bayyinaat

Published time: 15 ,May ,2018      01:44:47
An rawito daga Allama Hilli cikin risalas Sa'adiyya daga Imam Sadiq (AS): haqiqa duk wani muminin da ya ciyar da mumini loma cikin watan Ramadana Allah zai rubuta masa ladan wanda ya 'yanta bayi muminai talatin, kuma ya na da karvavviyar addu'a wajan Ubangiji.
Lambar Labari: 132
أعمال الإفطار في کل لیلة
الأول: الافطار، ويُستَحب تأخَيره عَن صلاة العشاء إلاّ إذا غلب عَليهِ الضعف أو كانَ له قوم ينتظرونه.
الثاني: أن يفطر بالحلال الخالي مِن الشبهات سّيما التمر، ليضاعف أجر صلاته أربعمائة ضعف، ويحسن الافطار أيضاً بأيٍّ مِن التمر والرطب والحلواء والنبات والماء الحار.
الثالث: أن يدعو عِندَ الافطار بدعوات الافطار المأثورة، منها أن يَقول:
اللّهُمَّ لَكَ صُمْتُ وَعَلى رِزْقِكَ أَفْطَرْتُ وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ.
ليهب الله لَهُ مثل أجر كُل مَن صام ذلِكَ اليَوم.
الرابع: وروي أن أمير المُؤمنين (عليه السلام) كانَ إذا أراد أن يفطر يَقول: 
بِسْمِ اللهِ، اللّهُمَّ لَكَ صُمْنا وَعَلى رِزْقِكَ أَفْطَرْنا، فَتَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ العَلِيمُ.
الخامس: أن يقول عند أوَّل لقمة يأخذها: 
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ، يا واسِعَ المَغْفِرَةِ اغْفِرْ لِي، ليَغفِرَ اللهُ لَهُ.
السادس: وفي الحديث: إنّ الله تعالى يعتق في آخر ساعة مِن نهار كُل يَوم مِن شَهر رَمَضان ألف ألف رقبة، فسل الله تعالى أن يجعلكَ منهم .
السابع: أن يتلو سورة ‌القدر عند الافطار.
الثامن: أن يتصدق عند الافطار، ويفطّر الصائِمين ولو بعدد من التمر أو بشربة مِن الماء. عن النبي (صلّى الله عليه وآله وسلم): انّ مَن فطّر صائماً فَلهُ أجر مثله مِن دون أن ينقص مِن أجره شي، وكانَ له مثل أجر ما عمله مِن الخَير بقّوة ذلِكَ الطعام .
روى آية الله العلامة الحلي في الرسالة السعدية عَن الصادق (عليه السلام): انّ أيّما مؤمَن أطعم مؤمناً لقمة في شَهر رَمَضان كتبَ الله لَهُ أجر مَن أعتق ثلاثين رقبة مؤمنة، وكانَ له عِندَ الله تعالى دعوة مستجابة .
***

AYYUKAN KOWANNE DARE
Na farko: Buxa baki, an so jinkirta shi daga sallar ishsha sai idan jikin sa ya raunana ko kuma gudun idanun mutanen da yake cikin su.
Na biyu: ya yi buxa baki da tsantsar halal musamman ma ya yi da dabino, don ya nunnunka ladan sallar sa zuwa ninki xari huxu, da kowane irin abu ya yi buxa bakin ba komai kamar xanye kayan zaqi da kayan itace ko ruwan zafi.
Na uku: ya yi addu'ar da aka rawaito, shi ne ya karanta:
Allahumma laka sumtu wa ala rizqika afxartu wa alaika tawakkaltu 
(ya Allah kai na yi wa azumi kuma cikin arziqin ka na ke buxa baki gareka na dogara)
Allah zai baka lada kimanin na duk wanxanda su ka azumci wannan ranar.
Na huxu: an rawaito cewa Amirul mumineen (AS) ya kasance idan zai yi buxa baki ya na cewa: 
Bismillahi, Allahumma laka sumna wa ala rizqika afxarna, fataqabbal minna, innaka antas samii'ul aliim, (da sunan Allah, Allah kai mu ka yi wa azumi kuma cikin arziqin ka mu ka buxe baki, ka karvi azumin mu, kai ne mai ji masani).
Na Biyar: yayin da ya xauki lomar farko zai kai bakin sa sai yace:
Bismillahir rahmanir rahiim, ya wasi'ul magfira igfirli, li yagfirallah, (da sunan Allah mai rahama mai jin qai, ya mai mayalwaciyar ni'ima ka gafarta min, Allah ka gafarta masa).
Na shida: cikin hadisi: Allah maxaukakin sarki na 'yanta mutane dubu qarshen kowace awan qarshen kowane daren watan ramadan, ka roqi Allah (SW) ya sanya ka cikin su.
Na bakwai: ya karanta suratul Qadri yayin buxa baki.
Na takwas: ya yi sadaqa yayin buxa baki, ya buxe bakin masu azumi koda da dabino ne ko rowa, an karvo daga Manzo (SAW) cewa: duk wanda ya buxi bakin mai azumi ya na da lada irin na wanda ya yi azumin ba tare da an ragi ladan sa ba, yana kuma da ladan duk wani aikin alheri da mai azumin ya yi da qarfin da ya samu daga cin abincin.
An rawito daga Allama Hilli cikin risalas Sa'adiyya daga Imam Sadiq (AS): haqiqa duk wani muminin da ya ciyar da mumini loma cikin watan Ramadana Allah zai rubuta masa ladan wanda ya 'yanta bayi muminai talatin, kuma ya na da karvavviyar addu'a wajan Ubangiji.
***
 
دعاهای مستحب در هر شب ماه مبارک
روى السيّد أنّ مَن قالَ هذا الدُّعاء في كُل لَيلَة مِن شَهر رَمَضان غفرت له ذنوب أربعين سنة: 
اللهم رَبَّ شَهْرِ رَمَضَانَ، الَّذِي أَنْزَلْتَ فِيهِ الْقُرْآنَ، وَافْتَرَضْتَ عَلَى عِبَادِكَ فِيهِ الصِّيَامَ، صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ، وَارْزُقْنِي حَجَّ بَيتِكَ الْحَرَامِ، فِي عَامِي هَذَا وَفِي كُلِّ عَامٍ، وَاغْفِرْ لِي تِلْكَ الذُّنُوبَ الْعِظَامَ، فَإِنَّهُ لا يَغْفِرُهَا غَيرُكَ، يَا رَحْمَانُ يَا عَلاّمُ .

ADDU'A TA MUSTAHABBI CIKIN KOWANNE DAREN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA
Sayyid ya rawaito cewar duk wanda ya karanta wannan addu'ar cikin kowane dare cikin watan ramadana za'a gafarta masa zunuban sa na shekara arba'in:
Ya ubangijin watan ramadana, wanda ka saukar da qur'ani a cikin sa, ka wajabtawa bayin ka azumi a cikin sa, ka yi salati ga Annabi Muhammad da Iyalan sa, ka azurta ni ziyartar xakin ka mai alfarma, cikin wannan sekkarar da ma kowacce, ka gafarta min waxancan manyan zunuban masu girma, domin ba mai gafarta su idan ba kai ba, ya mai rahama maxaukaki.
***

اللهم بِرَحْمَتِكَ فِي الصَّالِحِينَ فَأَدْخِلْنَا، وَفِي عِلِّيِّينَ فَارْفَعْنَا، وَبِكَاسٍ مِنْ مَعِينٍ مِنْ عَينٍ سَلْسَبِيلٍ فَاسْقِنَا، وَمِنَ الْحُورِ الْعِينِ بِرَحْمَتِكَ فَزَوِّجْنَا، وَمِنَ الْوِلْدَانِ الْمُخَلَّدِينَ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَكْنُونٌ فَأَخْدِمْنَا، وَمِنْ ثِمَارِ الْجَنَّةِ وَلُحُومِ الطَّيرِ فَأَطْعِمْنَا، وَمِنْ ثِيَابِ السُّنْدُسِ وَالْحَرِيرِ وَالْإِسْتَبْرَقِ فَأَلْبِسْنَا، وَلَيلَةَ الْقَدْرِ وَحَجَّ بَيتِكَ الْحَرَامِ وَقَتْلاً فِي سَبِيلِكَ فَوَفِّقْ لَنَا، وَصَالِحَ الدُّعَاءِ وَالْمَسْأَلَةِ فَاسْتَجِبْ لَنَا، يَا خَالِقَنَا اسْمَعْ وَاسْتَجِبْ لَنَا، وَإِذَا جَمَعْتَ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَارْحَمْنَا، وَبَرَاءَةً مِنَ النَّارِ فَاكْتُبْ لَنَا، وَفِي جَهَنَّمَ فَلا تَغُلَّنَا، وَفِي عَذَابِكَ وَهَوَانِكَ فَلا تَبْتَلِنَا، وَمِنَ الزَّقُّومِ وَالضَّرِيعِ فَلا تُطْعِمْنَا، وَمَعَ الشَّيَاطِينِ فَلا تَجْعَلْنَا، وَفِي النَّارِ عَلَى وُجُوهِنَا فَلا تَكُبَّنَا، وَمِنْ ثِيَابِ النَّارِ وَسَرَابِيلِ الْقَطِرَانِ فَلا تُلْبِسْنَا، وَمِنْ كُلِّ سُوءٍ يَا لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، بِحَقِّ لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ فَنَجِّنَا
 .
Ya Allah ka shigar da ni cikin salihan bayin ka, ka xaga mu cikin maxaukaka, ka shayar da mu daga idanuwar ruwan salsabiil, ka aura mana hurul iini don girman rahamar ka, ka hidimta min da 'ya'ya na dindindin masu kama da lu'u-lu'un da aka boye, ka ciyar da mu 'ya'yan itaciya da naman tsuntsayen gidan al'janna, ka sanya min kaya alhariri mai walqiya, ka datar da mu daren lailatul da ziyartar xakin ka da kuma yaqi a tafarkin ka, ka amsa mana kyawawan roqon mu da barar mu gare ka, ya mahaliccin mu ka ji roqon mu ka amsa mana, idan muka taru na farkon mu da na qarshen mu ka rahamshe mu, ka rubuta mu cikin kuvutattu daga wuta, kada ka sanya mu cikin jahannama, kada ka jarrabce mu da kasqantarwar ka da azabar ka, kada ka ciyar da mu daga zaqqum, kada ka sanya mu tare da shaixanu, kada ka sanya wuta a fusakun mu, kada ka sanya mana tufafin wuta da rigar gol tar, ka kare mu daga dukkan mummunan abu ya wanda babu wani ubangiji sai shi, ka tseratar da mu don darajar ka amatsayin ka na wanda babu wani ubangiji sai kai.
***

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: