bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:35:11
Ya Allah ka azurta ni da ziyartar dakin ka mai girma, cikin wannan shekara da cikin kowace shekara, cikin abinda ya yi saura gareni da cikin sauki da lafiya da yalwar arziki, kada ka hana ni samun wadannan wurare masu girma, da madaukakan wurare, da ziyarar kabarin annabin ka tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalan sa, ka kasance tare da ni cikin dukkan bukatun duniya da lahira, ya Allah ina rokon ka cikin dukkan abinda ka hukunta kuma ka kaddara, cikin lamuran da aka aiwatar, cikin lailatul kadr daga aiwatarwar ka wacce ba zata sauyu ko ta juya ba
Lambar Labari: 125
Ramadan I

Addu'ar Da Ake Karantawa Bayan Kowacce Sallar Wajibi Cikin Watan Ramadan

اعمال شهر رمضان المبارک
اللهم ارْزُقْنِي حَجَّ بَيتِكَ الْحَرَامِ، فِي عَامِي هَذَا وَفِي كُلِّ عَامٍ، مَا أَبْقَيتَنِي فِي يُسْرٍ مِنْكَ وَعَافِيَةٍ وَسَعَةِ رِزْقٍ، وَلا تُخْلِنِي مِنْ تِلْكَ الْمَوَاقِفِ الْكَرِيمَةِ، وَالْمَشَاهِدِ الشَّرِيفَةِ، وَزِيَارَةِ قَبْرِ نَبِيِّكَ صَلَوَاتُكَ عَلَيهِ وَآلِهِ، وَفِي جَمِيعِ حَوَائِجِ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ فَكُنْ لِي؛ اللهم إِنِّي أَسْأَلُكَ فِيمَا تَقْضِي وَتُقَدِّرُ، مِنَ الْأَمْرِ الْمَحْتُومِ، فِي لَيلَةِ الْقَدْرِ مِنَ الْقَضَاءِ الَّذِي لا يُرَدُّ وَلا يُبَدَّلُ، أَنْ تَكْتُبَنِي مِنْ حُجَّاجِ بَيتِكَ الْحَرَامِ، الْمَبْرُورِ حَجُّهُمْ، الْمَشْكُورِ سَعْيُهُمْ، الْمَغْفُورِ ذُنُوبُهُمْ، الْمُكَفَّرِ عَنْهُمْ سَيِّئَاتُهُمْ، وَاجْعَلْ فِيمَا تَقْضِي وَتُقَدِّرُ، أَنْ تُطِيلَ عُمُرِي، وَتُوَسِّعَ عَلَيَّ رِزْقِي، وَتُؤَدِّيَ عَنِّي أَمَانَتِي وَدَينِي، آمِينَ رَبَّ الْعَالَمِينَ .

AYYUKAN RAMADHAN MAI AL'BARKA
ADDU'AR MUSTAHABBI BAYAN NA ADDU'O'IN WAJIBI
Ya Allah ka azurta ni da ziyartar dakin ka mai girma, cikin wannan shekara da cikin kowace shekara, cikin abinda ya yi saura gareni da cikin sauki da lafiya da yalwar arziki, kada ka hana ni samun wadannan wurare masu girma, da madaukakan wurare, da ziyarar kabarin annabin ka tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalan sa, ka kasance tare da ni cikin dukkan bukatun duniya da lahira, ya Allah ina rokon ka cikin dukkan abinda ka hukunta kuma ka kaddara, cikin lamuran da aka aiwatar, cikin lailatul kadr daga aiwatarwar ka wacce ba zata sauyu ko ta juya ba, ka rubuta ni cikin masu ziyartar dakin ka mai al'farma, wadanda hajjin su ya karbu, dacen su ya zama abin godiya, wadanda aka gafarta zunuban su, wadanda aka kankare munanan ayyukan su, ka sanya wannan cikin abinda ka hukun ta ka zartar, ka tsawaita rayuwa ta, ka yalwata arziki na, ka sanya na sauke abinda ke kaina na amana ta da addini na, ka amsa ya ubangijin halittu.
***

يَا عَلِيُّ يَا عَظِيمُ، يَا غَفُورُ يَا رَحِيمُ، أَنْتَ الرَّبُّ الْعَظِيمُ، الَّذِي لَيسَ كَمِثْلِهِ شَي‏ءٌ، وَهُوَالسَّمِيعُ الْبَصِيرُ، وَهَذَا شَهْرٌ عَظَّمْتَهُ وَكَرَّمْتَهُ، وَشَرَّفْتَهُ وَفَضَّلْتَهُ عَلَى الشُّهُورِ، وَهُوَ الشَّهْرُ الَّذِي فَرَضْتَ صِيَامَهُ عَلَيَّ، وَهُوَ شَهْرُ رَمَضَانَ، الَّذِي أَنْزَلْتَ فِيهِ الْقُرْآنَ، هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ، وَجَعَلْتَ فِيهِ لَيلَةَ الْقَدْرِ، وَجَعَلْتَهَا خَيراً مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ، فَيَا ذَا الْمَنِّ وَلا يُمَنُّ عَلَيكَ، مُنَّ عَلَيَّ بِفَكَاكِ رَقَبَتِي مِنَ النَّارِ، فِيمَنْ تَمُنُّ عَلَيهِ، وَأَدْخِلْنِي الْجَنَّةَ، بِرَحْمَتِكَ يَا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ.

Ya madaukaki mai girma, ya maigafara mai jin kai, kai ne ubangiji mai girma, wanda ba wani abu kamar sa, shi ne mai ji da gani, wannan wata ne da ka girmama ka kuma daga matsayin sa, ka daukaka shi ka fifita shi kan sauran watanni, shi ne watan da ka wajabta min azumtar sa, shi ne watan Ramadan, wanda ka saukar da al'kurani mai girma a cikin sa, shiriya ga mutane kuma hujja ce ta shiriya da rarrabe gaskiya da karya, ka sanya daren da ake kira lailatul kadri cikin sa, ka sanyashi alheri daga watanni dubu, ya wanda ke bayarwa ba kuma wanda zai iya baka, ka taimake ni da 'yanta wuya na daga wuta, cikin wadanda ka kyautata wa, ka shigar da ni al'janna, don rahamar ka ya mai jin kan masu jin kai.
***

اللهم أَدْخِلْ عَلَى أَهْلِ الْقُبُورِ السُّرُورَ؛ اللهم أَغْنِ كُلَّ فَقِيرٍ؛ اللهم أَشْبِعْ كُلَّ جَائِعٍ؛ اللهم اكْسُ كُلَّ عُرْيَانٍ؛ اللهم اقْضِ دَينَ كُلِّ مَدِينٍ؛ اللهم فَرِّجْ عَنْ كُلِّ مَكْرُوبٍ؛ اللهم رُدَّ كُلَّ غَرِيبٍ؛ اللهم فُكَّ كُلَّ أَسِيرٍ؛ اللهم أَصْلِحْ كُلَّ فَاسِدٍ مِنْ أُمُورِ الْمُسْلِمِينَ؛ اللهم اشْفِ كُلَّ مَرِيضٍ؛ اللهم سُدَّ فَقْرَنَا بِغِنَاكَ؛ اللهم غَيِّرْ سُوءَ حَالِنَا بِحُسْنِ حَالِكَ؛ اللهم اقْضِ عَنَّا الدَّينَ، وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ، إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَي‏ءٍ قَدِيرٌ .

Ya Allah ka shigarwa mazauna kabari jin dadi cikin cikn kabarin su, ya Allah ka yalwata dukkan talaka, ya Allah ka kosar da dukkan mayunwaci, ya Allah ka suturta dukkan matsiraici, ya Allah ka biya bashin dukkan wanda ake bi bashi, ya Allah ka yaye wa dukkan mai bakin ciki, ya Allah ka mayar da dukkan baki gidajen su lafiya, ya Allah ka sako dukkan furzinoni, ya Allah ka kyara barnar duk barnar da 'yan iska ke wa lamurran musulmi, ya Allah ka yaye ciwon dukkan marasa lafiya, ya Allah ka toshe talaucin mu da wadatar ka, ya Allah ka canja munanan halayyen da kyawawan halayen ka, ya Allah ka biya mana basussukan mu, ka wadatar da mu daga talauci, domin kai mai iko ne kan dukkan komai.
***

اللهم إِنِّي بِكَ وَمِنْكَ أَطْلُبُ حَاجَتِي، وَمَنْ طَلَبَ حَاجَةً إِلَى النَّاسِ فَإِنِّي لا أَطْلُبُ حَاجَتِي إِلاّ مِنْكَ، وَحْدَكَ لا شَرِيكَ لَكَ، وَأَسْأَلُكَ بِفَضْلِكَ وَرِضْوَانِكَ، أَنْ تُصَلِّيَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَأَهْلِ بَيتِهِ، وَأَنْ تَجْعَلَ لِي فِي عَامِي هَذَا إِلَى بَيتِكَ الْحَرَامِ سَبِيلاً، حِجَّةً مَبْرُورَةً مُتَقَبَّلَةً زَاكِيَةً خَالِصَةً لَكَ، تَقَرُّ بِهَا عَينِي، وَتَرْفَعُ بِهَا دَرَجَتِي، وَتَرْزُقَنِي أَنْ أَغُضَّ بَصَرِي، وَأَنْ أَحْفَظَ فَرْجِي، وَأَنْ أَكُفَّ بِهَا عَنْ جَمِيعِ مَحَارِمِكَ، حَتَّى لا يَكُونَ شَي‏ءٌ آثَرَ عِنْدِي مِنْ طَاعَتِكَ وَخَشْيَتِكَ، وَالْعَمَلِ بِمَا أَحْبَبْتَ، وَالتَّرْكِ لِمَا كَرِهْتَ وَنَهَيتَ عَنْهُ، وَاجْعَلْ ذَلِكَ فِي يُسْرٍ وَيَسَارٍ وَعَافِيَةٍ، وَمَا أَنْعَمْتَ بِهِ عَلَيَّ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ وَفَاتِي قَتْلاً فِي سَبِيلِكَ، تَحْتَ رَايَةِ نَبِيِّكَ مَعَ أَوْلِيَائِكَ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَقْتُلَ بِي أَعْدَاءَكَ وَأَعْدَاءَ رَسُولِكَ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تُكْرِمَنِي بِهَوَانِ مَنْ شِئْتَ مِنْ خَلْقِكَ، وَلا تُهِنِّي بِكَرَامَةِ أَحَدٍ مِنْ أَوْلِيَائِكَ؛ اللهم اجْعَلْ لِي مَعَ الرَّسُولِ سَبِيلاً، حَسْبِيَ اللهُ، مَا شَاءَ اللهُ .

Ya Allah gareka na ke kuma gareka na miko bukatu na, idan wani ya mika bukatun sa ga mutane hakika ni bana neman bukatu na wajan kowa sai kai, kai kadai ne baka da abokin tarayya, ina rokon ka don falalar ka da yardar ka, ka yi salati ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa, ka sanya ni cikin masu zuwa hajjin dakin ka cikin wannan shekara, hajjin da take karbabbiya cikakkiya tsarkakkiyar da aka yi don kai, wacce zata zame min hasken shiriyar idanu na, ka daga daraja ta da ita, ta azurta ni da rufe idanu na kan dukkan munanan ayyuka, na kare farji na, na kame kaina daga dukkan abubuwan da ka haramta, har ya zama ba abinda ya rage tare da ni sai abubuwan da kake so na biyayyar ka da tsoron ka, da aikata abinda kake so, da abrin duk abinda kake ki da wanda ka hana a aikata, ka sanya hakan ya zama cikin sauki da saukakewa tare da lafiya, da abinda ka yi min ni'imar sa, ina rokonka ka sanya na batar da lokaci na a tafarkin ka, karkashin tutar annabin ka tare da waliyyan ka, ina rokon ka yin amfani dani wajan kashe makiyan ka da makiyan manzon ka (SAW), ina neman ka girmama ni da kimanta wanda kake son sa cikin halittun ka, kada ka kaskantar da ni da girman daya daga cikin waliyyan ka, ya Allah ka sanyani a tafarki daya da Manzon ka, kai ne isahshe, madalla da Allah mahalicci.


أعمال الإفطار في کل لیلة
الأول: الافطار، ويُستَحب تأخَيره عَن صلاة العشاء إلاّ إذا غلب عَليهِ الضعف أو كانَ له قوم ينتظرونه.
الثاني: أن يفطر بالحلال الخالي مِن الشبهات سّيما التمر، ليضاعف أجر صلاته أربعمائة ضعف، ويحسن الافطار أيضاً بأيٍّ مِن التمر والرطب والحلواء والنبات والماء الحار.
الثالث: أن يدعو عِندَ الافطار بدعوات الافطار المأثورة، منها أن يَقول:
اللّهُمَّ لَكَ صُمْتُ وَعَلى رِزْقِكَ أَفْطَرْتُ وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ.
ليهب الله لَهُ مثل أجر كُل مَن صام ذلِكَ اليَوم.
الرابع: وروي أن أمير المُؤمنين (عليه السلام) كانَ إذا أراد أن يفطر يَقول:
بِسْمِ اللهِ، اللّهُمَّ لَكَ صُمْنا وَعَلى رِزْقِكَ أَفْطَرْنا، فَتَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ العَلِيمُ.
الخامس: أن يقول عند أوَّل لقمة يأخذها:
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ، يا واسِعَ المَغْفِرَةِ اغْفِرْ لِي، ليَغفِرَ اللهُ لَهُ.
السادس: وفي الحديث: إنّ الله تعالى يعتق في آخر ساعة مِن نهار كُل يَوم مِن شَهر رَمَضان ألف ألف رقبة، فسل الله تعالى أن يجعلكَ منهم .
السابع: أن يتلو سورة ‌القدر عند الافطار.
الثامن: أن يتصدق عند الافطار، ويفطّر الصائِمين ولو بعدد من التمر أو بشربة مِن الماء. عن النبي (صلّى الله عليه وآله وسلم): انّ مَن فطّر صائماً فَلهُ أجر مثله مِن دون أن ينقص مِن أجره شي، وكانَ له مثل أجر ما عمله مِن الخَير بقّوة ذلِكَ الطعام .
روى آية الله العلامة الحلي في الرسالة السعدية عَن الصادق (عليه السلام): انّ أيّما مؤمَن أطعم مؤمناً لقمة في شَهر رَمَضان كتبَ الله لَهُ أجر مَن أعتق ثلاثين رقبة مؤمنة، وكانَ له عِندَ الله تعالى دعوة مستجابة .
***

AYYUKAN KOWANNE DARE
Na farko: Buda baki, an so jinkirta shi daga sallar ishsha sai idan jikin sa ya raunana ko kuma gudun idanun mutanen da yake cikin su.
Na biyu: ya yi buda baki da tsantsar halal musamman ma ya yi da dabino, don ya nunnunka ladan sallar sa zuwa ninki dari hudu, da kowane irin abu ya yi buda bakin ba komai kamar danye kayan zaki da kayan itace ko ruwan zafi.
Na uku: ya yi addu'ar da aka rawaito, shi ne ya karanta:
Allahumma laka sumtu wa ala rizkika afdartu wa alaika tawakkaltu
(ya Allah kai na yi wa azumi kuma cikin arzikin ka na ke buda baki gareka na dogara)
Allah zai baka lada kimanin na duk wandanda su ka azumci wannan ranar.
Na hudu: an rawaito cewa Amirul mumineen (AS) ya kasance idan zai yi buda baki ya na cewa:
Bismillahi, Allahumma laka sumna wa ala rizkika afdarna, fatakabbal minna, innaka antas samii'ul aliim, (da sunan Allah, Allah kai mu ka yi wa azumi kuma cikin arzikin ka mu ka bude baki, ka karbi azumin mu, kai ne mai ji masani).
Na Biyar: yayin da ya dauki lomar farko zai kai bakin sa sai yace:
Bismillahir rahmanir rahiim, ya wasi'ul magfira igfirli, li yagfirallah, (da sunan Allah mai rahama mai jin kai, ya mai mayalwaciyar ni'ima ka gafarta min, Allah ka gafarta masa).
Na shida: cikin hadisi: Allah madaukakin sarki na 'yanta mutane dubu karshen kowace awan karshen kowane daren watan ramadan, ka roki Allah (SW) ya sanya ka cikin su.
Na bakwai: ya karanta suratul Kadri yayin buda baki.
Na takwas: ya yi sadaka yayin buda baki, ya bude bakin masu azumi koda da dabino ne ko rowa, an karbo daga Manzo (SAW) cewa: duk wanda ya budi bakin mai azumi ya na da lada irin na wanda ya yi azumin ba tare da an ragi ladan sa ba, yana kuma da ladan duk wani aikin alheri da mai azumin ya yi da karfin da ya samu daga cin abincin.
An rawito daga Allama Hilli cikin risalas Sa'adiyya daga Imam Sadik (AS): hakika duk wani muminin da ya ciyar da mumini loma cikin watan Ramadana Allah zai rubuta masa ladan wanda ya 'yanta bayi muminai talatin, kuma ya na da karbabbiyar addu'a wajan Ubangiji.
***
 
دعاهای مستحب در هر شب ماه مبارک
روى السيّد أنّ مَن قالَ هذا الدُّعاء في كُل لَيلَة مِن شَهر رَمَضان غفرت له ذنوب أربعين سنة:
اللهم رَبَّ شَهْرِ رَمَضَانَ، الَّذِي أَنْزَلْتَ فِيهِ الْقُرْآنَ، وَافْتَرَضْتَ عَلَى عِبَادِكَ فِيهِ الصِّيَامَ، صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ، وَارْزُقْنِي حَجَّ بَيتِكَ الْحَرَامِ، فِي عَامِي هَذَا وَفِي كُلِّ عَامٍ، وَاغْفِرْ لِي تِلْكَ الذُّنُوبَ الْعِظَامَ، فَإِنَّهُ لا يَغْفِرُهَا غَيرُكَ، يَا رَحْمَانُ يَا عَلاّمُ .

ADDU'A TA MUSTAHABBI CIKIN KOWANNE DAREN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA
Sayyid ya rawaito cewar duk wanda ya karanta wannan addu'ar cikin kowane dare cikin watan ramadana za'a gafarta masa zunuban sa na shekara arba'in:
Ya ubangijin watan ramadana, wanda ka saukar da kur'ani a cikin sa, ka wajabtawa bayin ka azumi a cikin sa, ka yi salati ga Annabi Muhammad da Iyalan sa, ka azurta ni ziyartar dakin ka mai alfarma, cikin wannan sekkarar da ma kowacce, ka gafarta min wadancan manyan zunuban masu girma, domin ba mai gafarta su idan ba kai ba, ya mai rahama madaukaki.
***

اللهم بِرَحْمَتِكَ فِي الصَّالِحِينَ فَأَدْخِلْنَا، وَفِي عِلِّيِّينَ فَارْفَعْنَا، وَبِكَاسٍ مِنْ مَعِينٍ مِنْ عَينٍ سَلْسَبِيلٍ فَاسْقِنَا، وَمِنَ الْحُورِ الْعِينِ بِرَحْمَتِكَ فَزَوِّجْنَا، وَمِنَ الْوِلْدَانِ الْمُخَلَّدِينَ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَكْنُونٌ فَأَخْدِمْنَا، وَمِنْ ثِمَارِ الْجَنَّةِ وَلُحُومِ الطَّيرِ فَأَطْعِمْنَا، وَمِنْ ثِيَابِ السُّنْدُسِ وَالْحَرِيرِ وَالْإِسْتَبْرَقِ فَأَلْبِسْنَا، وَلَيلَةَ الْقَدْرِ وَحَجَّ بَيتِكَ الْحَرَامِ وَقَتْلاً فِي سَبِيلِكَ فَوَفِّقْ لَنَا، وَصَالِحَ الدُّعَاءِ وَالْمَسْأَلَةِ فَاسْتَجِبْ لَنَا، يَا خَالِقَنَا اسْمَعْ وَاسْتَجِبْ لَنَا، وَإِذَا جَمَعْتَ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَارْحَمْنَا، وَبَرَاءَةً مِنَ النَّارِ فَاكْتُبْ لَنَا، وَفِي جَهَنَّمَ فَلا تَغُلَّنَا، وَفِي عَذَابِكَ وَهَوَانِكَ فَلا تَبْتَلِنَا، وَمِنَ الزَّقُّومِ وَالضَّرِيعِ فَلا تُطْعِمْنَا، وَمَعَ الشَّيَاطِينِ فَلا تَجْعَلْنَا، وَفِي النَّارِ عَلَى وُجُوهِنَا فَلا تَكُبَّنَا، وَمِنْ ثِيَابِ النَّارِ وَسَرَابِيلِ الْقَطِرَانِ فَلا تُلْبِسْنَا، وَمِنْ كُلِّ سُوءٍ يَا لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، بِحَقِّ لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ فَنَجِّنَا
 .
Ya Allah ka shigar da ni cikin salihan bayin ka, ka daga mu cikin madaukaka, ka shayar da mu daga idanuwar ruwan salsabiil, ka aura mana hurul iini don girman rahamar ka, ka hidimta min da 'ya'ya na dindindin masu kama da lu'u-lu'un da aka boye, ka ciyar da mu 'ya'yan itaciya da naman tsuntsayen gidan al'janna, ka sanya min kaya alhariri mai walkiya, ka datar da mu daren lailatul da ziyartar dakin ka da kuma yaki a tafarkin ka, ka amsa mana kyawawan rokon mu da barar mu gare ka, ya mahaliccin mu ka ji rokon mu ka amsa mana, idan muka taru na farkon mu da na karshen mu ka rahamshe mu, ka rubuta mu cikin kubutattu daga wuta, kada ka sanya mu cikin jahannama, kada ka jarrabce mu da kaskantarwar ka da azabar ka, kada ka ciyar da mu daga zakkum, kada ka sanya mu tare da shaidanu, kada ka sanya wuta a fusakun mu, kada ka sanya mana tufafin wuta da rigar gol tar, ka kare mu daga dukkan mummunan abu ya wanda babu wani ubangiji sai shi, ka tseratar da mu don darajar ka amatsayin ka na wanda babu wani ubangiji sai kai.
***

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: