bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:42:19
Muslim ya ruwaito, ya ce: Yahya dan Yahya ya ba mu labari, ya ce: Na karana wa Malik daga Ibnu Shihab, daga Urwa ya karbo daga Nana Aisha, tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya yi sallar nafila a Masallaci a cikin dare
Lambar Labari: 153
SUNNAR MANZON ALLAH (s.a.w) A RUWAYAR AHLULBAIT (a.s):
Ruwayoyin Ahlulbait (a.s) sun sha bamban da wasu ruwayoyin da masu Sunan suka ruwaito, don haka ruwayoyinsu (a.s) sun bayyana cewa Manzon Allah (s.a.w) lokacin da ya fita da daddare zuwa Masallaci don ya yi salla shi kadai sai mutane suka bi shi a matsayin liman ya hana su, lokacin da ya ga dagewarsu a kan binsa, sai ya fasa sallar a Masallaci, ya tafi gida ya yi, kuma ga masu ruwayoyi kan haka:
Zurara da Muhammad bn Muhsin da Fudail sun tambayi Bakir da Sadik (a.s) kan sallar nafilar dare a watan Ramadan a cikin jam’i, sai suka ce: Tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya kasance in ya yi sallar Isha’i sai ya tafi gidansa, sannan ya fito a karshen dare ya shiga Masallaci, ya tsaya, ya yi salla, sai ya fito a farkon daren watan Ramadan don yin salla kamar yadda ya saba, sai mutane suka yi sahu a bayansa, nan take ya tafi gidansa ya barsu, sai da suka yi haka sau uku, a rana ta hudu ya tashi ya tsaya kan mimbarinsa, ya godewa Allah ya yabi Allah, sannan ya ce: "Ya ku mutane tabbas yin sallar nafila da daddare a watan Ramadan a cikin jam’i Bidi’a ne, sallar walaha ma bidi’a ce, kar ku yi jam’i da daddare a watan Ramadan lokacin sallar dare, kar ku yi sallar walaha, tabbas yin ta sabo ne, tabbas ko wace bidi’a bata ce, duk bata hanyar shiga wuta ne. Sannan ya sauka yana cewa: "Sunna kadan ta fi bidi’a mai yawa alheri”.( ) 
Ubaidu dan Zurara ya ruwaito daga Imam sadik (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) yana kara raka’o’in sallarsa a watan Ramadan, idan ya yi sallar Isha sai ya yi sallar nafila a bayanta sai mutane su bi shi salla sai ya shige gida ya bar su, sannan ya fito sai mutane su zo su bi salla sai ya bar su, sannan ya fito, sai mutane su zo su bi Sallah sai ya rabu da su ya tafi gida.( ) 
Akwai tsammanin Annabi (s.a.w) ya yi haka sau biyu, lokacin farko a karshen dare - kamar yadda ya zo a ruwayar farko - karo na biyu kuma bayan sallar Isha kamar yadda ya zo a ruwaya ta biyu. 

MATSAYIN BUKHARI DA MUSLIM A KAN TARAWIHI:
Abin da aka ruwaito ta fuskar Ahlus Sunnah ya sabawa haka, ga nassin da Bukhari da Muslim suka kawo:
Bukhari ya ruwaito ya ce: Yahaya dan Bukhair ya ba mu labari Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga Ibnu Shihabi Urwa ya ba ni labari, Aisha (r.a) ta ba shi labarin cewa; Manzon Allah (s.a.w) ya fita cikin dare ya yi salla a Masallaci, sai mutane suka bi shi sai gari ya waye mtuane suka ba da labari, sai mutane da yawa suka taru, sai ya fara sallah suka bi shi, da gari ya waye sai mutane suka dinga zancen a dare na uku, mutanen masallaci suka kara yawa, sai Manzon Allah (s.a.w) ya fito, mutane suka sake bin sa, a dare na hudu sai masallaci ya yi musu kadan, har ya fito yin Sallar Asuba, lokacin da ya gama sallar Alfijir sai ya fiskanto mutane ya yi shahada sannan ya ce: "Bayan haka, na san abin da kuka yi, amma dai ni na ji tsoron kar a farlanta muku ku kasa yi”. Kuma Har Manzon Allah (s.a.w) ya rasu a haka al’amarin yake.( ) 
Ya sake ruwaitowa a babin Tahajjudi: Tabbas Manzon Allah (s.a.w) wata rana ya yi salla a masallaci sai mutane suka bi shi, sannan washe gari ma ya fita mutane suka bi shi da yawa a bayansa, sannan a dare na uku ko na hudu suka taru, sai Manzon Allah (s.a.w) ya ki fitowa, da gari ya waye sai ya ce: "Na ga abin da kuka yi, ba abin da ya hana ni fitowa sai don na ji tsoron kar a farlanta muku sallar ne, hakan kuwa a watan Ramadan ne”.( ) 
Muslim ya ruwaito, ya ce: Yahya dan Yahya ya ba mu labari, ya ce: Na karana wa Malik daga Ibnu Shihab, daga Urwa ya karbo daga Nana Aisha, tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya yi sallar nafila a Masallaci a cikin dare, sai mutane suka bi shi, sannan washe gari ma ya yi sallar nafila mutane suka zo da yawa, a dare na uku ko na hudu suka sake taruwa ( ) sai ya ki fitowa, da gari ya waye, sai ya ce: "Tabbas na ga abin da kuka yi, ba abin da ya hana ni fitowa sai don tsoron kar a farlanta muku sallar”, ya ce: Wannan fa a watan Ramadan ne. 
Harmalata bn Yahya ya ba ni labari, Abdullahi bin Wahab ya bani labari ya ce: Yunus bin Yazid ya ba  ni labari daga Ibnu Shihab ya ce: Urwa bn Zubair ya ba ni labari cewa Aisha ta ba shi labarin cewa; Manzon Allah (s.a.w) ya fita cikin dare ya yi salla a masallaci, sai mutane suka bi shi, sai mutane suka wayi gari suna labari. Sai mutane da yawa suka taru, nan da nan Manzon Alah (s.a.w) ya fito a dare na biyu, sai suka bi shi sallah, da safe suka dinga zancen, sai mutanen Masallaci suka kara yawa, a dare na uku, nan da nan Annabi ya fito ya yi salla, suka bi shi a dare na hudu sai Masallaci ya yi kadan, Annabi (s.a.w) ya ki fitowa, sai da asuba bayan gama sallar Asuba, sai Annabi (s.a.w) ya fiskanto mutane ya yi kalmar shahada ya ce: "Bayan haka, na san abin da kuka yi jiya da daddare, amman fa ina tsoron kada a wajabta muku sallar dare”.( ) 
Sabanin abin da maruwaitan mu suka ruwaito daga Amirul Muminina Ali (a.s) da abin da Bukhari da Muslim suka ruwaito a fili yake. A maganar farko Annabi (s.a.w) ya hana yin jam’in ta, ya kuma kira ta da sunan bidi’a, a magana ta biyu Annabi (s.a.w) ya ki yin ta a cikin jam’i ne don kar a farlanta musu, tare da cewa hakan ya dace da addini da Shari’a to wace magana ce ta fi dacewa a bi?

MUNAKASHA KAN BUKHARI DA MUSLIM:
Tabbas a Hadisan Bukhari da Muslim akwai muhskiloli da yawa wanda suka dace a yi tsokaci a kansu:
Mushkilar farko: Ma’anar maganarsa da ya ce: "Na ji tsoron kar a farlanta muku, ku kasa yin ta”.
Shin ma’anar hakan, Shari’a tana la’akari da fuskantowar mutane da ba da bayansu, idan mutane sun himmatu a zahiri sai a farlanta musu, in ba haka ba, ba za a wajabta musu ba? Tare da cewa abin da ake la’akari da shi wajen farlantawa shi ne samuwar maslaha a cikin hukunci, ko akwai himmatuwar zahiri ko babu? Tabbas hukuncin Shari’ar Allah (SWT) baya bin son mutane ko kawar da kansu, ai Shari’ar Allah maslaha da rashin maslaha wanda Allah ne ya fi kowa sanin su, mutane sun fuskanto abin ne ko sun bawa abin baya. 
Mushkila ta biyu: Idan mun dauke cewa Sahabbai sun bayyana himmatuwarsu da sallar Asham da yin ta a cikin jam’i, shin hakan zai zama dalilin wajabta ta? Tabbas Masallacin Ananbi (s.a.w) a wannan lokacin waje ne iyakantacce ba zai ishi mutane da yawa ba, sai mutum dubu shida, ko kasa da haka, tabbas ya zo a cikin Alfikhu alal Mazahibil Khamsa cewa; "Masallacin Annabi (s.a.w) mita 35 cikin mita 30 sai Manzon Allah (s.a.w) ya kara shi ya zama mita 57 cikin mita 50”.( ) 
Shin zai yiwu himmantuwarsu ta bayyana himmantuwar baki dayan mutane a cikin baki dayan lokuta har ya zuwa ranar alkiyama?
Mushkila ta uku: Shi ne samuwar sabani a cikin adadin dararen da Annabi (s.a.w) ya yi jam’in nafilfilin Ramadanan. A bisa abin da Bukhari ya nakalto a kitabus Saumi tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya yi sallar tarawihi tare da mutane a darare ya yi sallar a dare biyu, Muslim ma ya nakalto haka kamar yadda Bukhari ya kawo a ruwaya ta biyu, abin da waninsu ya fada cewa Manzon Allah (s.a.w) ya yi sallar Tarawihi a wasu mabambantan darare (daren uku, biyar, bakwai da na ashirin, wannan yana bayyana rashin himmantuwar nakalto aikin Manzon Allah (s.a.w) kamar yadda yake, yaushe za mu nutsu da sauran abin da ya zo a ciki wai Annabi ya ga kyan abin da suka yi?
Mushkila ta hudu: Tabbataccen abin da Annabi (s.a.w) ya yi a dare na biyu dai ya yi sallar, ko dare hudu a karshen dare kuma ba ta wuce raka’a takwas ba, yin koyi da Annabi yana hukunta koyi da shi a cikin abin da ya tabbata, ba a cikin abin da bai tabbata ba, kai a hakan fa bai tabbata ba, kamar yadda kasdalani ya fada, ya kuma siffanta abin da ya karu a kan haka cewa bidi’a ne. kuma ga abin da yake cewa:
1- Tabbas Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta musu yin ta a jam’i ba.
2- Lokacin Abubakar Siddik ba a yin ta.
3- Ba a farkon dare ba.
4- Ba a ko wanne dare ba.
5- Ba kuma wannan adadin.( ) 
Sai ya fake a wajen t abbatar da halaccinta da cewa ijtihadin Halifa ne.
Aini yake cewa: Tabbas Manzon Allah bai sunnanta musu yinta ba, a lokacin Abubakar ma ba a yinta ba. Ya kafa hujja a kan halaccin ta da ijtihadin Umar da istinbadinsa na cewa Sharia ta tabbatarwa mutane su yi Salla a bayansa dare biyu.( ) 
Mushkila ta biyar: Lallai idan muka yi riko da ruwayar dayan nauyaya (mutanen gidan Annabi (s.a.w) yin jam’in nafilfilu bidi’a ne mdlakan, idan muka yi riko da ruwayar Bukhari da Muslim, gwargwadon da ya tabbata dai shi ne abin da ya zo a cikin maganar Kasdalani, kkari a kan haka fa bidi’a ce wacce aka raba, abin da ake nufi da ita shi ne abin da aiki a zatinsa halatacce ne, amman yadda aka yi shi ne ba halastacce ba.
Ba abin da suke kafa hujja da shi a kan halaccinta sai aikin da Halifa ya yi na hada su bin limami daya, wannan ne abin da za mu yi sharhi a kansa a bahasin gaba.

HADAN MUTANE A KAN LIMAMI DAYA A ZAMANIN UMAR
Bukhari ya ruwaito cewa; Manzon Allah (s.a.w) ya rasu mutane suna kan haka (wato basa yin jam’in tarawihi), sannan al’amari ya ci gaba a haka lokacin halifancin Abubakar da farkon mulkin Umar.( ) 
Ya ruwaito daga Abdurrahman bn Abdulkari ya ce: Na fito tare da Umar dan Khaddab a daren Ramadan zuwa Masallaci, sai ga mtuane a rarrabe kowa na yin sallarsa shi kadai, wani kuma yana yin salla wasu mtuane suna binsa.( ) 
Sai Umar ya ce: Ina ganin da zan sawa wadannan makaranci daya da ya fi. Sannan ya kuduri aniyar sa musu Ubayyu bn Ka’ab, sannan na taho tare da shi a cikin wani dare mutane suna bin sallar makarancinsu (limaminsu), sai Umar ya ce: Madalla da wannan bidi’ar, wacce kuke bacci kuke barinta ta bi wacce kuke yi. Yana nufin karshen dare, mutane sun kasance sun yin sallar a farkon dare.
Amman zahirin masu sharhin Sahihul Bukhari cewa suka yi yinta cikin jam’i ba halataccen abu banme, ga bayanin a dunkule a cikin abu biyu:
(1) Maganarsa: "Annabi (s.a.w) ya rasu mutane suna kan haka, sannan al’amarin ya ci ga da zama a haka a lokacin Halifancin Abubakar”. Tabbas masu sharhi sun fassara shi da cewa; wato barin jam’in sallar Tarawihi, Manzon Allah (s.a.w) bai hada mtuane kan yin jam’in tarawihi ba.( ) 
Badruddin Aini ya ce: Mutane suna kan haka (barin jam’in Tarawihi) sannan ya ce: Idan ka ce Ibnu Wahabin ya ruwaito daga Abu Huraira cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ito sai ga mtuane suna salla a masallaci cikin watan Ramadan, sai ya ce: "Meye haka?” sai aka ce: Mutane ne Ubayyu bn Ka’ab ya ke musu Sallah, sai ya ce: "Sun yi dai-dai kuma madalla da abin da suka yi”. Ibn Abdil Barri ne ya kawo shi.
Sannan da kowa ya sani tabbas Umar (RA) ne ya sa mtuane bin Ubayyu bn Ka’ab a Sallar Tarawihi.( ) 
Kasdalani ya ce: "Al’amarin haka yake (wato ba a yin jam’in tarawihi) kuma dai haka al’amarin ya ci gaba da halifancin Abubakar har zuwa karshen abin da ya fada”.( ) 
(2) Maganarsa da ya ce: Madalla da wannan bidi’ar, a zahirin maganarsa: "Madalla da wannan bidi’ar”. Tabbas tana cikin sunnonin Halifa, ba ta da alaka da shari’a, lallai taron malamai ne suka fadi haka.
Kasdalani ya ce: Umar ya ambace ta da bidi’a saboda Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta musu yin ta a jam’i ba, lokacin Abubakar Siddik ma ba a yin ta a jam’i, ba kuma a yi ta a farkon dare, kuma ba a kowanne dare ake yinta ba, ba kuma wannan adadin ake yi ba, har inda yake cewa: Tsayuwar Ramadan ba bidi’a ba ce, domin Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ku yi koyi da wadanda suke bayana Abubakar da Umar. Idan Sahabbai da Umar suka hadin a kan haka, to sunan bidi’a ya gushe”.
Aini yake cewa: "Ya kira ta da sunan bidi’a saboda Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta musu ita ba, babu ita a zamanin Abubakar, kuma Annabi (s.a.w) bai kwadaitar a kanta ba”.( ) 
Malamai da yawa sun hadu kan cewa Umar ne farkon wanda ya sunnanta jam’in sallar Tarawihi, bugu da kari kan abin da ya gabata na irin wannan ma’anar, za mu fadi wasu maganganun malamai:
1- Ibnu Sa’ad ya fada a tarjamar Umar yake cewa: "Shi ne farkon wanda ya sunnata tsayawa a cikin watan Ramadan mai suna Tarawihi, ya kuma sa mutane suka taru don yinta, ya rubuta wasika aka kai garuruwa, hakan kuwa ya faru ne a watan Ramadan 14H”.( ) 
2- Ibn Abdul Barri ya fada a tarjamar Umar: "Shi ne ya haskaka watan Azumi da Sallar Tarawihi a cikinsa”.( ) 
Wato dan Shihana ya fada a wajen da ya ambaci rasuar Umar a tarihin abubuwan da suka faru na 23H: "Shi ne wanda ya hana siyar da iyaye bayin da suka haihu... shi ne farkn wanda ya sawa mutane liman a sallar Tarawihi”.( ) 
In dai Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta jam’in tarawihi ba, Umar ne ya sunnanta jam’in Tarawihi ba, Umar ne y sunnata ta, shin wannan ce madogarar halaccinta ko bidi’antakarta? Tare da cewa ba wani mutum har Manzon Allah (s.a.w) mai isar da sakon Allah ne a cikin Shari’a da kawo sunna, shin abin da bai halatta ga Manzo ba zai halatta ga wanin Manzo (s.a.w)?
Tabbas Wahayi yana dauke da shari’a zuwa ga Annabi mai girma (s.a.w) wanda aka yi masa wahayi, da zarar ya rasu shi ke nan wahai ya kare, an toshe kofar kawo shari’a da sunnantawa, al’umma ba ta da wani abu sai dai ijtihadi a cikin Kur’ani da sunna, ba kawo shari’a da sunna ba, duk wanda ya ga cewa wanin Alah (SWT) yana da hakkin sunnatawa, to abin fa da yake nufi shi ne har yanzu wahayi bai kare ba.
Ibnul Asir ya fada a cikin Nihaya: Cikin irin wannan akwai maganar Umar: "Madalla da wannan bidi’ar (tarawihi) tun da tana cikin ayyukan alheri, ta shiga cikin bangaren yabo don haka ya kira ta da bidi’a, ya kuma yabe ta, sai dai Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta musu ita ba, ya yi sallar ne a wasu darare, sannan ya bar ta bai nace a kanta ba, bai kuma sa mutane yin ta jam’i ba. Ba a yin ta a lokacin halifancin Abubakar ma, Umar ne ya sawa mutane Liman yake musu jam’i, ya kira su su yi ta, saboda haka ne ma ya kira ta bidi’a kuima ita a hakikanin gaskiya sunna ce, saboda Hadisin Manzon Allah (s.a.w) da ya ce: "Na hore ku da sunnata da sunnar Halifofi masu shiryarwa a bayana” da wani Hadisi ma: "Ku yi koyi da wadannan biyun a bayansa Abubakar da Umar”.( )

ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: