bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:03:17
Tarihin rayuwar mace yana cike da duhu a cikin al'ummu sakamakon danniya da ta fuskanta a cikinsu, sakamakon haka ne Allah madaukaki ya aiko da 'yan sako a cikin lokuta da marhaloli da zamuna mabambanta
Lambar Labari: 135
A nan muna son kawo wasu bayanai masu takaituwar gaske a dunkule game da irin wannan halaye da mace ta samu kanta ciki na danniya a tsawon tarihin rayuwar dauloli da kasashe don matan da suka samu kansu cikin ni'imar shiriyar Allah su gode masa da kara yabo gare shi. 
MARHALOLIN TARIHIN MACE
Tarihin rayuwar mace yana cike da duhu a cikin al'ummu sakamakon danniya da ta fuskanta a cikinsu, sakamakon haka ne Allah madaukaki ya aiko da 'yan sako a cikin lokuta da marhaloli da zamuna mabambanta, zuwa ga al'ummun nahiyoyin wannan duniyar domin su fitar da su daga wannan duhun zuwa ga haske. Sai dai a ko da yaushe suka juya baya sai al'ummu su sake koma wa cikin al'adunsu, su dulmuya cikin duhunsu, su ci gaba da fandare wa ubangijinsu.
Afrika da Gabas
Sau da yawa akan yi tambaya mene ne hakikanin mace,matsayinta, tasirinta, hakkokinta, tarihinta, da marhalar da ta wuce a cikinal'ummu? Amsar wadannan tambayoyi tana iya baiyana cikin bincike da zamu yi a kan mace a al’ummu, da addinai a takaice. 
Idan muka duba rayuwar mace a al’ummun wasu yankunan Australiya, da wasu yankunan Afrika, da Tsibiran Rasha, da na Tekun Pasifik, da Tsohuwar Amurka, rayuwar tasu tana daidai da rayuwar dabbobi ko ma kasa da hakan,domin a yawacin wadannan yankuna namiji yana da ikon mallakarta ya amfana daga gare ta kamar dabba . 
 A wasu wurare suna ganin kamar an yi ta ne don namiji kawai, samuwarta kafin aure da bayan aure tana bin ta maza ne, a wasu wurare ana sayar da su ne ba aura ba, ana ma iya bayar da rancensu, da aronsu, domin ta haihu ko ta yi wata hidima, har ma ana iya kashe ta kuma babu kisasi. Dukiyarta kuwa ta namiji ce haka ma duka wani abu da ta mallaka, haka ma komai na gida na wahala yana kanta kamar hidimar ‘ya’ya, da bukatun namiji, da sana’a, kuma dole ta jure ba yadda za ta yi . 
Ana iya ganinta ne a taron mata idan ya shafi gida kawai amma duk wani lamari ko taro na addini da ya shafi al’umma gaba daya to a nan wani abin mamaki ne a ga mace. Haka ma ba a san ta ba a lamarin shugabantar kungiya ko taron jama’a sai a wasu wurare. Idan kuwa aka koma fagen ilimi to babu wata kofa da aka bude wa mata. 
Tsofaffin Addinai
 Al’ummu da dauloli suna da al’adu mabambanta, wasu gada ake yi wasu kuma ana tasirantuwa da su ne ta hanyar zamantakewa a wani waje ko kuma daga yanayin dabi'ar wuri. Bari mu ga mace a al’ummu daban-daban da ba su da littafi na doka da aka saukar daga sama, kamar Tsohuwar Kasar Sin, Indiya, Masar, da Farisa, wadanda sun yi taraiya wajan rashin ba wa mace ‘yancinta. 
Mace ba ta da 'yanci ko da na nufi da abin da take so, da na aiki, ko cin gashin kanta, ana tilasata mata taraiya cikin duk wahala, da kebantuwa da aikin gida. Sai dai tana da dan ‘yancin rayuwa cikin al’ummar da take domin a wasu al’ummu ta kan yi gado da aure duk da ba ta da wani cikkakken ‘yanci, namiji ya kan yi aure ba iyaka a wajansu ya kuma kori wacce ya so, idan ya mutu ba ta isa ta yi wani aure ba amma shi namiji yana da hakkin wannan, kuma har ila yau a mafi yawancin daulolin namiji yana iya taskace ta a gida ko duk inda ya so. 
Haka ma Farisa a zamanin da tsarin dabakoki ya haifar wa dangin sarauta halaccin iya auren dangi domin ka da jinin ya watsu a cikin wasunsu, sai aka haramta wa mace auren talaka kuma aka taskace iradarta da abin da gidan sarauta ya ga dama kawai. Ko da yake ta wani bangare wannan tsarin ya rage kaifin zalunci kan dabakar mata saboda damar rike sarauta da tafiyar da al’amuran hukuma da ‘Ya’yan sarki mata suka samu . 
Wani lokaci kuwa zaluncin kwace kyawawan mata da sarakuna suke yi ne ya taimaka wajan haifar da wasu tunani a tarihin wasu al’ummu kamar na ‘yan tunanin Mazdak da saboda zaluncin ne suka yi tawaye suka haifar da wata fikira mai ganin cewa; Ai mace kamar sauran kaya ne don haka duk wacce ka hadu da ita mallakarka ce. 
Kasar Sin da Indiya
A Tsohuwar kasar Sin (Chana) kuwa auren mace kamar saye ne da mallaka, sannan ba ta da gado, kuma ba a cin abinci tare da ita ko da tare da ‘ya’yanta ne, Kuma maza da yawa suna iya taraiya a kan mace daya kamar yadda ake hada hannu wajan sayan doki daya kuma kowannensu yana da ikon jin dadi da ita, sai dai ‘ya’yanta na wanda ya fi saura karfi ne . 
Indiyawa suna da dokokin da suka kebanci mata kawai, a kasar Indiya an hana mace kallon bakar fatar asalin yankin  masu shan wahalar wariyar launin fata, wasu masana suna ganin cewa Ariyawa  sun sanya wannan dokar kan mata ne domin kada mace farar fata ‘yar kabilar Ariyawa ta ji tana son Bakar fata. Ba su tsaya a nan ba sai da suka sake hana mata taba duk wani abu da wadannan kabilu suka taba. Kasancewar hukuncin ya kebanta da mace kawai yana nuna mana irin wariya da mace ta ke fama da ita a fagage daban-daban na rayuwa a Indiya . 
A Indiya mace na bin mijinta ne a samuwa, kuma ba ta da ikon yin aure bayan mutuwarsa, ana kona ta  da ranta ne tare da gawar mijinta abin da aka fi sanin da "Sati" . A Addinin Hindu idan mata suna haila to sun zama dauda haka ma duk abin da suka taba da tufafinsu, kuma dole ne a nisance su, haka nan suna ganin cewa; ita wata halitta ce tsakanin mutum da dabbobi . A Littafinsu na dokokin addini mai suna "Manu Dhrama Sastra” a Babin bayani game da mace ya zo cewa: 
Dole ne mace ta zama ba ta da zabi a kan kanta ko yarinya ce, ko tsohuwa, ‘ya ta ubanta ce, kuma mata ta mijinta ce, uwar marayu tana karkashin ‘ya’yanta ne. Mace ba ta isa ta ci gashin kanta ba har abada, kuma dole ta yarda da wanda babanta ya zaba mijinta har abada, ta yi wa miji hidima har mutuwa kuma ba ta isa ta yi wani miji ba idan ya mutu ko ta yi tunanin wani miji bayan mutuwarsa. 
Kuma dole ne yayin nan ta bar duk wani abu da take marmari ko kwadayi na ci mai dadi ko tufafi mai kyau da duk wani ado har rayuwarta ta kare, idan mijinta ba ya son ta yana bin wata matar kada ta sake ta ji haushi kuma ba ta da ikon takaita masa hidima da neman yardarsa. Aljannarta  tana karkashin mijinta kada ta yi wani abu sai da yardarsa. Uban yarinya kada ya ci sadaki ko yaya daga ciki, in ko ya yi haka daidai yake da wanda ya sayar da ita. 
Duba ku ga yadda mace ba ta da ikon tunani ko sanya mai kyau ko cin abin da take marmari ko aure don mijinta ya mutu, wato da ana an gwanci ya mutu shi ke nan ta gama aure har ta mutu koda kuwa za ta shekara dari a Duniya, sannan kuma ba ta da ikon tunani a kan makomarta.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Web Site: www.haidarcenter.com
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: