bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:43:20
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna kan saukar waxannan surori biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa, an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haxa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah)
Lambar Labari: 158
سورة الفلق
 
SURATUL FALAƘ (SURA TA 113)

DALILIN SAUKA
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna kan saukar waxannan surori biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa, an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haxa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah) sai ya zama kamar yadda su ke cewa a waxannan ruwayoyin na su wai Manzon (SAW) na jin kamar ya yi wani abu amman wai bai yi ba, sai ya ji kamar ya zo gida amman bai zo ba, kamar ya jewa iyalan sa amman bai je ba.
Mabiya Imam Ali (AS) da ƴaƴan sa sun yi raddin wannan magana raddi mai tsanani su na ganin wannan maganar da ta fito daga yan uwan mu ahlussunna an ƙirƙiro tane kawai don a rusa musulunci, ana son nuna cewa wani abu zai iya tasiri kan ruhi mai tsarki na Manzo (SAW), alhalin idan ka ga wani ya yi tasiri kan ruhin wani, ruhin mai tasirin ya fi ƙarfi, shi kuwa manzo (SAW) ya na tattare ne da ruhil ƙuds alhalin ba zai yiyu wanda bashi da ruhil ƙuds ya yi tasiri kan wanda ke da ruhil ƙuds ba, musamman ma irin na Manzo (SAW) da ya fi na kowa ƙarfi, wannan ba zai taɓa yiyuwa ba, sannan  duk wanda ke da ruhil ƙuds Allah na bashi kariya daga dukkan wani abu da zai iya taɓa hankalin su har abada ba zai yiyu ba, ran su na da ƙarfi sosan gaske, ba wani abu da ya fi shi ƙarfi, kuma duk abinda su ka so su yi da izinin Allah za su iya, kamar yadda ya zo a ƙurani mai girma da ruwayoyi.
Matsalar da kan iya biyo bayan waccen magana ta ahalussuna shine: kenan zai yiyu a saukar masa da wahayi ya manta ko kuma ba'a saukar ba ya zata cewa an saukar masa, ko ya zata ya isar da wani saƙo ashe bai isar ba, don haka wancccen ruwaya da tunani na su idan aka bi shi ba inda zai kai musulunci sai ga rushewa, Allah ya kare mu.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ (1)
Ce ina neman tsarin ubangijin asuba/safiya.

مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ (2)
Daga sharrin dukkan abinda ka halitta (hatta mutum a kan kansa, kada ya zamewa kansa sharri akan sa).

وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ (3)
Da sharrin dare idan ya yi duhu (lokacin ne wasu ke samun lulluɓewar duhu su aikata saɓo, domin ba daren ne da sharrin ba, masu amfani da shi wajan aikata sharrin ne ke zama sharrin lokacin).

وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ (4)
Daga sharrin masu tofi cikin ƙulle – ƙulle su na yi wa mutane sihiri cikn ƙulli (masu sihiri don samun biyan buƙatar su kan mutane, ta hanyar tsafi da makamancin su).

وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ (5)
Daga sharrin mai hassada idan ya tashi hassadar sa (masu hassada su ne mafiya sharrin abokan zama, domin su kan ioya kashe ma'abocin ni'ima yayin da hassadar su ta motsa, Allah ya yi mana tsari daga sharrin mai hassada).

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: