ya ci gaba har alfijir ya bullo tare da cewa yana da niyyar yin wanka .
11, Da zai bata azumin sa ta hanyar yin niyyar yanke azumin ko kuma saboda riya, tare da cewa bai aikata wanji abu da yake karya azumi ba .
iii. Idan ya yi wani abu da yake karya  azumi kafin ya lura da cewa alfijir ya  keto, sai kuma ya gano cewa ya riga ya bullo.
ib. Idan ya manta da wankan janaba har  kwana daya ko har kwanaki suka shude masa.
B. Ci bisa dogaro da labarin cewa yanzu dare ne alhali alfijir ya keto.
b1, Ci bayan mai labari ya ba shi labharin bullowar alfijir, a bisa kudirewar sa cewa izgilance yake masa.
B11, ci abinci ta hanyar dogaro kan labarin cewa rana ta fadin alhali  bata fadi ba, idan mai bada labarin ya zama wanda  za`a iya dogaro  da labarin sa ne.
biii. Cin abinci saboda ya yi yakinin dare ya yi ashe bai shiga ba tare da cewa babu wani dalili da aka samu a sama.
ib. Zarcewar ruwa zuwa cikin makogwaro bayan shigar da shi cikin baki, domin kuskurar shi ko sanyaya shi.
b. Ramuwa tare da kaffara (babba)
I. Zuwa da abin da yake karya azumi da gaggan, banda amai, kuma bisa ihtiyadi idan mutum ya nutsar da kansa cikin ruwa da kuma allura kuma bisa fatawa a cikin sauran, amma ganganta amai baya wajabta kaffara.
II. Kaffara it ace `yanta wuyaye (bawa ko baiwa) ko azumtar watanni biyu ko ciyar da miskinai sittin kuma ba`a maimaita kaffarar da maimaituwar abin da yake wajabta ta a cikin rana guda, koda jinsin ta ya bambanta.
C. Ramuwa tare da kaffara da ta`aziri.
Da zai tara da matarsa cikin watan Ramadan da rana alhali su biyun suna azumi, idan ya zama ya tara da ita tare da yardarta, to kowanne daga cikin su za`a yi masa bulala ashirin da biyar, sannan ya yi kaffara, idan kuma tilastata ya yi, zai dauke mata kaffara da ta`aziri.
D. Ramuwa tare da zuwa da dukkanin kalolin kaffara
Da zai yi kalaci da abin da aka haramta a watan ramadana, wajibi ne ya zo da dukkanin kalolin kaffara guda uku.
E. ramuwa ba tare da kaffara ba.
1. Tsoho/tsohhuwa da mai cutar kishirwa idan ba za su iya yin azumin ba wajibi ne su rama azumin ba tare da kaffara ba idan har suka sami dama ma’ana (za su iya).
ii. wanda ya ci saboda wani uzuri kamar tafiya, sai uzurin ya ci gaba har zuwa wani azumin, ramuwa kawai zai yi.
F. fidiya (fidda`u).
1). mai ciki makusanciya da mai shayarwa mai karancin nono, da ace azumin zai cutar da su ko ya cutar da yayan su.
ii. kaffarar ta su, ita ce su bada uku bisa hudun kilo na abinci.
G. Ramuwa tare da fidda`u
i. wanda ya ci saboda rashin lafiya kuma yanayin ya ci gaba da shi har zuwa wani ramadanan, ya yi kaffara da mudu daya a maimakon kowace rana, kuma ramuwar ta saraya.
2) Hukunce-hukuncen ramuwar watan Ramadan.
i. bai halatta a jinkirta ramuwa zuwa wani watan na Ramadan bisa zabi ba.

11, idan ya jinkirta da gangan, ya yi sabo, kuma ramuwar zata zamo tare da kaffara mudu daya a kowace rana.
111, Ya halatta a ciyar kafin karkatar rana idan har ba zai takura \ kuntata ba
1B, Idan ya karya azumin bayan karkatar rana ya yi sabo kuma kafafra ciyar da miskinai 10 ta hau kansa, idan kuma ba zai iya ba sai ya yi azuin kwana uku.
B. Ya wajaba ga waliyyi ya rama abin da ya tserewa mamacinsa wanda rama shi ya zama wajibi, banda wanin sa, waliyyi a nan shi ne: Babban da namijia cikin `ya`yan da mahaifin su ya rasu ya bari,
3) Wadanda ramuwa bata wajaba a kan su ba.
I. Mahaukaci da wanda ya suma bai wajaba su rama azumin da suka sha ba a lokacin da suke cikin uzuri .
II. Kafiri na asali, ba zai rama abin da ya sha a lokacin kafircin sa ba.
III. Basunne bayan da ya yi istibsari, ba zai rama abin da ya yi daidai da mazhabarsa da ko mazhabar da ya koma ba.
IB. wanda ya balaga da rana, koda kuwa ya kasance kafin karkatar rana ne, ba wajibi ba ne ya yi azumin wannan wunin ba, kuma ba zai rama shi ba.
B. Wanda azumi ya kubuce masa a cikin watan Ramadan saboda rashin lafiya ko haila ko biki, sai ya/ta mutu kafin watan (ramadanan da yake ciki) ya kare  .

Hukunce-hukuncen Azumi
(daga cikinlittafin Ahlamul Islam)
"Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku”.
 142> Azumi ya wajaba a bisa dukkan musulmi baligi a cikin watan ramadan, kuma daya ne daga cikin mafi muhimmancin ibadu a musulunci. Azumi shi ne kamewa daga dukkan abin da yake bata azumi tun daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana na shari’a da nufin neman yardar Allah (S.W.T).
 143> (m.1577)     Ba wajibi ba ne azumtar ranar kokwanto wacce ba a san cewa, shin karshen sha’aban ce ko kuwa farkon Ramadan. Da zai yi nufin azumtar ranar bai halatta ba a gare she ya yi nufin yin azumin Ramadan yana mai ayyanawa ko kuma da nufin yin azumi tsakanin Ramadan ko sha'aban. Don haka wajibi ne gare shi ya yi niyyar ramuwa ko makamancinta, idan daga baya ta bayyana cewa tana daga cikin Ramadan sai ya kididdiga shi daga cikinsa.
 144> (m.1581) Masu warware azumi su ne:
 1, da 2- Ci da Sha, kai tsaye ko da kuwa kadan ne;
 3- Jima’i;
 4- Yin karya ga Allah (S.W.T) Ko Manzo ko Imamai (A.S);
 5- Shigar kakkaurar kura zuwa makoshi/makogwaro;
 6- Nitsar da kai a cikin ruwa;
 7- Wanzuwa da janaba, ko haila ko jinin biki (nufasi) bayan tsarkaka daga gare su har zuwa alfijir;
 8- Istimna’i; (kokarin fitar da maniyyi ta kowace hanya)
 9- Allura ta ruwa;
 10- Yin amai da gangan;

 145> (m.1662) Idan wani mutum ya zo da daya daga abubuwan da aka ambata, da gangan da kuma zabi, to azuminsa ya baci, idan kuwa da rafkanwa ne, to babu komai (kuma azuminsa yana nan).
 146> (m.1664) Idan aka zuba wani abu a bakin mai azumi ta karfin tsiya to azuminsa bai baci ba, amma idan aka tilasta shi a kan hakan ta hanyar tsorata shi da cutarwa ta bangaren dukiya ko ta jiki sai ya ci saboda tsoron abin da zai biyo baya, azuminsa ya baci.
 147> (m.1669) Kaffarar yin abin da yake bata azumi da gangan a cikin watan ramadan, ga wanda azumi ya wajaba a kansa ita ce; bayan ya rama azumin zai yi dayan abubuwa uku:-
 1- 'Yanta baiwa/bawa;
 2- Ko azumin watanni biyu jerarru;
 3- Ko ciyar da miskini sittin.
 148> (m.1674) Wajibi ne yin dukkanin kaffarorin guda uku, da suka gabata, idan ya karya azumi da haram, idan kuma bai iya rama dukkan kaffarar da take kansa ba to ya wajaba ya yi iya yinsa.
 149> (m.1673, dab) Azumi ba ya wajaba a yanayoyi masu zuwa, daga cikinsu akwai:-
1-    Maras lafiyar da azumi yake cutar da shi.
2-    Tsoho mai yawan shekarun da ba zai iya azumi ba.
3-    Mace mai ciki ko mai reno da azumi zai cutar da ita ko zai cutar da jaririnta, kuma wajibi ne a rama bayan gushewar uzurin.
 150> (m.1712) Idan bai yi azumi a ramadan ba saboda rashin lafiya, kuma ya wanzu har zuwa wani ramadan mai zuwa, to bai zama wajibi a gare she ba ya rama abin da ya tsere masa daga ramadan da ya wuce, don haka ya wajaba ya bayar da mudu (abin da ya yi daidai da kilogiram daya) na abinci ga miskinai na daga alkama ko sha'ir ko makamancinsu maimakon azumin kowace rana.
Amma idan bai yi azumi ba saboda wani uzuri na daban kamar tafiya kuma uzirin nasa ya yi saura har zuwa ramadan mai zuwa, to wajibi ne ya rama abin da ya tsere masa na Ramadan da ya wuce.
 151> (m.1713) Idan bai yi azumi ba a ramadan saboda wani uzuri sai uzurin ya gushe bayan fitar ramadan, kuma bai yi azumin ba da gangan har wani Ramadan ya zo, to wajibi ne ya rama ya kuma bayar da mudu na abinci maimakon kowace rana.
 152> (m.1748) Ya haramta yin azumi a ranar idi biyu.

Azumin Matafiyi
 153> (M.1723) Matafiyin da kasaru ta wajaba gare she bai halatta ya yi azumi ba. Amma matafiyin da yake cika sallarsa, kamar wanda sana'arsa ta kasance tafiye-tafiye, ko wanda tafiyarsa ta kasance ta sabo, to wajibi ne ya yi azumi a cikin tafiyarsa.
 154> (m. 1730) Idan mai azumi ya yi tafiya bayan karkatar rana to wajibi ne ya cika azuminsa, idan kuwa ya yi tafiya kafin karkatar rana wajibi ne ya sha ruwa, amma bayan ya isa gejin rangwame, wato wajen da ba ya ganin katangar garin ko ba ya jin sautin kiran sallarsa. Idan kuwa ya sha ruwa kafin ya isa wannan mahallin, to kaffara ta wajaba gare shi.
 155> (m.1731) Idan matafiyi ya isa garinsa kafin karkatar rana ko wani waje da yake nufin zama kwana goma, kuma bai yi wani abu mai karya azumi ba, ko abin da yake da hukuncin karya azumi, to ya wajaba ya azumci wannan ranar, idan kuwa ya riga ya yi abin da yake karya azumi, to azumin ranar bai wajaba a gare shi ba.


[Muna yi muku fatan alkhairi ]

Makomar bincike
Hiwaratun fikihiyya -        na   sayyid sa id alhakim
Uyunu  ahbarir ridha –      na   shek sudduk
Raudhatul wa izin -           na    alfattalun  nasaburi
Aljadid fi tadrisil fikihu-   na    ibrahim  dihini
Ahkamul Islam                na    Kulliyatu Usulunddin ta Allama Askari      

AMINCI YA TABBATA GA MANZO MUHAMMAD DA ALAYENSA DA SS.
MUNIR MUHAMMAD SA’ID.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: