bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:28:41
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1) Da sunan Allah mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
Lambar Labari: 121
سورة الفاتحة
SURATUL FATIHA (Sura ta 1)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (2)
Dukan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin (mai jujjuya al'amuran) halittu.

الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (3)
Mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ (4)
Ma mallakin ranar sakamako (domin akwai ranaku daban – daban, kamar ranar haihuwar mutum zuwa nan duniyar da ta halittar sa a duniyar baya kafin nan da ranar mutuwa da ranar tashi da ranar shiga wuta ko aljanna).

إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ (5)
Kai kaɗai mukewa bauta kuma kaikaɗai muke neman taimako daga gare ka (ba wanda ake naman taimakon sa sai ubangiji maɗaukaki, zai iya yiyuwa wani ya nemi taimako wajan wani wannan ba ya cin karo da wannnan aya, shi neman taimako ta hanyar sila izinin ubangiji ne domin ba zai yiyu Allah ya baka abu hannu da hannu ba sai da sila wacce ita ce bayin sa, abinda ake so shine kada mutum a zuciyar sa ya sallama 100% cewa dogaron sa Allah, domin shi ya halicci silar, ko kuma bauta, idan wani ya zama bawan wani ba yana nuna cewa bawan ya fita daga bautar Allah bane, dukkanin su biyun suna komawa zuwa ga mahaliccin su baki ɗaya, a kowane abu akwai bi'iznillah da min dunillah, abinda wasu su ka kasa bambancewa daga cikin musulmai kenan har ma su kafirta musulmi).

اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ (6)
Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya miƙaƙƙiya (addu'a ce da ta biyo bayan neman shiriyar ubangiji maɗaukakin sarki).

صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ (7)
Hanyar waɗanda ka cika musu ni'ima (su ne Manzon Allah da iyalan gidan sa tsarkaka (AS) kamar yadda ƙur'ani mai girma ya ambata cikin suratu Maryam aya ta 58), banda hanyar waɗanda ka yi fushi da su, kuma banda ta waɗanda su ke ɓatattu.


Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: