bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:38:46
Wajibi ne ga musulmin duk duniya su zama abu guda, masu manufa guda’ kuma masu Magana da murya daya, ta yadda jagoran cin su na duniya zai zama guda, kamar yadda manzo ya koyar, domin idan musulmin da yake yamma ya nemi temakon wanda ya ke gabas sannan na gabas din bai amsa masa ba
Lambar Labari: 127
 Da sunan sa madaukaki

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya aikoda Manzo (s.a.w) domin tausayawa ga talikai. Tsira da aminci su kara tabbata ga wanda aka aiko izuwa dukkanin halitta, manzon rahama, abin zabi mafifici, baban Alkasim, Muhammad dan Abdullah, tare da ‘ya’yan gidan sa tsarkaka, da sahabban sa managarta, wanda yake cewa: "An aiko ni domin in ciki kyawawan halaye” "musulmai yan’uwan juna ne”
  Hakika samuwar wannan Manzo (s.a.w) ita ce mafi girman rahama ga bayi tun da duk wani mai kira zuwa gyara (Annabawa, Manzanni dss) ko dai ya zama mai share masa fage ko kuwa mai ci gabatar da da abin da ya yi.
  Wajabcin Hadin Kai
Wajibi ne ga musulmin duk duniya su zama abu guda, masu manufa guda’ kuma masu Magana da murya daya, ta yadda jagoran cin su na duniya zai zama guda, kamar yadda manzo ya koyar, domin idan musulmin da yake yamma ya nemi temakon wanda ya ke gabas sannan na gabas din bai amsa masa ba, to ya rage saura musulmi daya ke nan a doron kasa, domin su musulmai yan’uwan junane, karami daga cikin su na dauke da alkawarin su, (in a ka taba shi an taba sauran) kuma su hannu daya ne absa wadanda suke ba su ba.
  Wani abin ban mamaki a yau shi ne yadda muke fama da matsalolin cikin gida ta yadda wasu musulmi ba sa damuwa a kan abin da ya ke damun yan’uwansu ballantana su yi tunani a kan yadda za a samar musu da mafita daga abin da suke ciki, kai ta kai ma ga cewa su ne ke kashe junansu da kan su wai don suna da banbancin akida, hakika wannan abu na da ban mamaki! ka dubi abin da yake faruwa a Iraq da Syria da Yemen da Flastin, da Afghanistan da Somalia, dss wanda duk wannan yana faruwa ne sakamakon daidaitar al’ummar musulmi. Ka duba kaga babbancin da ke tsakanin sauran kungiyoyin yammacin duniya da suke daga kabilu mabanbanta da addinai daban-daban, amma duk da haka sun hade kansu wajen cimma abin da suka sa a gaba wanda daga ciki akwai sace dukiyar kasashan musulmai da na Africa da haifar musu da yake-yaken cikin gida. Sai mu musulmi da muka yi imani da Allah daya Manzo daya dss, amma mun kasa samar da centre daya wacce kowa ya yarda da ita, al’amarin da ya sa muke fama da matsalolin da ba za su iya lissafuwa ba, idan wani musulmi ya ce ga mafita daga matsala ka za, zaka samu cewa farkon wanda zai fara yin fada da shi akai shi ne musulmi dan’uwan sa. Wannan wane irin bala’i ne!!!?
 A binciken da na yi kan addinai na gano cewa addinin kiristanci, banbance- banbancen da yake tsakanuin mazhabobin su ya fi wanda yake tsakanin mazahabobin musulmai domin su da dama zaka ga sabaninisu a tushe ne ba a reshe ba, amma mu musulmai mafi yawanci zaka samu na mu ya tsaya a reshe kawai, duk da wannan amma su suna da hedkwata daya bisa jagorancin addinin su, wanda gabadayan su ne  suka tattara suka samara da ita, kuma wannan centre tana da wakilci da kuma offishin jakadanci a ko wace kasa ta duniya, da sauran tsare-tsare masu kyau da wannan centre ta ke da su wadanda ba za su lissafu a nan ba, a yayiu da mafiya yawan mu tun asali bama tunani kan wannan. Idan kuma an sami wani ya yi kokari ya samar da wani abu sai ka ga mun fara gunaguni muna cewa: (ai dan kaza ne) a kullum mu ke nan muna rayuwa kamar wasu namun daji, inna lillahi wa inna ilaihirraju’un!!!
  Me Ya Ja Mana Koma Baya.
Kamata ya yi a ce sauran al’ummu na duniya su yi koyi a wajen mu, ta ko wane bangare, kamar yadda lamarin ya ke sama da shekaru 500 da suka wuce da kuma kwankin musulumci na farko, ta yadda ya zama komai na ci gaba, a wajen musulmi ake fara ganinsa. Al’amarin ya cenza ne da ga baya, sakamako rarraba da ta yi yawa a cikin musulmai, ta yadda lalacewar lamarin ya kai ga, ana hada kai da musulmi a yaki dan’uwan sa musulmi, kamar yadda muke gani a yau. Shin kasan cewa abin da yake faruwa yau a iraki, na kashe- kashe rayukan (mutanen gari) ta hanyar dana bama- bamai manya- da samar da kungiyar ‘yanta’adda ta Da’ishkasashen yamma ne dare da hadin kan manya shuwagabbanin gabas ta tsakiya ne suke shirya shi don kar a sami daular musulumci, wacce ta yiyu ta zama hadari ga mulkin su nan gaba, ta hanyar wayar da kan mutanen su wajen neman yan’ci da kuma shari’ar musulumci da ‘yanacin zabar  mazahaba. Kana tsammanin shuwagabannin gabas ta tsakiya da gaske suna son yan’cin irakawa? me ya sa suka bawa Amerika matsugunin da daga nan ana iya tasar jirage a kaiwa yan’uwan su hari? Don me ya sa suke jimamin kashe Sadam bayan su suka bada sararin samaniya, (in banda Iran) da masaukin da aka yake shi ta nan? A da cen sadam  bai yake Iran da Saudiyya da Kuwait ba har suka hada kai a kasa wa Iraq takunkumi ba? Me ya sa kuma a yau suke gaba da kashe sadam?  Idan ka zuba wadannan tambayoyi a faifai ka amsa su zaka samu cewa duk abin dalilin wadannan abubuwan ya tsaya ne kan kare maslahar su da yadda mulkin su zai ci gaba, bayan nan babu wata tausayawa ga Sadam ko mutanen Iraq. Misali, ba su so a kashe Sadam ba don kar wata rana irin wannan ya zo kan masu yin aiki irin nasa na mulkin danniya da zalumci, da biyayya ga makiyan musulmi da musulumci, na yhammacin duniya.
ME YE MAFITA
 Idan muka koma zuwa koyarwar Manzo (S.A.W) ta ainihi, muka kuma yi riko da wasiyyar sa, wacce ya bayyana ta a gurare da yawa wacce kuma take cikin manya manyan litattafan addini, kamar misalin, Sahihan litattafai shida, (sihahus sitti) na cewa yana yi mana wasici da abu biyu littafin Allah da Ahlin gidan sa, hakika Allah ya ba shi lanbarin cewa ba za su rabuwa ba (ku’ani da ahlulbait) har sai sun riske shi a tafki. Don haka sharadin farko shi ne yin riko da wadannan nauyaya (wato masu girma da daraja) guda biyu. Abu na biyu shi ne mu hade kan mu, mu a jiye banbance-banbance a gefe ta yadda za a bawa kowa cikakken yancin fadar fahimtar sa, tare da girmama ra’ayin saura. Domin tabbas hannu daya ba ya daukar jinka, (kada ku yi tashin-tashina sai ku rushe kuma karfin ku ya gushe) kamar yadda Allah Ta’ala, ya ce.
 Anan dole ne mu sa neman ilimi da tsoron Allah Ta’ala a gaba fiye da komai domin ta wannaa hanyar ne kawai zamu iya gano hakika da kuma yadda zamu yi koyi da manzo daidai da zamanin da muke ciki, "madalla da mutumin da ya san zamaninsa ya san addininsa sannan ya daidaita tafarkinsa”
Aminci ya tabbata ga Manzo Muhammad dan Abdullah, ranar da a ka haife shi da ranar da ya koma zuwa ga Allah da ranar da za a tashe shi rayayye.
Aminci ya tabbta a wanda ya bi shiriya
Makomar bincike:
Sahihibukari/ muslim, ds.
Nafahatur risaliyya
 Al-qur’an  
Muhammad rasulullah
Zamu ci gaba a fitowa ta gaba insha’Allah.
 Muhir Muhammad Said.                            

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: