bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:25:55
Magana kan imam Khomaini magana ce a kan wani kogi wanda ya gajiyar da alkaluman marubuta, da harsunan masu Magana da kuma tunanin masu tunani. An haife shi aranar da aka haifi sayyida Fatima (A.S) kuma Sunan sa shi ne: Ruhullah Almusawi Al-khomaini, wanda sunan sa ya yi dai dai da na Annabi isa (A.S), gidan su gida ne na ilimi da tarbiyya, kuma ya yi karatun addini mai zurfi har yakai ga zama marji’in addini
Lambar Labari: 120
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ka

MALAMAI MAGADA ANNABAWA NE.
IMAM KHOMAINI GORZON WANNAN KARNIN

 Kashi na daya
 Magana kan imam Khomaini magana ce a kan wani kogi wanda ya gajiyar da alkaluman marubuta, da harsunan masu Magana da kuma tunanin masu tunani. An haife shi aranar da aka haifi sayyida Fatima (A.S) kuma Sunan sa shi ne: Ruhullah Almusawi Al-khomaini, wanda sunan sa ya yi dai dai da na Annabi isa (A.S), gidan su gida ne na ilimi da tarbiyya, kuma ya yi karatun addini mai zurfi har yakai ga zama marji’in addini,
  Imam yana ganin wajabcin neman ilimi a kowane lokaci kuma ako wane mataki na rayuwa, don haka ma zaka ga rayuwar sa gaba daya ta tafi a wajan neman ilimi ne da kuma yada shi ga al’umma, kamar yadda ya kasance yana dora dukkan burinsa akan matasa da kuma karfafar su akan haka, ya zo a cikin wata wasiya tasa ta musamman ga matasa cewa: "ina yiwa matasa wasici da abu uku:
1-    Neman ilimi,
2-    Karatun alkur’ani, da kuma
3-    Motsa jiki.
Idan ka dauki ilimi zaka ga ya yi magan ganu akan sa, acikin mafi yawan zantukan sa, bana mantawa da abin da wani daya daga cikin abokai na kuma wanda ya shugaban ci daurar da mu ka yi a kum, ya k e gaya mana cewa bayan da aka kare yakin Iran da Irak  ya umarci kowa da ya koma makaranta, sannan ya ware wa wannan bangaren makudan kudade.  
Ya zo a cikin maganganun sa a kan ilimi cewa:
Farkon wurin fara gyara shi ne mutum a kan kan sa. Idan mutum bai ilimantu sosai ba, ba yadda za a yi, ya iya ilimantar da wasu. Idan aka yaye mutum da ilimantar da shi sosai to dukkan abubuwa aduniya zasu gyaru.
Babu wata halitta abayan kasa da ke janyo wahala da keta abayan kasa kamar mutum, wannan dabbab mai kafa biyu, kuma babu wata halitta da ke bukatar ilimi da tarbiyya kamar yadda wannan dabba mai kafa biyu ta ke bukata. Kamar yadda ya ke duk wani mutum an wajabta masa ya gyara kan sa, haka ma an wajabta masa yayi wa wasu gyara.
Dukkan litattafan Allah an saukar wa Annabawa da su ne domin ilimantar da wannan halittar, wanda, idan aka kyale ta za ta zama  halitta mafi hadari, don haka a kasa ta a karkashin tarbiyya ahanyar Allah ta yadda za ta zama halitta mafi kyau, kirki, da kuma fifici.  Duniya makaranta ce kuma Annabawa da Waliyai ne Malamai. Ta ilimantarwa wadda ta dace da tarbiyar mutane dukkan duniya zata gyaru. Munufar assasa duniya, shi ne, raino da ilimantar da mutum ta yadda ya dace. Mafi yawan bala’o’in da suka shafi kasashenmu sun samo asali ne daga muggan malamai da kuma rashin ingantar karantarwa, sun sami sani amma ba su da nagarta.
Zamu ci gaba asati na gaba.
KASHI NA BIYU
TUSHEN ADDINI (ci gaba)
Wanda yayi imani da Allah da manzon sa… da dai sauran abubuwan da ake kira tushen akida, bisa hujja kuma ta ilimi, (a sakamakon zuwa makaranta) wannan ne kadai Allah yake kallon aikin sa domin, ya saka masa a gobe kiyama. Amma wanda yake yin musulumci, saboda iyaye ko masu raino ko malamai ko wasu mutane da yake ganin kimar su, ya ga suna yi, to wannan Allah baya ma kallon ibadar sa ballan tana ma ya karba, koda kuwa ya yi salla ya yi azumi ya bauta wa Allah tsawon rayuwar sa, domin wanda yake yin addini saboda na gaba da shi suna yi, babu bambanci a wajen sa, ko ma wane addini iyayen na sa suke yi. Da wani yaren, da ya sami iyayen sa suna bautawa gunki da shi ma gunkin zai bautawa, hakama ko ma me suke bautawa.{بل قالوانتبع ما الفينا عليه أباءبا}  (bari da za mu bi abin da muka sami iyayaen mu akan sa) a wani wajen kuma Allah Ta'ala ya ce: {ان يتنعون الا الظن} ba komai sike biba sai zato.
  Saboda hakane ma malamai saka yi baya ni a kan imanin mukallid (wato wanda yake yin addidi ido rufe) su ka yi ijma`i.
Menene matsayin imanin mukallidi?
Shin ya hallata a yi taklid a tsushen addini?
Me nene matsayin hankali a cikin tushen addini?
Dukkanin wadaanan zamu hadu acikin su afitowa ta gaba, in sha Allah Ta'ala.
KASHI NA UKU
LADUBBAN ANGWANCI KO AMARCI DA KUSANTAR IYALI
Tsira da aminci su kara tabbata ga manzon rahama, Muhammad dan Abdullahi da ahalin gidansa tsarkaka wadanda bin su shi ne shiriya.
Ladubban angwanci/amarci da kusantar iyali
Ladubbana angwanci sun kasu kashi biyu
A-    Mustahabbi: Shi ne abin da Allah ya yi uamrni da shi amma ba ya azbta wanda ya bar shi.  
B-    Makaruhi: Shi ne abin da Allah ya yi hani da shi amma ba ya azbra wanda ya aikata shi.  
A-     Mutahabbi,
1-    mustahabbi ne ga wanda zai kusanci matar sa ya yi salla raka’a biyu sannan ya yi addu’a, sai ya umarci matar ita ma ta yi salla ta yi addu’a domin su kasance su biyun a cikin tsarki, sannan ya dora hannun sa a gaban kanta ya karanta wannan addu’ar: "allhumma ala kitabika tazauwajutuha, wa fi amanatika akhaztuha, wa bi kalimatika istahlaltu farjiha, fa in kadhaita fi rahimiha shai’an faj’alhu musliman sawiyyan wala taj’alhu sharakash shaidani”.
2-    Mustahabbi ne ya zamanto da daddare ango zai fara kusantar matarsa.
3-    Kuma mustahabbi ne ya gayyaci muminai su ci walimar.
A-    Makaruhi,
1-    Makaruhi ne mutum ya sadu da matar sa a wadansu lokuta kamar haka, na farko daren da aka yi kisfewar wata.
2-    Daren da aka yi kisfewar rana.
3-    Lokacin karkatar rana da lokacin faduwar ta har sai shafaki (jaja-jajan gabas) ya buya.
4-    Da lokacin bullowar rana.
5-    Farkon daren ko wane wata banda na ramadhan.
6-    Daren rabin ko wane wata da lokacin da mutum ya yi tafiya tare da matarsa kuma ba su da ruwan wanka.
7-    Da lokacin da aka yi mummunar iska baka ko ja ko kuma guguwa baka ko ja, hakama idan aka yi girgizar kasa.
8-    Kuma kar mutum ya yi jima’i tsurara, ko idan ya yi mafarki, har sai ya yi wanka ko alwala, kuma kar ya yi jima’I idan wani yana ganinsa ko da kuwa jinjiri ne, kuma kada ya kalli farjin matarsa a lokacin da yake yin jima’in.
9-    kuma kar su kalli gabas ko yamma.
10-    Kuma kar ya yi jima’I a cikin jirgin ruwa.
11-    Kuma kar su yi Magana a lokacin da suke yi sai dai idan zikirin Allah ne.
Sakamako
1-    Idan mutum ya sadu da matar sa a lokacin kusufin rana idan aka sami ciki yaron zai kasance cikin cututtuka da fatara har ya mutu.
2-    Idan aka yi jima’a a daren alhamis aka sami ciki, yaron zai zama mai arzikin duniya da lahira kuma shedan ba zai kusance shi ba har ya bar duniya.
3-    Idan mutum ya sadu da matar sa a farkon dare (magriba), idan aka sami da to zai zama matsafi, kuma ya fifita duniya a kan lahira.
4-    An karhanta jima’I a karshen dare musamman darare biyu na sha’aban, idan aka sami yaro to zai zama makaryaci ko asharari ko mai temakon azzalumai ko mutane su rika hallaka a hannunsa.
5-    Ba a yin jima’I a farkon wata domin yaron zai iya samun tabin aljanu ko ya zama galahanga (dolo), musamman daren karamar salla, idan aka sami yaro zai zama masharranci kuma ba a bin da zai haifar sai manyan matsaloli, ko kuma ayi barin cikin tun yana karami, amma banda watan ramadhan, mustahabbi ne ma a yi a farkon sa.
6-    Ba a so a yi jima’I ran daren shabiyar na ko wane wata, idan aka sami yaro zai zama gaula ko mai tabin aljau, ko kuturu musamman a watan sha’aban, idan aka sami yaro zai zama shu’umi, da an gan shi an ga shu’umci.
7-    Idan mutum ya yi jima’I da janaba a jikinsa ta mafarki tun kafin ya yi alwala, idan aka sami ciki, yaron zai zama mai temakon ko wane azzalumi, yin jima’I a jere ba tare da alwala a tsakani ba na sa abin da aka haifa ya sami tabin aljan.
8-    Idan mutum ya yi jima’I a cikin dakin da yara, wadanda yake ganin su ko yake jinsu to wannan ko wadannan yaran ba za su rabauta ba har abada, kuma idan aka sami ciki yaron zai zamo mazinaci ko mazinaciya.
9-    Idan mutum yana jima’I yana kallon farjin matar idan aka sami yaro zai zama makaho, yin Magana a lokacin da ake yin jima’I na sa a haifi kurma, kuma yin jima’I bayan azahar na sa yaro ya zama hararar garke, kuma shedan yana yin murna idan ya ga hararar garke.
10-    Yin jima’I bayan mutum ya yi sha’awar wata matar da ba ta sa ba, na sa a haifi marowaci ko mata-maza.
11-    Kada miji da mata su yi amfani da kyalle daya wajen shafe maniyyin da suka zubar domin yin haka na haifar da gaba da kiyayya a tsakanin su har ta kai ga rabuwa.
12-    Yin jima’I a tsaye kamar jaki, na sa a haifi yaro mai fisarin kwance.
13-    Yin jima’I a dararen babbar salla na karama na sa a haifi yaro mai yatsu shida ko hudu.
14-    Yin jima’I a karkashin bishiya mai ‘ya’ya na sa a haifi yaro mai fitana da kisan kai da jayayya.
15-    Yin jima’I a hasken rana yana sa a haifi yaro wahalalle har ya mutu yana cikin talauci.
16-    Yin jima’I tsakanin kiran salla da ikama na sa ahaifi yaro mai kwadayin zubar da jinin mutane a ko da yaushe.
17-    Yin jima’I a kan daki ku baranda (saman rufin daki), na sa a haifi yaro mai riya ko manafinci. Yin jima’I a daren da mutum zai yi tafiya na sa ahaifi yaro almabazzari.
18-    Yin jima’I lokacin da mutum da matarsa suka yi tafiya ta tsawon kwana uku a wadannan dararen yana sa a haifi yaro mai temakon azzalumai.
19-    Yana da kyau mutum ya yi jima’I ranar litinin domin idan aka sami yaro zai zama mahardacin alkur’ani, kuma mai yarda da abin da Allah ya hukunta masa.  
20-    Yin jima’I ran daren talata na sa a haifi yaro wanda zai yi shahada bayan ya yi Kalmar shahada kuma Allah ba zai azabtar da shi ba in dai ba mushiriki ne ba, kuma zai zama mai yawan kyauta mai tausayi, wanda ba ya alfasha.
21-    Yin jima’I a daren alhamis na sa yaron ya zama shugaba daga cikin shuwagabanni masu adalci ko malami daga cikin malamai.
22-    Yin jima’I a daren juma’a na sa a sami yaro mai iya Magana ta fahimta da hikima.
23-    Jin jima’I bayan la’asar a ranar juma’a idan aka sami yaro zai zama mashahurin malami.
24-    Idan mutun ya yi jima’I ranar alhamis bayan (zawali) karkatar rana, yaron shedan ba zai kusance shi ba har tsufa, Allah zai sa shi cikin aminci duniya da lahira.
25-    Yin jima’I bayan isha’i ranar juma’a na sa a sami yaro ya zama daga cikin fitattun manyan bayin Allah.
[MUNA YI  MUKU FATAN ALHAIRI]
AMINCIN ALLAH YA KARA TABBATA A BISA MUHAMMAD DA ALAYENSA TS
        
MAKOMAR BINCIKE

•    KALMOMIN HIKAMA DA WAAZI NA IMAM KHOMAINI.
•    LIFE OF IMAMA KHOMAIN.
•    AKA’IDUL-IMAMIYYA
•    SHARHI UMMUL-BARAHIN

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: