bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:48:19
ABUBUWAN DA WAHABIYAWA SU KA SA6A DA SAURAN MUSULMAI Wahabiyawa sun sa6a da sauran musulmai kan mafiya yawan abubuwan da su ke na ijtihadi, zaka samu a iya sa6awa da wahabiyawa kan : abubuwan da ke 6ata salla,
Lambar Labari: 159


ABUBUWAN DA WAHABIYAWA SU KA YI ITTIFAKI DA SAURAN MUSULMAI
Wahabiyawa sun yi ittifaki da sauran musulmai kan mafiya yawan  abubuwan da su ke na wajibi da su ka zo daga sharia madaukakiya da sanin Allah, sun yi ittfaki da bakikayan musulmai kan abubuwa da yawa kamar:
1-    Kadaitakar Allah.
2-    Imani da Manzo (SAW) sa sauran dukkan annabawa.
3-    Tashin kiyama.
4-    Al'kurani.
5-    Hisabi.
6-    Siradi
7-    Lada
8-    Azaba.
9-    Wajabcin sallah, zakka, azumi, Hajji,
10-    haramcin karya, giya, ha'inci, giba,
11-    siffofinn Allah, dss
ABUBUWAN DA WAHABIYAWA SU KA SA6A DA SAURAN MUSULMAI
Wahabiyawa sun sa6a da sauran musulmai kan mafiya yawan abubuwan da su ke na ijtihadi, zaka samu a iya sa6awa da wahabiyawa kan : abubuwan da ke 6ata salla, azumi, mikdarin zakka, wasu aiyyuka na hajji, ya siffofin Annabi da wasiyyan sa su ke, shin kurani abin halitta ne ko ba abin halitta ba, da sauran su, a takaice dai ina son cewa: dukkan fitina na cikin mas'alolin ijtihadi.
Wadannan abubuwa ne ke nuna cewa ba abinda zai hana hadin kai tsakanin musulmai baki daya, hatta da wahabiyawa da su ne kadai masu bakin kafirta sauran 6angarorin muslmai, zai iya yiyuwa kenan a samu masallaci da limami wahabi, mamu yan shia ko darika, ko akasin haka.
Idan haka ne me ya sa wahabiyawa ke tuhuma kan wanda ya yi riko da mazhabin Ahlulbait (AS) a fikihu da akida? Me ya sa wani a fikihu zai zama hanafi, Hambali, Maliki, Shafi'iy, a akida ya zama maturidi, ash'ary ko Mu'utazili, amman bawahabiye zai takura shi ya tsananta masa sabida kawai ya zama ba shi ba, wannan ba karamin rashin adalci bane da wahabiyawa kewa sauran 6angarorin muslmi musamman shia, wannan a takaice kenan dangane da abinda ya shafi tunanin da kallon bawahabiye kan sauran musulmi da shia, wadannan buhus ne masu fadi amman mun takaice su a matsayin gabatarwa.
Hanyar da tafi kai waye da muhimmanci wajan ganarwa ko munakasha da bawahabiye shine hanyar: tabbatar da hadisin thakalain da hadisin da ke tabbatar da halifofin sha biyu ne maimakon yadda ahlus sunna ke lissafa su da hudu a yau.
Sabida haka ne ma ya kamata kowa cikin mabiya mazhabin Ahlulbait (AS) ya san hujjoji da masadir tare da lissafi na hankali kan hadisin thakalain da na adadin halifofi sha biyu koda duk mutum daya na da nasa lissafin hankali bayan dogara da nassi, wannan ne mafi karancin abinda ya kamce mu.
Wahabiyawa sun dogara da cewa halifofi sha biyu bisa ijtihadi za a fitar da su ba ta hanyar ruwaya ba, bayan akwai ruwayar da ta kawo su mai yawa cikin litattafan da su ka yi imani da su, mu kuma cikin sauki za mu iya tabbatar musu da cewa halifofi sha biyu ne kuma nassi ne ya tabbatar da su ba ijtihadi ba.
Saiyyidunal Ustaz na cewa: duk tarihin dan adam kakaf cin sa, babu wata al'umma da mu ke da labari za mu iya tabbatar da ita a rubuce koda ko akwai ta amman dai bamu da shi a hujja, in banda halifofi sha biyun da Manzo (SAW) ya kawo su daga Imam Ali (AS) har zuwa Imam Mahdi (AF) wadanda al'ummar musulmi su ka yi ittafiki kan cewa babu kamar su a falala, ilimi da tsoron Allah.
Ba mamaki wahabiyawa da salafawa su yi inkarin wannan magana sabida su na bin koyarwar Ibni taimiyya ne, shi kuma yana gaba da gidan Annabta, amman kafin sa ba'a samu mai musun wannan ba a tarihin musulunci, sannan suka zama a jere kowannen su ya haifi magajin sa, dukkan su kuma sun rayu cikin mutane.
Fifikon su kan tabbata idan mu ka duba tarihin rayuwar su cikin mutanen da su ka zauna, zamu ga yadda su ke munazara cikin mutane, karfin kafa hujjar su yayin da su ke magana da ma'abota addinai.
Kashi na biyar na nan tafe in Allah ya so

Don neman karin bayani kuna iya duba Littafin Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
 
 
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: