bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:27:03
Idan auren ya rabu kafin yin jima’i matar ba za ta samu komai a sadakin ba, idan kuma an samu jima’i to tana da gaba xayan sadaki.
Lambar Labari: 157

B. Kulawa Ko Xaukar Nauyi (Nafaqa)
Da zarar mace ta tare a gidan mijinta, dole ne ya xauki nauyin kula da ita dai-dai da mace mai irin matsayinta. Kulawa ta haxa da ciyarwa, tufatarwa, makwanci da abubuwan da suka zama dole a rayuwa. Biyan sadaki ya wajaba a kan miji da zarar an xaura aure, amma ba da kulawa tana tabbata ne kawai a kan miji bisa dalilin bawa mijin damar saduwa da ita da kuma biyayyarta ga mijinta a sauran vangarorin rayuwa. Idan mace ba ta biyayya ga mijinta to ba wajibi ne ya kula da ita ba.
Mu gane fa! a musulunci, dole ne mace ta yi biyayyaga mijinta amma a kan abin da bai savawa sharia ba. Da zai umarce ta da aikata savanin sharia to Allah kawai za ta bi ba mijinta ba.
Yayin da mace take cikin idda bayan saki na kome, to tana da haqqin kulawa tun da har yanzu matarsa ce. Matar da take iddar sakin da ba na kome ba (manisancin saki) na da haqqin kulawa ne kawai idan tana da ciki.
A mahangar Maliku, Hambali da shafi’i, idan ta bayyana miji ba zai iya kulawa da matarsa  a kan abubuwan  rayuwa ba, tana da ‘yancin neman raba auren ta hannun Alqali. Shi’a da Hanafiyya sun ce matar da ba ta samun cikakkiyyar kulawa daga mijinta za ta iya kai qara wajen Alqali, shi kuma alqali na da haqqin xaukar duk matakin da ya ga zai kai ga daidaita yanayin, misali, jan hakalin mijin ya nemi aikin yi.( Fiqhu, 4, 581 Sharhul Lum'a 5, 237 – 38 Riyadh, 11, 109 – 10).

C. Rabuwa  
A duk lokacin da xayan ma’aurata ya samu nakasa ta jiki ko tavin hankali wanda ci gaba da zama tare da shi zai wuya, xayan na da `yancin neman rabuwa. Wannan nakasa wato nau’o’in ta sun sava a mahangar mazhabobi. Dukkanin mazhabobin ban da Hanafiyya sun tafi a kan cewa hauka, rauni na kasala, ko qunci talauci, rashin kuzari na xa namiji da kuma rashin hankali, kuturta da toshewar farjin matar, haka nan duk mazhabobin ban da Hanafiyya sun qara adadin wasu nakasoshi a kan waxanda suka gabata, waxanada ma’aurata za su iya rabuwa idan sun samu. Mazhabar Hanafiyya ta ce mace na da `yancin rushe aure idan abubuwa ukun da suka gabata suka sami mijinta, amma miji ba shi da ikon rusa aure domin wata nakasa.(Fiqhu, 4, 189 – 92).
Dayan ma’aurata na da ‘yancin rusa aure idan ya gano wata nakasa ga xayan, amma dole a gaggauta rabawa ko kuma `yancin ya saraya. Haka nan idan akwai masaniyar samuwar nakasa kafin xaura aure, to xaura auren ya nuna amincewa da wannan nakasa, don haka babu hujjar vata auren, sai dai, shafi’i da Maliki sun tafi a kan cewa; sanin mace game da rashin qarfin namiji kafin aure ba zai ba ta `yancin warware auren ba. (Ibid, 197).
Idan auren ya rabu kafin yin jima’i matar ba za ta samu komai a sadakin ba, idan kuma an samu jima’i to tana da gaba xayan sadaki.
Gaba xayan mazhabobin sun tafi a kan haka kuma sun haxu a kan cewa ana iya raba aure saboda naqasar da xayan ma'auratan yake da ita tun kafin xaura aure, sai dai akwai savani idan naqasar ta sami xayan su bayan xaura aure. Maliki ya ce, , dangane da nakasa bayan xaura aure, matar ce kawai take da ‘yancin rushe auren kafin yin jima’i matuqar mijin lafiyarsa qalau kafin auren. Amma dangane da hauka da kuturta, ana ba mijin shekara xaya don neman magani idan bai samu waraka cikin shekara xaya ba, to sai a vata auren. (Ibid 181 – 98). Duk mazhabobin nan sun haxu a kan cewa ana buqatar shekara xaya kafin alqali ya tabbatar da hukunci a kan miji, bayan shekara xaya to a na iya raba auren. Shafi’i da Hambali sun tafi a kan cewa duk ma’auratan suna da damar raba auren ko dai kafin ko bayan yin jima’i. Mazhabobin sunna sun tafi a kan cewa Alqali ne zai raba auren. Shi’a sun tafi a kan cewa nakasar da ta faru bayan yin aure ba hujja ce ta vata aure ba, idan ka xauke nakasa ta hauka daga miji, a kan lamarin hauka, ana raba aure ko da kuwa bayan yin jima’i ne, amma game da rashin kuzarin namiji, matar za ta nemi Alqali ya ba shi tsawon shekara xaya, bayan lokacin tana iya sa a raba auren. (Sharhul Lum'a 5, 387 Riyad 11, 132 – 35).

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: