bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:15:30
Shi kuwa tsuntsun nan mai gudun neman mafaka, shine mutumin da yake baka shawara mai kyau. Dan haka yana da kyau ka KARBI kyakkyawar shawarar mutumin da yake baka shawara.
Lambar Labari: 146

DAN HALAL SHINE RIBAR AURE

An taba yin wani mutun mai tarin arziqi da kuma hikima, a zamanin da can (wato tun lokacin Annabawan farko) yana da wani Da nagari (kamar shi) da ya Haifa daga wata matar shi Mumina (mai tsare kanta).

A yayin da ajalin shi ya matso kusa, sai ya kira 'ya'yan shi ya gaya musu: inna mutu dukkan dukiya ta, ta mutun daya ce daga cikin ku.

Bayan mutuwar shi, sai babban Dan yace, ai dukiyar nan tashi ce, tunda shine zababben mahaifinsu. Shima Dan na tsakiya yace shine Wanda mahaifinsu yake nufi, Dan autansu ma yace ai lallai shine mafi soyuwa a wajen babansu, kuma akan shi ne aka yi wasiyya.

Dan haka sai duk suka ruguntsuma zuwa gaban Alqali domin yanke hukumci.

Koda alqali yaji batun su, sai yace abun yafi qarfin saninshi, saidai suje ga wasu 'Yan uwa su uku 'ya'yan wani bawan Allah -yayi musu kwatancen inda suke- yaran nan suka tashi suka tafi can, suka fara zuwa gurin daya daga cikin su, wadda suka same shi dattijo ne ya manyanta (ya Tsufa), suka zayyana mashi abin da yake tafe dasu. Da yaji sai yace dasu, su tafi wajen yayanshi wadda da suka je sai suka same shi matashi wato a zahiri ya fi kanenshi yarinta, suka gaya mashi abin dake tafe dasu, shima yace dasu su tafi wajen Babban yayansu, wadda da suka je Shi kuma suka same shi matashi sharaf.

Cikin mamaki da farko sai suka buqaci da yayi musu bayanin yadda akayi suka ga haka - wato ya akayi gashi mafi shekaru amma yafi zama matashi, na tsakiyar su kuma ya Dan nuna manyanta, Sannan kuma qaraminsu sai ya bayyana tsoho haka-?

Sai yayi musu bayani kamar haka:

Wanda kuka fara zuwa gurinshi shine qaramin mu, dalilin tsufanshi shine, Matarshi ce bata da kirki ko daya, kullum tana muzguna mashi, shi kuma yana jurewa da haquri, saboda kada ya rika tanka mata, ayi ta yin dauki ba dadi (fitina) a gidan.

Shi kuma na biyun wato na tsakiyar mu, shi kuma Matarshi ta kasance baina-baina (tsaka-tsaki) wato wata rana ta kyautata mashi, wata rana kuma quntatawa. Shiyasa kuka ganshi, ya dan manyanta idan aka kwatanta shi da ni wato yayanshi.

Ni kuma da kuka ganni haka duk da yake nine babbansu a shekaru amma yaro a jiki, dalilin haka kuwa shine, ni Matata, kodayaushe tana matuqar kyautata min qwarai da gaske wadda har zuwa yanzu bata taba bata min rai ba, to shi yasa kuka ganni matashi sharaf haka.

To shikenan, bayan sun gama sauraron shi, sai kuma suka zayyana mashi nasu batun.

Da yaji abin da yake tafe dasu, sai yace musu, to kafin ayi muku hukumcin wannan batu naku sai kunje kun tone gawar mahaifinku, kun fito da qasusuwanshi kun qone su, sannan sai ku dawo kuji hukumcin da zanyi muku.

To sai yara biyun da suka fito daga dayar matar (Mara kamewa), suka qudiri aniyar tone kabarin, amma sai Dan autan nasu -Dan ita muminar matar- ya zare Takobi yace: Zan iya barin Gaadona, amma ba zan taba bari a tone kabarin mahaifina ba.

A qarshe sai su duka ukun suka koma gurin alqalin, suka gaya mashi abin da ya faru.

Sai yace to komai yazo qarshe, duk ku tattaro dukiyar baban naku, ku kawo nan, suka kawo, sai ya dauka duka ya baiwa Dan autan, yace da sauran biyun: Da kun kasance halastattun 'ya'yan shi, da kuma ba zaku taba bari a tone kabarin shi har a qone qasusuwanshi ba. Kamar yadda qaramin nan naku yaqi amincewa.

Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya dawwamar damu akan yi maShi biyayya. Ameen.

***

SIRRI BIYAR A RAYUWA

A cikin Annabawan da suka gabata, Allah Yayiwa wani wahayi cewa ka HADIYE duk abin da ka fara haduwa dashi kashegari da safe, ka BOYE na biyu, ka KARBI na uku, kada ka BAIWA NA HUDU KUNYA Sannan ka GUJI na biyar.

Shikenan sai Annabin nan kashegari ya ci gaba da tafiyarshi. Farkon abin da ya fara haduwa dashi shine, wani baqin tsauni babba a gabanshi. Ya raya a zuciyarshi cewa, Ya Ubangiji na, ka umarce ni da in hadiye shi, amma ta yaya? Sai kuma ya tuna cewa, LALLAI, Ubangijina, ba Zai umarce ni da abin da ba zan iya ba? Kawai sai ya tinkari wannan Tsauni, a yayin da ya yake kusantar shi, sai yaga kawai tsaunin nan yana qanqancewa yana zama qarami, har ya zama kamar Laumar abinci, shikenan sai ya dauka ya cinye shi. Kuma ya ji shi da dandani mai dadin da bai taba ji ba.

Sai ya ci gaba da tafiyarshi, sai kuma ya hadu da wani faranti (mazubin abinci) na Zinare a gefen hanya, sai yace a ranshi Ubangijina Ya umarceni da na bisne shi. Dan haka sai ya haqa rami, ya turbudeshi, bayan ya dan ci gaba da tafiya, sai ya juyo, sai yaga farantin zinaren nan ya sake bayyana. Sai yace a ranshi, shi dai ya cika umarnin Ubangijinshi, dan haka yanzu ba shine ke da alhakin sake bayyanarshi ba.

Sai ya ci gaba abinshi, yana cikin tafiya, sai ga wani tsuntsu a guje Shaho ya biyo shi zai cinye shi. Tsuntsun nan ya nemi mafaka gurin Annabin nan, sai ya tuna da umarnin Ubangijinshi cewa ya KARBE shi, Dan haka sai ya bude hannun rigarshi, sai tsuntsun ya shige ciki.

Sai kuma Shahon ya qaraso, yace: ya za ka kama min abin farautana, da na dade ina binshi.

Sai Annabin yayi tunanin KADA YA GWASALE Shahon nan. Dan haka sai ya yanko naman Cinyarshi, ya bai wa Shahon, sai ya ci gaba da tafiyarshi, sai ya iso wani guri da ya iske wata Gawa ta rube har ta fara tsutsotsi, tana yin wari. Sai ya tuna da umarnin Ubangijinshi cewa YA GUJE ta, sai ya kauce mata, ya juyo ya dawo gida. Da dare sai yayi mafarki, a cikin mafarkin wani ya tambaye shi, ko ya san ma'anar duk abubuwan da Ubangijinshi Ya umarce shi dasu?

Yace, a'a! Sai ya gaya mashi kamar haka:

Shi wannan Tsaunin a matsayin FUSHI yake, saboda a duk lokacin da mutun ya fusata, to yana manta kanshi ne, amma idan ya dubi kanshi ya shaida kanshi, to fushin ya kan sauka, a qarshe ya zama kamar 'yar Laumar can mai dadin ci (kuma ka dandana dadin ta a baya).

Shi kuwa waccan Farantin zinare, KYAKKYAWAN AIKI ne, a yayin da Bawa ya boye kyakkyawan aikin shi daga idon mutane, to Shi kuma Allah Subhanahu wa Ta'ala sai Ya bayyana shi gare su, saboda mutane su yi sha'awar abin da yake boyewa garesu, wadda aka tanada musu Ranar gobe qiyama.

Shi kuwa tsuntsun nan mai gudun neman mafaka, shine mutumin da yake baka shawara mai kyau. Dan haka yana da kyau ka KARBI kyakkyawar shawarar mutumin da yake baka shawara.

Shi kuwa Shaho, shine misalin mutumin da zai zo ya tambaye ka ko ya roke ka wani abu. Dan haka kada ka hanawa irin wadannan mabuqatan.

Ita kuwa Rubabbiyar Gawar nan mai warin tsiya, Gulma ce. Dan haka kodayaushe ka guji yin mummunar magana akan Wanda bayanan (a bayan idon mutum).

Ubangiji Allah Yasa mu iya kiyayewa, domin mu rabauta, ranar gobe qiyama. Ameen!!!!!

***

TASIRIN YIN SULHU TSAKANIN MA'ABOTA SABANI

A zamanin da can an taba yin wani mutumi bawan Allah da ya dauki saqar da iyalin shi tayi zuwa kasuwa domin ya siyar ya siyo musu abin da zasu cetar da kawukansu daga yunwa.

Ya siyar da saqar nan Dirhami daya, ya tawo gida abinshi da nufin yaje ya sayi abin da zasu yi Gurasa suci.

To a kan hanyarshi sai ya iske wasu mutum biyu suna yin fada akan Dirhami daya, har sun karcewa juna fuska, amma basu daina fadan ba.

Sai bawan Allahn nan ya matsa kusa dasu, yace, gashi ku karbi wannan dirhami, dan haka sai ku kawo qarshen fadan haka, ya sulhuntasu, ya tafi gida hannu Rabbana, da yaje ya bai wa iyalin tashi labarin abin da ya faru, itama tayi farin ciki da abin da mijin nata yayi.

Sai matar ta tashi ta dan dudduba a gidan ko zata samo wani abu mai qima da za a iya siyarwa dan su samu suci abinci, amma bata samu ba sai kayan sanyawarta, suma sun dan tsufa, amma ta dauka ta ba maigidan nata, tace yaje ko za a dace, in suka sami shiga sai ya samo musu dan abin da za a yi abincin.

Maigida ya karba ya koma kasuwa, yaje yayi-yayi amma babu labari. Sai can ya ga wani matum dauke da kifi ya kusa lalacewa yana zagayawa shima ko zai sami mai siye, sai bawan Allahn nan yace da mai kifin yazo suyi musaya (kakara) mai kifi ya yarda kuwa, saboda yana ganin har kayannan zasu fi saurin shiga akan kifin.

Sai bawan Allah ya karbi kifi ya nufi gida, da zuwa gida sai iyali ta kama aikin gyara kifi, bude cikin kifi ke da wuya, sai taga Abu mai qima wato Lu’u-lu’u (pearl) a ciki, ta kira maigida ta bashi dan yaje kasuwa ya siyar, ya karba yaje ya siyar da lu'u-lu'un nan da qimar gaske, ya dawo gida abinshi, a yayin da ya iso qofar gida zai shiga, sai ga wani Faqiri ya tareshi yace: Bani daga abin da Allah Ya azurta ka!!!!

Sai bawan Allahn nan ya bude ma faqirin duka kudin nan ya miqa masa, yace: Gashi ka debi duk yadda zai yi maka!!!

Ya Allah!!!!!

Sai faqirin nan ya dan dibi kadan, ya juya dan taku kadan ya tafi, sai ya juyo ya cewa bawan Allahn nan: Ni ba Faqiri bane, Ma'aiki ne daga Allah nazo in sanar maka cewa, wannan daga cikin ladan kyakkyawan aikin ka ne, na Sulhu da kayi tsakanin mutun biyun nan, shine ka fara girba tun a wannan duniyar!!!!

Ya Allah!!!!! Ka sulhunta tsakanin dukan musulmi baki daya, dama sauran al'ummu. Ameen.

***

SHAIDAN DA WANI MAI IBADA

A al'ummar bani Isra’ila anyi wani mutun mai yawan ibada, aka kai mashi labarin cewa, a guri kaza akwai wata bishiya da mutanen yankin suke bauta mata. Jin haka sai ya fusata, sai ya dauki gatarinshi ya saba a kafada domin yaje ya sare wannan bishiya.

Sai Iblis ya fito cikin sifar tsoho ya tare shi a kan hanyarshi, yace, Ina zaka je?

Mutumin nan yace: zan je ne in sare bishiyar can da ake bautawa, domin mutanen su tsaya ga bautawa Allah kadai.

Iblis yace: dan dakata in fada maka wata magana tukun.

Mutumin yace: to fadi da Allah da sauri (mutumin yana rawar jiki)

Iblis yace: in da akwai buqatar sare waccan bishiya, da Allah Zai aiko Annabawa ne, domin su sare ta.

Sai mutumin nan yace ai lallai sai naje na sare bishiyar can.

Iblis yace: ba zan bari ba, ya cakumi wuyan rigar mutumin (wato yaci kwalarshi), sai mutumin ya daga Iblis sama ya buga a qasa. Sai iblis yace to dan dakata ina da wata maganar da zan gaya maka.

Da ya dakata, sai iblis yace mashi: kaga kai mutum ne mabuqaci, da zaka sami dukiya ka rika taimakawa bayin Allah masu Bauta, yafi ace kaje ka sare waccan bishiyar. Ka kyale sare ta, kullum nayi alqawarin sa maka Dinar biyu a qarqashin matashinka.

Sai mutumin nan mai ibada yace: kaga kuma hakane, sai in rika bayar da sadakar dinar daya, ni kuma ina amfani da dinar daya, yafi in sare wannan bishiya. Tunda ni dai ba Annabi bane balle in dage akan sai na sare wannan bishiya, sai ya saki Iblis.

Yayi kwana biyu yana ganin Dinar biyu a qarqashin matashinshi, ya rika dauka yana kashewa, amma a kwana na uku sai bai ga komai ba, sai ya fusata, dan haka sai ya dauko Gatarinshi domin yaje ya sare bishiyar nan.

Sai iblis ya tare shi a hanya, yace malam ina zuwa?

Mutumin yace zan je in sare bishiyar nan ne. Sai Iblis yace mashi, ai ba zaka taba iyawa ba. Sai ya cakumi mutumin nan ya buga da qasa, yace mashi ka koma, in ba haka ba zan cire maka kai.

Sai mutumin yace: To, sake ni in koma, amma me yasa a waccan lokacin nafi qarfi sosai?

Iblis yace mashi: A waccan lokacin ka fito ne da zuciya daya wato da Ikhlasi (domin Allah) dan sare bishiyar, shi yasa Allah Ya Sallada ka akai na. Amma wannan lokacin kayi fushi domin kanka ne da kuma Dinare ba domin Allah ba, shi yasa na sami galaba akan ka.

Allah Yasa kodayaushe mu fifita Son Allah akan son ranmu, kuma komai zamu yi, muyi dan Allah, hakazalika mu bari dan Allah.

Allah kuma Ya dada yi mana tsari daga sharri da yaudarar shaidan la'ananne.

*****

To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na hudu a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na biyar’, da wannan ni Hassan Adamu nake cewa ku huta lafiya. Limawa86@yahoo.com.

Hassan Adamu

Littattafan da aka ciro wadannan Qissoshi sune:

1- Yek sad Maudhu’ 500 dastan (Sayyid Ali Akbar Sadaqat)

2- Hayat Al-Qulub (Allama Majlisi)

3- 100 moral stories (Akramullah Syed)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: