bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:29:16
Daga Imam Sadiq (AS) ya ce: ana faxa cikin kowane daren lailatul qadri na watan ramadana cewa: Ya Allah ina roqonka ka sanya ni cikin waxanda ka qaddara tare da aiwatarwa, cikin lamarin da ka sanya hannun sa
Lambar Labari: 139
Ramadan III

عن الصادق (عليه السلام) قال: تقول في كُل لَيلَة مِن شَهر رَمَضان:
اللهم إِنِّي أَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ فِيمَا تَقْضِي وَتُقَدِّرُ، مِنَ الْأَمْرِ الْمَحْتُومِ، فِي الْأَمْرِ الْحَكِيمِ، مِنَ الْقَضَاءِ الَّذِي لا يُرَدُّ وَلا يُبَدَّلُ، أَنْ تَكْتُبَنِي مِنْ حُجَّاجِ بَيتِكَ الْحَرَامِ، الْمَبْرُورِ حَجُّهُمْ، الْمَشْكُورِ سَعْيُهُمْ، الْمَغْفُورِ ذُنُوبُهُمْ، الْمُكَفَّرِ عَنْهُمْ سَيِّئَاتُهُمْ، وَأَنْ تَجْعَلَ فِيمَا تَقْضِي وَتُقَدِّرُ، أَنْ تُطِيلَ عُمُرِي فِي خَيرٍ وَعَافِيَةٍ، وَتُوَسِّعَ فِي رِزْقِي، وَتَجْعَلَنِي مِمَّنْ تَنْتَصِرُ بِهِ لِدِينِكَ، وَلا تَسْتَبْدِلْ بِي غَيرِي .

Daga Imam Sadiq (AS) ya ce: ana faxa cikin kowane daren lailatul qadri na watan ramadana cewa:
Ya Allah ina roqonka ka sanya ni cikin waxanda ka qaddara tare da aiwatarwa, cikin lamarin da ka sanya hannun sa, cikin qaddarar da bazata canju ko ta juya ba, ka rubuta ni cikin mahajjatan xakin ka mai albarka, masu karvavven hajji, masu dace ababan godiya, waxanda aka gafarta musu zunuban su, kuma aka kankare munanan ayyukan su, ka sanya cikin abinda ka hukunta ka qaddara, ka tsawaita rayuwa ta cikin alheri da lafiya, ka yalwata arziqi na, ka sanya ni cikin waxanda ka ke taimakon addinin ka, kada ka canja ni da wani na.
***

الهِي وَقَفَ السَّائِلُونَ بِبابِكَ، وَلاذَ الفُقَراءُ بِجَنابِكَ، وَوَقَفَتْ سَفِينَةُ المَساكِينِ عَلى ساحِلِ بَحْرِ جُودِكَ وَكَرَمِكَ، يَرْجُونَ الجَوازَ إِلى ساحَةِ رَحْمَتِكَ وَنِعْمَتِكَ. إِلهِي، إِنْ كُنْتَ لاتَرْحَمُ فِي هذا الشَّهْرِ الشَّرِيفِ إِلاّ مَنْ أَخْلَصَ لَكَ فِي صِيامِهِ وَقِيامِهِ، فَمَنْ لِلْمُذْنِبِ المُقَصِّرِ إِذا غَرِقَ فِي بَحْرِ ذُنُوبِهِ وَآثامِهِ؟ إِلهِي إِنْ كُنْتَ لاتَرْحَمُ إِلاّ المُطِيعِينَ، فَمَنْ لِلْعاصِينَ؟ وَإِنْ كُنْتَ لاتَقْبَلُ إِلاّ مِنَ العامِلِينَ، فَمَنْ لِلْمُقَصِّرِينَ؟ إِلهِي رَبِحَ الصَّائِمُونَ، وَفازَ القَائِمُونَ، وَنَجا المُخْلِصُونَ، وَنَحْنُ عَبِيدُكَ المُذْنِبُونَ، فَارْحَمْنا بِرَحْمَتِكَ، وَاعْتِقْنا مِنَ النَّارِ بِعَفْوِكَ، وَاغْفِرْ لَنا ذُنُوبَنا، بِرَحْمَتِكَ يا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ

Ya Allah maroqa sun tsaya a qofar ka, talakawa sun xanxani zaqin kusantar ka, jirgin ruwan miskinai ya tsaya a gefen kogin kyautar ka da girman ka, su na neman sakamakon yalwar rahamar ka da Ni;imar ka. Ya Allah idan baka zama mai rahama cikin wannan wata sai ga wanda ya tsarkake tsaiwar sa da azumin sa gare ka, ya kuma ga mai zunubin da ya gaza lokacin da ya nutse cikin kogin zunuban sa da savon sa? Ya Allah idan baka rahama sai ga masu yi maka biyayya. Ya kuma ga masu sava maka? Idan baka karvar aiki sai daga masu aiki, ya kuma ga waxanda su ka gaza? Ya Allah masu azumi sun ribata, ma su tsayuwa sun raabauta, masu tsarkake niyya sun tsira, mu kuma gamu bayin ka masu zunubai, ka yi mana rahama da afuwar ka, ka 'yanta mu daga wuta da afuwar ka, ka gafarta mana zunuban mu, da rahamar ka ya mai jin qan masu jin qai.
***
أدع في كلّ ليلة مِن ليالي شهر رمضان:
أَعُوذُ بِجَلالِ وَجْهِكَ الْكَرِيمِ أَنْ يَنْقَضِيَ عَنِّي شَهْرُ رَمَضَانَ، أَوْ يَطْلُعَ الْفَجْرُ مِنْ لَيلَتِي هَذِهِ، وَلَكَ قِبَلِي ذَنْبٌ أَوْ تَبِعَةٌ تُعَذِّبُنِي عَلَيهِ؛
Ka yi wannan addu'ar cikin dararen watan Ramadan:
Ina neman tsarin Allah don girman fuskar sa mai girma da da yankewar watan ramadana gareni, ko al'fijir ya ketomin daga cikin darare na, gashi ina da zunubai masu yawa ko wata matafiya da zaka azabtar da ni matuqar ina kanta,
***

إِلهِي! وَقَفَ السَّائِلُونَ بِبابِكَ، وَلاذَ الفُقَراءُ بِجَنابِكَ، وَوَقَفَتْ سَفِينَةُ المَساكِينِ عَلى ساحِلِ بَحْرِ جُودِكَ وَكَرَمِكَ، يَرْجُونَ الجَوازَ إِلى ساحَةِ رَحْمَتِكَ وَنِعْمَتِكَ؛ إِلهِي! إِنْ كُنْتَ لاتَرْحَمُ فِي هذا الشَّهْرِ الشَّرِيفِ إِلاّ مَنْ أَخْلَصَ لَكَ فِي صِيامِهِ وَقِيامِهِ، فَمَنْ لِلْمُذْنِبِ المُقَصِّرِ إِذا غَرِقَ فِي بَحْرِ ذُنُوبِهِ وَآثامِهِ؟ إِلهِي! إِنْ كُنْتَ لاتَرْحَمُ إِلاّ المُطِيعِينَ فَمَنْ لِلْعاصِينَ؟ وَإِنْ كُنْتَ لاتَقْبَلُ إِلاّ مِنَ العامِلِينَ فَمَنْ لِلْمُقَصِّرِينَ؛ إِلهِي! رَبِحَ الصَّائِمُونَ، وَفازَ القَائِمُونَ، وَنَجا المُخْلِصُونَ، وَنَحْنُ عَبِيدُكَ المُذْنِبُونَ، فَارْحَمْنا بِرَحْمَتِكَ، وَاعْتِقْنا مِنَ النَّارِ بِعَفْوِكَ، وَاغْفِرْ لَنا ذُنُوبَنا، بِرَحْمَتِكَ يا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ.

Allah na! Maroqa sun tsaya a qofar ka, talakawa sun xanxani zaqin kusantar ka, jirgin ruwan miskinai ya tsaya a gefen kogin kyautar ka da girman ka, su na neman sakamakon yalwar rahamar ka da Ni;imar ka. Ya Allah idan baka zama mai rahama cikin wannan wata sai ga wanda ya tsarkake tsaiwar sa da azumin sa gare ka, ya kuma ga mai zunubin da ya gaza lokacin da ya nutse cikin kogin zunuban sa da savon sa? Ya Allah idan baka rahama sai ga masu yi maka biyayya. Ya kuma ga masu sava maka? Idan baka karvar aiki sai daga masu aiki, ya kuma ga waxanda su ka gaza? Ya Allah masu azumi sun ribata, ma su tsayuwa sun raabauta, masu tsarkake niyya sun tsira, mu kuma gamu bayin ka masu zunubai, ka yi mana rahama da afuwar ka, ka 'yanta mu daga wuta da afuwar ka, ka gafarta mana zunuban mu, da rahamar ka ya mai jin qan masu jin qai.
***

الدعاء الذي رواه الكليني في الكافي عن الصادق (عليه السلام) قال: تقول في العشرة الأواخر مِن شَهر رَمَضان کل ليلة: 
أَعُوذُ بِجَلالِ وَجْهِكَ الكَرِيمِ أَنْ يَنْقَضِيَ عَنِّي شَهْرُ رَمَضانَ أَوْ يَطْلُعَ الفَجْرُ مِنْ لَيْلَتِي هذِهِ وَلَكَ قِبَلِي ذَنْبٌ أَوْ تَبِعَةٌ تُعَذِّبُنِي عَلَيْهِ.
Addu'ar da aka rawaito daga Kulainy cikin Kafy daga Imam Sadiq (AS) ya ce: ka karanta wannan addu'ar cikin kowane daren goman qarshe na watan ramadana:
Ina neman tsarin Allah don girman fuskar sa mai girma da da yankewar watan ramadana gareni, ko al'fijir ya ketomin daga cikin darare na, gashi ina da zunubai masu yawa ko wata matafiya da zaka azabtar da ni matuqar ina kanta,
***

أعمال الأسحار
 الأول: أن يتسحّر، فلا يدع السحور ولو على حشفة تمر أو جرعة مِن الماء، وأَفضَل السحور السويق والتمر، وفي الحديث: أن الله وملائكته يصلونَ عَلى المستغفرين والمتسحّرينَ بالاسحار.
الثاني: أن يقرأ عِندَ السحور سورة إِنا أنزلناهُ، فَفي الحديثِ: ما مِن مؤمَن صام فقرأ إنّا أنزلناه في لَيلَة القَدر عِندَ سحوره وعِندَ إفطاره إِلاّ كانَ فيما بينهما كالمتشحط بدمه في سبيل الله.
الثالث: أن يدعو بهذا الدُّعاء العَظيم الشان الَّذي روي عَن الرضا (عليه السلام) أنه قال: هو دعاء الباقر (عليه السلام) في أسحار شَهر رَمَضان:
اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ بَهائِكَ بِأَبْهاهُ، وَكُلُّ بَهائِكَ بَهِيُّ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِبَهائِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ جَمالِكَ بِأَجْمَلِهِ، وَكُلُّ جَمالِكَ جَمِيلٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِجَمالِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ جَلالِكَ بِأَجَلِّهِ، وَكُلُّ جَلالِكَ جَلِيلٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِجَلالِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ عَظَمَتِكَ بِأَعْظَمِها، وَكُلُّ عَظَمَتِكَ عَظِيمَةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِعَظَمِتِكَ كُلِّها، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ نُورِكَ بِأَنْوَرِهِ، وَكُلُّ نُورِكَ نَيِّرٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِنُورِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ رَحْمَتِكَ بِأَوْسَعِها، وَكُلُّ رَحْمَتِكَ وَاسِعِةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِرَحْمَتِكَ كُلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ كَلِماتِكَ بِأَتَمِّها، وَكُلُّ كَلِماتِكَ تامَّةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِكَلِماتِكَ كُلِّها، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ كَمالِكَ بِأَكْمَلِهِ، وَكُلُّ كَمالِكَ كامِلٌ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِكَمالِكَ كُلُّهِ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ أَسْمائِكَ بِأَكْبَرِها، وَكُلُّ أَسْمائِكَ كَبِيرَةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَسْمائِكَ كُلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ عِزَّتِكَ بِأَعَزِّها، وَكُلُّ عِزَّتكَ عَزِيزَةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِعِزَّتِكَ كُلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ مَشِيَّتِكَ بِأَمْضاها، وَكُلٌ مَشِيَّتِكَ ماضِيَةٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِمَشِيَّتِكَ كُلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ قُدْرَتِكَ بِالقُدْرَةِ الَّتِي اسْتَطَلْتَ بِها عَلى كُلِّ شَيْءٍ، وَكُلُّ قُدْرَتِكَ مُسْتَطِيلَةٌ، اللّهم إِنّي أسألُك بقدرتِك كلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ عِلْمِكَ بِأَنْفَذِهِ، وَكُلُّ عِلْمِكَ نافِذٌ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِعِلْمِكَ كُلِّهِ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ قَوْلِكَ بِأَرْضاهُ، وَكُلُّ قَوْلِكَ رَضِيُّ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِقَوْلِكَ كُلِّهِ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ مَسائِلِكَ بِأَحَبِّها إِلَيْكَ، وَكُلُّها إِلَيْكَ حَبِيبَةٌ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِمَسائِلِكَ كُلِّها؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ شَرَفِكَ بِأَشْرَفِهِ، وَكُلُّ شَرَفِكَ شَرِيفٌ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِشَرَفِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ سُلْطانِكَ بِأَدْوَمِهِ، وَكُلُّ سُلْطانِكَ دائِمٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِسُلْطانِكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ مُلْكِكَ بِأَفْخَرِهِ، وَكُلُّ مُلْكِكَ فاخِرٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِمُلْكِكَ كُلِّهِ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ عُلُوِّكَ بِأَعْلاهُ، وَكُلُّ عُلُوِّكَ عالٍ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِعُلُوِّكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ مَنِّكَ بِأَقْدَمِهِ، وَكُلُّ مَنِّكَ قَدِيمٌ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِمَنِّكَ كُلِّهِ، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ آياتِكَ بِأَكْرَمِها، وَكُلُّ آياتِكَ كَرِيمَةٌ؛ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِآياتِكَ كُلِّها، اللّهُمَّ إِنِّي‌أَسْأَلُكَ بِما أَنْتَ فِيهِ مِنَ الشَّأْنِ وَالجَبَرُوتِ، وَأَسْأَلُكَ بِكُلِّ شَأْنٍ وَحْدَهُ وجَبَرُوتٍ وَحْدَها، اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِما تُجِيبُنِي حِينَ أَسْأَلُكَ، فَأَجِبْنِي يااَللهُ.
ثم سَلْ حاجتكَ فإنها تقضى البتة.

AYYUKAN SAHUR
Na farko: ya yi sahur, kada ya bar sahur koda da tsagin dabino ne ko da maqwarwar ruwa daya ce, mafifcin sahur shi ne sahur da saweeq (abincin ne da ake yin sa da alkama ake cin sa da dabino ko zuma)  da dabino, ya zo cikin hadisi cewa: Allah da mala'ikun sa na yin salati ga masu istigfari da yin sahur tare da masu sahur.
Na biyu: ya karanan suratul qadri lokacin sahur, ya zo cikin hadisi cewa: babu wani mumini da zai yi azumi sannan ya karanta suratul qadri lokacin sahur xin sa da buxa bakin sa har sai ya zama daidai ya bada jinin sa sabida Allah.
 Na uku: ya yi addu'a da wannan addu'ar mai girman sha'ani daga Imam Ridha (AS) ya faxa cewa: addu'ar Imam Baqir (AS) ce cikin sahur xin watan ramadan:
Ya Allah ina roqon ka don haskakawar ka da kyan ta, domin dukkan haskakawar ka haskakakkiya ce, ya Allah ina roqon ka da haskakawar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don kyawunka da dukkan kyaun sa, domin kyawun ka kyakykyawa ne, ya ubangiji ina roqon ka daga da kyauwun ka dukkan sa. Ya Allah ina roqon ka don buwayar ka mabuwayiya, don dukkan buwayar ka mabuwayiya ce, ya ubangiji ina roqon ka don buwayar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don girman ka da dukkan girman sa, dukkan girman ka mai girma ne, ubangiji ina roqon ka don don girman ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don hasken ka da haskakwar sa, kuma dukkan hasken ka mai haske ne, ubangiji ina roqon ka don hasken ka dukkan sa. Ya Allah ina roqon ka don rahamar ka da faxin ta, domin rahamar ka mai faxi ce, ubangiji ina roqon ka don rahamar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don kalmomin ka da cikar su, domin dukkan kalmomin ka cikakku ne, ya ubangiji ina roqon ka don girman kalmomin ka dukkan su. Ya Allah ina roqon ka don girman cikar ka da cikar ta, dukkan cikar ka ciakkyia ce, ubangiji ina roqon ka don cikar ka da girman ta, Ya Allah ina roqon ka don sunayen ka da girman su, domin dukkan sunayen ka masu girma ne, ubangiji ina roqon ka don sunayen ka masu girma, ya Allah ina roqon ka don izzar ka da izzar ta, domin izzar ka mai izza ce, ubangiji ina roqon don izzar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don nufin ka mai qarfin cika, domin nufin ka mai cika ne, ubangiji ina roqon ka don nufin ka mai cika, Ya Allah ina roqon ka don ikon ka mai aiwatar da dukkan komai, domin ikon ka mai zartuwa ce ubangiji ina roqon ka don ikon ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don ilimin ka da tabbatuwar sa, domin dukkan ilimin ka tabbatacce ne, ubangiji ina roqon ka don ilimin ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don zancen ka da yarjewar sa, domin zancen ka yardajje ne ubangiji ina roqon ka don zancen ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don roqon ka da soyuwar ka gareshi, dukkan roqon da aka yi maka abin so ne wajan ka, ubangiji ina roqon ka do roqon ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don xaukakar da xaukakar ta, domin dukkan xaukakar ka xaukakakkiya ce, ubangiji ina roqon ka don xaukakar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don mulkin ka da dauwwamar sa, domin mulkin ka dauwwamamme ne, ubangiji ina roqon ka don dawwamar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don mulkin ka da alfaharin sa, domin mulkin ka abin alfahari ne, ubangiji ina roqon ka don mulkin ka dukkan sa, Ya Allah ina roqon ka don xaukakar ka da xaukakar ta, don dukkan xaukakar ka maxaukakiya ce, ubangiji ina roqon ka don xaukakar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don kyautar ka wacce kan gudana kafin mai ita ya sani, domin dukkan kyautar ka mai gabata ce, ubangiji ina roqon ka don kyautar ka dukkan ta, Ya Allah ina roqon ka don ayoyin ka da girman su, domin dukkan ayoyin ka masu girma ne, ubangiji ina roqon ka don ayoyin ka dukkan su, Ya Allah ina roqon ka don abinda ka ke cikin sa na daga dogaro da kai da xaukaka, ina roqon ka don dukkan sha'nin ka shi kaxai da xaukakar ka ita kaxai ya Allah ina roqon ka da abinda ka amsa min yayin da nake roqon ka, ka amsa min ya Alla.
Sannan ka roqi buqatar ka za a biya maka in Allah ya yadda.
***
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: