bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:52:00
Ka sani cewa lallai zurfafar musibar karbala da kuma zurfafar sirrikanta da ke bayan hakan daga ilimummuka na sanain Allah wanda babu mai iya riskarsu hakikanin riska face Ahlul-baiti (a.s) misalinsu ke cewa
Lambar Labari: 142

Da sunan Allah mai rahama nmai jin kai

Mene ne ya fi kyawu da kayartawa daga abin da gwagganmu Hurriya Zainabul Kubura (a.s) ta bada labari da goben `dan’uwanta Husaini (a.s) kamar yadda ya zo cikin littafin Alkamilul ziyarat da isnadinsa daga majibancinmu kakanmu Imam Zainul Abidin shugaban masu sujjada Ali ibn Husaini (a.s) ya ce: lokacin da abin da ya faru ya faru damu a garin daffi da kashe babana (a.s) aka kuma kashe wadanda suka kasance tare da shi daga `ya`yansa da `ya’uwansa da sauran iyalansa aka dora matayensa masu alfarmarsa kan dokkai ba tare da siddi ba aka nufi kufa damu sai na dinga kallon gawarwakinsu kwance kan kasa ba tare da an binne su ba kai hakan ya girmama cikin kirjina ya tsananta damuwata, raina ya kusa fita sai gwaggona Zainabul Kubra diyar Ali (a.s) ta fuskanci halin da nake ciki sai tace: yaya nake ganinka kana kyauta da ranka ya kai wanda kai ragowa daga zuriyar kakana da babana da `yan’uwana?

Sai na ce: yaya bazan yi raki da gigita bacin ina kallon shugabana da `yan’uwana da baffanena da iyalina suna jike cikin jinanensu an barsu kwance kan tsaurin kasa an yi musu kwacen hakki anbar su ba tare da likkafani ba a binne gawarwakinsu ba babu wanda ya zo wajensu ko kusanto su, kai kace su wani gida ne daga Dailama ko Kazar.

Sai sayyada Zainab ta ce: kada abin da kake gani ya gigita ka ya saka raki wallahi wannan alkawali ne daga Allah da manzon Allah (s.a.w) zuwa ga kakanka da baffanka hakika Allah ya riki alkawalin wasu mutane daga wannan al’umma wadanda fir’aunoni kan kasar wannan zamani basu sansu ba, sannan su sanananu ne a wajen mutanen sammai lallai su ne zasu tattaro gabban wadannan jikkuna da gangunan jiki da suke jike cikin jini suke a warwatse su binne su sanya wata alama a kabarin babanka shugaban shahidai a wannan gari na daffi da kabarinsa bi dusashe ba ya zama ba wata alama da za tai nuni zuwa gare shi tsawon darare da kwanaki lallai jagororin kafirci da mabiya bata suna bakin iyawarsu da kokarinsu wajen busashe kabarinsa da shafe shi amma babu abin da hakan ke kara masa face kara bayyana da kara daukakar lamarinsa

Ka sani cewa lallai zurfafar musibar karbala da kuma zurfafar sirrikanta da ke bayan hakan daga ilimummuka na sanain Allah wanda babu mai iya riskarsu hakikanin riska face Ahlul-baiti (a.s) misalinsu ke cewa: (babu wata rana misali ranarka ya baban Abdullah) amma muka fuskanta daga wannan waki’a mai girma da musiba mafi girma to bai wuce gwargwadon kwarfar tafin hannu ba daga tafkunan Husainiyya dake cike da kumfa mai karo da juna mai zurfin da nisan geffa mai nitsa matuka da aka gaza riskar zurfinta

Kamar yadda ya gabata lallai Imam Rida (a.s) Imami na takwas daga hujjojin Allah yana cewa: (lallai tunawa da ranar Husaini na sanyawa idaniyarmu ciwo).

misalin mafi girman waliyyin Allah ma’abocin zamani (af) yana cewa: (zan yi maka kukan jini mayin hawaye).

menene ya farune ranar Ashura cikin kasar karbala da har ya kawo misalin irin wannan radadi da gigita da shiga musiba daga Imamanmu (a.s) tsarkaka?!

Za mu iya fuskanta daga wadannan hadisai guda biyu masu daraja ma’ana hadisin Imam Rida da na Imam Hujja (a.s) cewa kwarmin idaniyarsu ta zubar da hawayen jini sakamakon musibar da ta sami baban Abdullah (a.s) da kakansu shugaban shahidai bawai kadai cikin kwanakin watannin Muharram da Safar ba kadai bari dai tsawon kwanakin cikar shekara baki daya ba tare da kayyadewa ba ko kebantarwa, ba komai ya sanya hakan ba face bakin ciki mai girma kan waki’ar Karbala

Da ya afku ranar Ashura sai idaniyar ta bushe sakamakon yawan kuka da dawwamarsa safe da yamma kan musibar da ta sami kakansu baban Abdullah Husaini (a.s)

Lallai muna da abin kwaikwayo nagari kakkyawa daga garesu, ya zama wajibi kan mu cikin kowanne zamani da lokaci mu halarto da musibar da ta afku a karbala da tunawa da ita, kai hatta idan mun samu damar iya tsayar da bukukuwan jaje da ta’aziyya ko da kuwa da mustawar iya tara makota da abokaine da mutanen unguwa daga kowanne gida guda daga gidajen muminai tsawon shekara cikin kowacce rana daya bayan dayansu safe da yamma, lallai shi tunawa da Ahlul baiti (a.s) na da lada mai girman gaske da albarka ga dangi da mutanen gida da dukkanin wanda ya halarci ta’aziyya, cikin hakan akwai tarbiyantar da yara kan soyayyar Husaini (a.s) da kaunarsa da narkewa cikin tushensa da misalsalansa madaukaka wadda ya sadaukar da ransa dominsu domin ya zamanto abin koyi da misali da fitila shiriya ga wanda yake son bin hanyarsa hanyar `yanci da aikata muslunci na Asali da dabbaka shi, kamar yadda shi dama ya kasance jirgin tsira ga wanda ya haushi don ya kai ga bakin gabarsa (a.s) da bakin tafkin nutsuwa da zikirin Allah matsarkaki.

ya dace ga dukkanin masoyi shi ne ya zama wajibi ya karu cikin sanin wannan tafarki mai yalwa da fadada ya kuma tsinkayi sasanni sabbi ya jibanci sabuntawa da cigabantarwa tare da kiyaye Asali da ilimummuka masu kima, lamarin Ashura da musibar Husaini shugaban shahidai (a.s) itace mafi girman musiba da tarihin dan adam ya shaida, saboda wannan nema magabata nagargaru daga malamanmu masu girma da maraji’ai masu girma suke tanadi domin raya da girmama alamun Husainiyyya bayan bikini din Gadir mafi haske, shi’a sun kasance cikin zaman makoki da bakin ciki sukan rataye bakin kyalle jikin bangunan Husainiyya da maukibobi da tarukan majalisai, ana kafa minbarori a raya zaman makoki da ta’aziyya cikin sasannin duniya, Allah ya so tutocin daffin Husaini su wanzu suna madaukaka a dage suna filfilawa a sama, lallai amabaton Husaini(a.s) madawwami ne mai dawwama tare da dukkanin kokari da yunkurin makiya cikin busasheshi da gogeshi da shafin samuwa, lallai Allah matsarkaki yana sakayya da kuma azaba cikin gidan duniya da lahira ga dukkanin wanda ya yi gaba da kiyayya da shi yayi kiyayya da gaba da ibadunsa da bukukuwansa, shaida nawa muke da su cikin tarihi kan haka, musammam ma cikin wannan zamanin da muke ciki, lallai Allah yana gaggauta azabtar da makiyan Imam Husaini(a.s) kai hatta hakan ya kusa ya zama ana kidaya shi daga Abubuwan da Imam Husaini ya kebanta da su ya dayantu da su.

Haka iradar Allah da mashi’arsa ta so ta kuma hukunta ya yi mu’amala da lamarin Husaini (a.s) a haka yana mai banbantawa daga waninsa, ya kasance al’umma bayan al’umma suna tunawa da shi fiye da yadda ake tunawa da waninsa, tare da cewa makiya da munafukai sunyi bakin kokarinsu cikin dusashe ambatonsa da goge shi da bushe haskensa. Sai dai cewa Allah yaki yarda face sai ya cika haskensa, lallai an rubuta a daman Al'arshi cewa Husaini shi ne fitilar shiriya jirgin tsira, lallai babu shakka ko kokwanto kan cewa lamarin Al'arshi da sammai na sama da lamarin kasa da cikinta da wanda ke cikinta. Idan ya zamanto Imam Husaini (as) da dukkanin zahirinsa hakika Allah ya togaceshi to babu abin da yake kan mu face muyi ta’ammuli da lamarinsa ta yadda aka bukace mu da muyi da kuma fifitawa kamar yadda halin hakan yake wurin `yan shi’a da masoya masu daraja, lallai ana sanin `dan shi’a Imamiyya da imaninsa da Gadir da Ashura, lallai tsawon zamani da cikin dukkanin kasashe da garuruwa an san shi’anci da raya ranar Wilaya (Ranar Gadir) da kuma ranar bara’a daga makiya ranar Ashura.

Lallai hukumar Banu Umayya ta yi ganganci tun ranar farko cikin boye hasken Imam Husaini(a.s) idan muka duba ingantattun littafan sunna za su shaida ma wannan lamari a bayyane saboda karancin hadisai kan Imam Husaini (a.s) da falalolinsa, misali cikin sahihul buhari bai nakalci riwaya ba kan Imam Husaini (a.s) face riwaya guda daya rak tare da ke cikinta daga matsaloli kamar yadda ma’aboda ilimi da sani suka fadaka da hakan, sai dai cewa tare da hakan akwai hadisai cikin littafan jamhur dake bayyana girman shugaban shahidai (a.s) da shahadarsa da lamarinsa.

cikin musnad Ahmad juz 1 sh 85, musnad Abu ya’ala juz 1 sh 298 h 33. Mu’ujamu Kabeer na dabarani juz 3 sh 105 h 2811 da isnadinsa daga Najani Hadarami cewa ya yi tafiya tare da Imam Husaini (a.s) ya kasance shi ke rike da butar alwalarsa yayin da ya taka sawun garin Nainawa (karbala) hanya zuwa Siffaini sai ya daga murya ya ce: hakuri ya baban Abdullah

Sai na ce: me ya faru ya baban Abdullah?

Sai ya ce: wata rana na shiga wajen annabi (s.a.w) idanunsa suna kwarar da hawaye sai na ce ya Annabin Allah mene ne ya samu idanunka take kwararar da hawaye? shin wani mutum ya bakanta maka? Sai ya ce: Jibrilu ne ya tashi daga wajena da zu ya kuma bani labari cewa za a kashe Husaini a gefen koramar Furatu, sai ya ce mini shin kana so in kamsar da kai kamshim kasar da za a kashe Husaini cikinta?

Sai na ce: na’am

Sai ya mika hannunsa ya damko wata kasa ya bani sai na kasa mallakar idaniyata har sai da ya kai ta zubar da hawaye

Irin wannan ta faru da Sarkin muminai Ali (a.s) a kan hanyarsa zuwa garin Siffaini gabanin mai afkuwar ta afku a karbala da shekaru ashirin sai baban Husaini ya yi zaman makoki kansa tun gabanin shahadarsa kamar yadda Annabawa sukai tun daga Adamu har zuwa cika makin Annnabwa (s.a.w).

Umar Alhassan Salihu

Faroukumar66@gmail.com

+989335382587


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: