bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:15:28
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna game da saukar surorin nan biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa: an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haɗa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah)
Lambar Labari: 137
سورة الناس
SURATUN NAAS (SURA TA 114)
DALILIN SAUKA
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna game da saukar surorin nan biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa: an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haɗa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah) sai ya zama kamar yadda su ke cewa a waɗannan ruwayoyin na su wai Manzon (SAW) na jin kamar ya yi wani abu amman wai bai yi ba, sai ya ji kamar ya zo gida amman bai zo ba, kamar ya jewa iyalan sa amman bai je ba. 
Mabiya Imam Ali (AS) da ƴaƴan sa sun yi raddin wannan magana raddi mai tsanani su na ganin wannan maganar da ta fito daga yan uwan mu ahlussunna an ƙirƙiro tane kawai don a rusa musulunci, ana son nuna cewa wani abu zai iya tasiri kan ruhi mai tsarki na Manzo (SAW), alhalin idan ka ga wani ya yi tasiri kan ruhin wani, ruhin mai tasirin ya fi ƙarfi, shi kuwa manzo (SAW) ya na tattare ne da ruhil ƙuds alhalin ba zai yiyu wanda bashi da ruhil ƙuds ya yi tasiri kan wanda ke da ruhil ƙuds ba, musamman ma irin na Manzo (SAW) da ya fi na kowa ƙarfi, wannan ba zai taɓa yiyuwa ba, sannan  duk wanda ke da ruhil ƙuds Allah na bashi kariya daga dukkan wani abu da zai iya taɓa hankalin su har abada ba zai yiyu ba, ran su na da ƙarfi sosan gaske, ba wani abu da ya fi shi ƙarfi, kuma duk abinda su ka so su yi da izinin Allah za su iya, kamar yadda ya zo a ƙurani mai girma da ruwayoyi.
Matsalar da kan iya biyo bayan waccen magana ta ahalussuna shine: kenan zai yiyu a saukar masa da wahayi ya manta ko kuma ba'a saukar ba ya zata cewa an saukar masa, ko ya zata ya isar da wani saƙo ashe bai isar ba, don haka wancccen ruwaya da tunani na su idan aka bi shi ba inda zai kai musulunci sai ga rushewa, Allah ya kare mu.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ (1) 
Ka ce, ina neman tsarin ubangijin mutane (samar wa mutane da komai ta ɓangarorin rayuwar su ta yau da gobe, duk da cewa ya kan wakilta mala'iku wajan aiwatar da wasu daga mafiya yawan ayyukan sa, ta hanyar sunan da ke tajalli kan kowane mala'ika don gudanar da aiyyukan sa, wannan duk na nuna cewa ayyukan na zuwa ne daga ubangijin halittu domin komai sai da izinin sa).

مَلِكِ النَّاسِ (2)
Mamallakin mutane (wanda ke tafiyar da su tare da jujjuya samuwar su shi kaɗai tal).

إِلَهِ النَّاسِ (3)
Abin bautar mutane (ɗaya tal ba tare da abokin tarayya ba).

مِنْ شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ (4)
Daga sharrin mai waswasi mai ɓoyewa/buya (duk wannan kira da ka yi wa ubangiji da kiran sa, mamallai, abin bauta da ubangiji duk kana neman taimakon sa ne kan ya kare ka daga sharrin mai waswasi mai ɓuya/ɓoyewa, kuma shaiɗan na ciki kamar yadda mu ka yi bayani a baya.

الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ (5) 
Wanda ke waswasi cikin zukata/ƙirazan mutane (a nan shaiɗan ya yi ɓuyan da za mu iya kiran sa silence killer gano irin waɗannan ɓoyayyar gadar zare na da wuya sai dai luɗufin Allah kawai, ya yi ɓuyan da mutum kan iya aikata aiki a sunan daidai amman yana ɓarna bai sani ba, Allah ya kare mu daga irin waɗannan sharruka na shaiɗan).

مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ (6)
Daga al'janu da mutane (bayanin da mu ka yi a baya ya kara fitowa fili, wannan aya na nuna cewa shaiɗanin ka na iya zama mutum ko al'janu da sauran halittu kafin ya zama iblis da kan sa, kamar yadda mu ka faɗa a baya cikin fassarar ta'awizi cewa iblis na da wakilai iri – iri cikin halittun ubangiji.

Don neman faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: