bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:26:16
Duk yayin da mutum ya auri mace, dole ya ba ta sadaki sakamakon jin daxin da zai samu na jima’i da ita.
Lambar Labari: 156



2. DOKOKIN AURE

A. Sadaki (Mahr).
Duk yayin da mutum ya auri mace, dole ya ba ta sadaki sakamakon jin daxin da zai samu na jima’i da ita. Dole sadakin ya zama fayyacaccan adadi na kuxi ko wani abu a matsayin kuxi. Dole ya kasance na halal kuma mallakar mijin. Duk mazhabobin sun haxu a kan cewa ba dole ne a ambaci sadaki a yayin xaura auren ba. Idan aka ambata kuma sai ya zama sadakin bai cika sharaxin sadaki ba, to auren ya qullu amma sai an gyara sadakin.
Sadaki ya kasu biyu. 'Ambataccen sadaki', shi ne wanda namiji da mace suka amince da shi. 'Dagantaccen sadaki', shi ne wanda mace ta ke karva idan namiji da mace ba su daidaita kan su akai ba ko kuma idan wani dalili ya sa ambataccen sadaki ya zama vatacce. Dangantaccen sadaki, dukiya ce da ake ba mace dai-dai da abin da ake ba mace me irin matsayinta a shekaru, kyau, ilimi, da sauransu a wannan zamanin.
Mazhabobi huxu sun haxu a kan cwa da zarar an xaura aure, matar ta mallakar dukkan sadaki. Malikiyya sun ce rabin sadakin ne kawai mallakinta. A wannan lokacin.(Fiqhu, 4, 108). Da matar za ta buqaci sadakinta nan take, to dole mijin ya ba ta, amma da zai sake ta kafin ya yi jima’i da ita kuma har lokacin ba ta karvi sadakinta ba, to zai ba ta rabi kawai.
Mazhabobin gaba xayansu, sun tafi a kan cewa, yin jima’i ko rasuwar xayan ma’aurata ya wajabta biyan dukkan sadaki. Malikiyya sun qara da cewa idan mace ta zauna tare da mijinta a qalla tsawon shekara xaya, ba makawa sai an sami jima’i a tsakni, don haka dole ya biya ta dukkanin sadakin.(Ibid 109). Hanafi ya ce da zarar ya kevanta da matar kevantar da babu abin da zai iya hanasu jima’i, to hakan ya isar ya ba ta dukkanin sadakin.(Ibid 111).
Amma Hanbali ya tafi a kan kevatar miji ga matarsa, yin wasa me motsa sha’awa, da ganin tsaraicinta sun wadatar ga biyanta dukkan sadakinta.(Ibid 115).
Kafin ya tara da matar, ko ya sadu da ita, biyan gaba xayan sadaki ko wani bangare yana saraya ta dalilai masu zuwa: 1- Rabin sadaki yana saraya ta dalilin saki. 2- Idan mace ta bar addininta, ta sarayar da dukkan sadakinta. 3- Idan mijin ya bar addininsa, to babu makawa auren ya vaci, amma duk da haka dole ya ba ta rabin sadakinta. 4- Idan xaya daga cikin su - miji ko matar - ya vata auren saboda wata nakasa ta jiki ko cin amana, to dukkan sadakinta ya saraya, sai dai Shi’a sun tafi a kan cewa matar na da haqqin a ba ta rabin sadakinta idan ta vata aurensu saboda mijin ba namiji ba ne.(Sharhul Lum'a 11, 101, Riyadh, 11, 135). (ba shi da lafiyar jima'ai). 5- Idan miji da mata suka fahimci haramcin aurensu ta dalilin wata dangantaka, misali, sun sha nono xaya, idan matar ba ta sani ba, to za ta karvi rabin sadakinta, amma in har tana da laifi to dukkan sadakinta ya saraya.
Mazhabar Malikiyya, Hambalyiyya da Shi’a sun tafi a kan cewa: idan auren da aka kulla ya zama vatacce, amma kuma sun san juna (sun sadu), to matar na da sadakin da suka amince tsakaninta da mijin.(Fiqhu, 4, 120 – 21 Sharhul Lum'a 11, 101 Riyadh 11, 135). Shi kuwa shafi’i cewa ya yi tana da sadaki daidai da mace me matsayi irin nata.(Fiqhu, 4, 118). Amma Hanafi ya ce za ta karvi abin da yake mafi qanqanta daga sadakin (Ibid, 116). (guda biyu).
Dangane da kuskuren jima’i yayin da namiji da mace suka  tsammanin su miji da mata ne, - har suka sadu - to matar na da sadaki dai-dai da mace me irn matsayinta.
Mace na da damar qin amincewa da jima’i matuqar ba a ba ta sadakinta ba. Bisa haka, a wannan yanayin kuwa miji ba shi da damar dagewa da sunan cewa yana da iko kan yin jima’i da matar, sai dai idan an ambata varo-varo a yayin xaura auren cewa za a ba da sadakin a wani qayyadajjen lokaci mai zuwa. Amma idan mace ta amince da yin jima’i kafin ta karvi sadakinta, to daga rannan ba ta da ikon qin yarda da mijinta sai idan ta bayyana cewa ba shi da halin biyan sadakin, a nan fahimtar Shi’a ta sha ban-ban da ta ahlussunna, cewa da zarar an sami jima’i, matar ba ta da ikon qin yarda da mijinta saboda dalilin rashin halin mijin na biyan sadakin. (Sharhul Lum'a 5, 371 – 72 Riyadh, 11, 149). Hambali, Shafi’i, da Maliki sun ce: idan rashin halin biyan sadakin ya bayyana kafin jima’i, matar za ta iya vata auren, sai dai Hanbali a nan ya sava da cewa ba za ta yi haka ba mutuqar an sami jima’i tun da yardar ta da yin jima’i ya tabbatar da amincewarta da auren.(Fiqhu, 4, 165). Hanafi da Shi’a sun ce: ba za ta vata auren ba sai dai za ta iya qin amincewa da jima’i. (Ibid 163, Riyad 11, 109 – 10).
Idan mace ta yanke shawarar dawo da wani kaso ko dukkan sadakin ga mijinta, to mijin ya kuvuta daga wajabcin biyanta.


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: