bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:36:39
Daya daga cikin lamarin mai mihimmancin gaske da ya zama wajibi al’ummar musulmai su waiwaya shi ne lamarin halifanci bayan Manzo (s.a.w)
Lambar Labari: 126
Da Sunan Allah Ta'ala Mai Rahama Mai Jin Qai

Daya daga cikin lamarin mai mihimmancin gaske da ya zama wajibi al’ummar musulmai su waiwaya shi ne lamarin halifanci bayan Manzo (s.a.w).
Don haka ne ma naga ya dace in waiwayi wannan babban lamari don mu san haqiqanin abin da ya Manzo (s.a.w) ya daro al’ummarsa a kai bayan wafatin sa. Da yawa mutane kan yi tambaya shin Manzo (saw) ya yi wasiyya da halifanci? Shin ya ayyana wanda zai gaje shi a bayansa?
qwarai da gaske, tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya bayyana hakan a ingantattun Hadisai a bayyane ba wata shakka a kansu, duk wanda ya cire ta’assubanci da qin mutanen gidan Annabi (s.a.w) zai gane haka kamar yadda ingantaccen hankali ke nuna haka.
  Amma hadisai, cikinsu akwai: "matsayinka a wajena irin matsayin Haruna wajen Musa ne sai dai ni ba Annabi Abayana”( ).
   "kai macivincin duk wani mumini ne a bayana”( ).
   "qur’ani na tare da Aliyu ba za su rabu ba har sai zo min a tafkin Alkausara”( ).
   Duk wanda ni shugabansa ne to Aliyu ma shugabansa ne”( ).
    Tabbas waxanan hadisan kaxai sun isa kan cewa Manzon Allah (s.a.w) ya halifantar da Aliyu ga wanda ya kalli lafuzan da zurfin ma’anoninsu, kamar lokacin fita yaqin Tabuka, kamar yadda Musa ya Halifantar da Haruna a kan mutanensa ya mayar da shi waziri. Tabbas kamantawar da Annabi (s.a.w) ya yiwa Aliyu (a.s) da Haruna a wajen Musa akwai kafa dalili kan cewa shi ne zai gaje shi bayan komawarsa ga Allah.
     Qissar Ghadir ma sananniya ce mutawatira ita kaxai ma tana tabbatar da cewa Manzon Allah (s.a.w) ya tabbatarwa da Aliyu (a.s) shugabanci don shi ne Halifansa. Tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya yi niyyar rubuta takardar da zata hana su vata da rarrabar juna a lokacin rashin lafiyarsa ya yin da ya ga sahabbai na cikin rikici, amma sai Umar xan Khaxxab ya hana shi rubuta takardar.
    Hakam Hadisin Manzon Allah (s.a.w) da ya ce: "duk wanda ni shugabansa ne to Aliyu ma shugabansa ne” a fili ne cewa Aliyu ne shugaban mumini da mumina.
    Amma dalilin hankalin da ke nuna cancantar Iman Ali (a.s) da Halifanci shi ne bai dace wani ya zama Halifa har ya jivinci al’amarin musulmai bayan Manzon Allah (s.a.w) ba sai wanda ya fi kowa ba irinsa a wajen xabi’u da darajoji kuma dole ya fi sa’aninsa komai, yana gaba da tsararrakinsa ya zama daban a cikin mutane, ba shi da wata matsala, shi kaxai ne ba shi da kwatankwaci, ida niya ba ta ganin irinsa ba a haxuwa da irin sa, mai kamalar addini, da kamalar ilimi da tsoron Allah, da xaukaka Kalmar Allah (La ilaha illallah Muhammadur Rasulullah), da taimakon shugaban Talikai (s.a.w) don ya riga mutane musulunta, shi ne mafificinsu wanda ya fi su jarunta ya kuma fi su tsoron Allah da gaske.
     Duk waxannan siffofin Aliyu ne (a.s) yake da su, shi ne aka Haifa musulmi ya miqa wuya ga al’amarin Allah (T.W.T), a makarantar Manzon Allah (s.a.w) aka yaye shi, ya taso har girma a hannun Manzon Allah (s.a.w) shugaban masu tsoron Allah (s.a.w).
   Jihadinsa a kan tafarkin Allah ne kuma yana sama da duk wani jihadi, tsoron Allansa na sama da duk wani tsoron Allah, jaruntarsa na sama da duk wata jarumta, imaninsa da gudun Duniyarsa na sama da duk kowanne gudun Duniya da Imani, yana sauraron Annabi (s.a.w) a lokacin da yake ganawa da Ubangijinsa mahaliccinsa sai ya qoshi da maganganun Annabi (s.a.w), da wa’azozinsa, ya san ififici daga daga magangararsa kuma ya sami ilimi daga mafitarsa haka ma imani daga mabubbugarsa. Ya san haka tun yana yaro a hannun shugaban mursalan da ya yi masa tarbiyya Annabi (s.a.w) yana xora shi kan cinyarsa, ya kan rungume shi a qirjinsa, yana kwantar da shi kan shinfixarsa, yana goga masa maxaukakin jikinsa, yana shaqar qamshin jikinsa, yana nuna masa hasken wahayi.
    Tabbas kaset xin Tarihi lokacin da yake wucewa ta kusa da ingantaccen hankali yana bijiro da manyan sahabbai (R.A) da ayyukansu xaya bayan xaya, yana kuma haxa tsa kanin ayyukan Imam Ali (k.w) da qoqarinsa da Jahadinsa da tasowarsa da matsayinsa a wajen Manzon Allah (s.a.w), tabbas zai yi hukunci ba tare da kai kawon cewa shi ne ya fi dace wa da Halifanci ya kuma fi cancanta da shi, ba tare da kokwanto ba.
   Wane Hankali ne ba ya tabbatar da cewa Aliyu (k.w) ne ya fi cancanta da Halifanci kuma Annabi (s.a.w) ya ba shi shugabanci? Shi ne wanda aka Haifa musulmi bai tava yiwa gunki sujjada ba, ya yi iklasin yiwa Allah Kalmar shahada, ya riga mutane muslunci sanadiyyar da’awar Manzon Allah mai girma (s.a.w).
   Wane Hankali ne ba zai ce Aliyu (a.s) ne ya dace da Halifanci ba, shi ne wanda aka Haifa a ka’aba, ya yi sallah tare da Manzon Allah (s.a.w) a farkon sallar da Annabi (s.a.w) ya yi.
     Wane Hankali ne ba zai ce Aliyu ne ya dace da Halifanci ba, alhalin Allah ya tsarkake shi shi da mutanen gidansa daga dauxa tsarkakewa a ayar tsarkakewa, wannan ce iradar Allah (T.w.a) mai aikata abin da ya so.
  Wane Hankali ne ba zai ce Aliyu (a.s) ne ya da ce da Halifanci ba alhalin shi ne a cikin yaqoqin Manzon Allah (s.a.w) tun daga farko har zuwa qarshe banda yaqin Tabuta, saboda Annabi (s.a.w) ya ba shi riqon garin Madina, shi ne ya dace, shi ne zaki a fagen daga ba wanda ke taka rawa irin ta sa, bai guduwa daga fagen fama ba, bai tava jin tsoron rubduna ba, kai har mala’ika ma sun yi mamakin haqurinsa da tabbatarsa, nan take Jibrilu ya yi yekuwa a tsa kanin sama da qasa ya ce: "Ba wani saurayi sai Aliyu, ba wata takobi sai zulfiqar”.
    Wane Hankali ne ba zai ce Aliyu (a.s) ne ya fi cancanta da halifanci ba, shi ne wanda Annabi (s.a.w) ya ce a kansa lokacin da ya yi fito-na-fito da Amru bn Abdilwuddin Al’amari a yaqin gwalalon "Gaba xayan imani ya fito zuwa ga baki xayan shirka”.
    Wane hankali ne ba zai ce Aliyu (a.s) ne ya dace da halifanci ba alhalin Allah ya xorawa duk musulmai qaunarsa da qaunar mutanen gidansa don Allah (s.w.t) ya sanya qaunar ta zama a maimakon ladan wahalhalun da Manzon Allah ya sha na isar da saqo da kuma nauyin day a xauka na saqon.
     Wane hankali ne ba zai ce Aliyu (a.s) ne ya cancanci halifancin Manzon Allah (s.a.w) ba, shi ne wanda Annabi (s.a.w) ya ce: "Ni ne birnin ilimi Aliyu ne qofar”.
    Wane hankali ne ba zai ce Aliyu ne ya fi cancanta da halifancin Annabi (s.a.w) alhalin shi ne xan uwansa a duniya da Lahira, shi ne mai taimaka masa kuma wazirinsa shi ne jakar iliminsa wanda ya gaji hikimarsa, magabacin Al’umma, abokin ganawa, wanda ya bada dukiya a voye da a fili, wanda ya gaji littafi mai kunne mai kiyayewa.
      Wane hankali ne ba zai ce Aliyu ne ya fi cancanta da halifancin Annabi (s.a.w) ba, shi ne fa shugaban muminai, shugaban addini, mijin sayyida Zahara, mai kashe fajirai, mai tuta, shugaban larabawa.
          Wane hankali ne ba zai ce Aliyu ne ya cancanta da halifanci ba, shi ne fa wanda Umar xan khaxxab (r.a) ya ce: "Ba don Aliyu ba da Umar ya halaka”.
          Wane hakanli ne ba zai yi imani da cancantar Aliyu da halifancin Manzon Allah (s.a.w) alhalin dattijai biyu Abubukar da Umar sun tabbatar da shugabancinsa a ranar Ghadir khum har suka ce: Da kayu madallah ya xan Abu Xalib ka zama shugabana kuma shugaban kowanne mumini da mumina.
          Kai wane hakalin ne ba zai tabbatar tare da sallamawa cancantar halifantar da shi da Annabi (s.a.w) ya yi ba alhalin Annabi (s.a.w) ya ce: "Ya Allah ka juyar da gaskiya duk inda Aliyu ya juya”.
          Tabbas Aliyu (k.w) shi ne ya fi cancanta da halifanci a bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w) saboda siffofin nan da yake da su, a kokwanto.
          Halifanci mai dace da kowa ba sai da shi, shi ma bai dace da komai ba sai da halifanci.
          Abubakar yah au halifanci bayan Manzon Allah (s.a.w) duk da cewa Imam Ali (a.s) wanda shi ne shugaba mafifici na nan, wannan baya nuna fifikon Abubakar a kansa. A kowane zamani da gari akwai siyasa, hakan ya faru ne saboda abin da aka yi a saqifa aka bar Umarnin Allah (T.A) da Umarnin Manzonsa, aka bi son zuciyar quraishawa. Ai hakan saboda natijar sassavawar ra’ayoyi ne a ranar da shugaban Duniya (s.a.w) ya nemi waxanda ke wajen wato sahabbansa da su kawo abin rubuto don ya rubuta nusu abin da in suka yi riqo da shi ba za su vata ba har abada.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: