bayyinaat

Published time: 25 ,January ,2017      11:32:33
Alaka da sauran mutane fanni ne daga cikin muhimman fannonin rayuwa ta zamantakewa, da yawa daga cikin mutane ba sa kyautata fannin alaka da sauran mutane…don haka ne suke fuskantar rashin nasara wajen samun abokai da kuma lalata alakarsu da sauran mutane. Hakan kuwa saboda ba su san yadda za su jawo hankalin mutane (abokai) zuwa gare su ba ne da kuma yadda za su yi mu'amala da su ba. Hakika ilmummukan sanin dan'Adam, na yau da kullum da kuma uwa-uba shiryarwa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma tsarkakan Imamai (a.s.) duk sun koyar da mu hanyoyin samun abokai da kuma yadda za mu yi mu'amala da su.
Lambar Labari: 16
Tun farko-farkon yarinta, hatta ma kafin yaro ya koyi magana, yakan fara komawa da kuma kaunar yaran da suke tare da shi a cikin gida. Yakan yi wasa da rige-rige da su kan abubuwan wasa ko kuma halawa da dai sauran abubuwan da suke hannayensu... 
Hakika irin wannan komawa ta dabi'a zuwa ga sauran mutane da yaro yake yi, bugu da kari kan wasa da sauran yara 'yan'uwansa, yana nuni da irin sha'awar zaman tare da ke tattare da dan'Adam….. 
Don kuwa an halicci mutum (cikin hikimar Ubangiji) ne don ya rayu cikin al'ummar, don haka ne sha'awarsa da kuma ruhinsa da ke son rayuwa tare da sauran mutane suke tura shi zuwa ga kulla alaka tare da sauran mutane. Don haka kuma mutum yakan ji kadaitaka da kuma damuwa a duk lokacin da ya kasance shi kadai ba tare da wani a kusa da shi ba. Ba wai kawai hakan ba, lalle dan'Adam dai yana bukatuwa da waninsa kamar yadda wanin nasa shi ma yake bukatuwa da shi. Sannan kuma ta hanyar sanayya, abokantaka, taimakekkeniya, tattaunawa da canje-canjen tunani da manufofi, dan'Adamtakan mutum takan cika, haka nan ma samuwa da kuma bukatunsa na duniya da kuma na ruhi…. 
Alkur'ani mai girma ya bayyana mana wannan hakika, cikin fadinSa Madaukaknin Sarki cewa: 
"Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabiloli domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa…." (Surar Hujurat, 49: 13) 
Ta haka ne rayuwar mutum ta kasance tausayi, soyayya da kuma taimakekkeniya …babu alheri cikin mutumin da ba ya son mutane haka su ma ba sa son sa. Sannan kuma a bangare guda irin wannan mummunan dabi'a ta gudun jama'a tana nuni ne da irin nakasi da kuma rashin yarda da kai da shi wannan mutumin yake fama da shi… 
Lalle mutum mai halin kaunar jama'a da kuma fara'a ga kowa, wanda kuma yake kokarin kulla alaka da sauran mutane, shi ne mutum wanda ya mallaki siffar yarda da kai kana kuma ma'abucin ingantacciyar dabi'a. Don kuwa shi yakan sami kansa cikin kwanciyar hankali da wadatuwar zuci cikin alakarsa ta abokantaka da sauran mutane a duk lokacin da yake nuna wa sauran mutane fuskar soyayya da yarda sannan su ma suke mayar masa da irin wannan siffa abin yabo. 
Mutum yakan sami kyakkyawar alaka da abokansa ne ta hanyar tattaunawar farin ciki, wasannin motsa jiki, karatu, taimakon abubuwan rayuwa, ayyukan taimakon jama'a, da dai sauransu…a daidai wannan lokacin mutum zai sami kansa cikin yanayin yarda da kai da kuma samun yardar Ubangiji da kuma sauran mutane. Sannan kuma ta hanyar abokantaka da abokan kirki zai samu damar samun kwanciyar hankali da daukakar ruhi. 
Kamar yadda aboki yakan amfana da wasu siffofinsu masu kyau na abokansa, da suka hada da karfinsu na kirkire-kirkire, ilimi da masaniya, haka su ma suke amfanuwa da shi ta hanyoyi daban-daban. A takaice dai ta hanyar wannan abota tasu za su iya amfanuwa da juna. Bugu da kari, ta haka zai iya amfanar da su ta ilimi da masaniyarsa, kyawawan halaye da tunace-tunacensa masu amfani, sannan kuma ta hakan kuma zai dinga jin kimar rayuwarsa da kuma yarda da kai. Don kuwa ta hanyar wannan alaka ta sa da sauran mutane zai iya fahimtar yanayinsa da kuma karfinsa na mu'amala da su da kuma irin tasirantuwan da zai yi da su da kuma samun karfin da yake bukatuwa da shi. Dukkan hakan zai sanya masa kwanciyar hankali da kuma yarda da kai. 
Hakika kimar ingantaccen yanayin mutum yana tabbata ne ta hanyar halaye da kuma irin amfanar da al'umma da ya yi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana hakan cikin fadinsa cewa: "Mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da su (mutane) ( )". 
"Duk wanda mummunan aikinsa ya bata masa rai, kana kuma kyakkyawan aikinsa ya dadada masa rai, to mumini ne( )". 
Sannan kuma Imam Ali (a.s.) yana cewa: 
"Kimar mutum tana cikin abin da ya kyautata( )". 

Ya Ya Za Mu Zabi Abokai
Hakika abokin mutum yana nuni ne da irin yanayinsa, a duk lokacin da mutane suka san yanayin abokin mutum, to sun san yanayinsa, haka nan ma a duk lokacin da suka san yanayin mutum, to sun san yanayin abokinsa…. masu iya magana sukan ce abokin barawo, barawo ne, kuma abokin mutum, abokinsa ne cikin tunani. Don kuwa mutum yana koyi da mutanen da yake tare da su cikin halaye da tunani ne. 
Don haka ne ma ya zo cikin wani hadisi mai tsarki cewa: 
"Mutum yana kan addinin (tunanin) masoyinsa, don haka ku binciki wanda za ku yi abota da shi( )". 
Abokantaka ita ce haduwa ta ruhi da kuma tunani wacce take hada tsakanin mutane da kuma haifar da ji-a-jika da kuma tausasawa tsakaninsu… 
Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa 'yan'uwantakar da ta kasance karkashin asasin shiriya da amfanarwa, ita ce soyayya da kuma tausasawa tsakanin zukata, sannan kuma mai hada yanayi da kuma ruhin dan'Adam, kana kuma ya ambaci irin wannan 'yan'uwantaka da soyayya a matsayin babbar ni'ima ga dan'Adam… 
Allah Madakakin Sarki Yana cewa: 
"…Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari da ni'imarsa, 'yan'uwa…" (Surar Al'Imarana, 3: 103) 
Kana kuma Yana cewa: 
"…Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan kasa gaba daya ba za ka iya hada zukatansu ba, amma kuma ga shi Allah Ya hade tsakaninsu…" (Surar Anfali, 8: 63) 
Wannan bayani na alakar 'yan'uwantaka da kuma soyayya da ake samu tsakanin mutane, a bisa asasin imani da ingantacciyar alaka, ita ce tsarkakakkiyar 'yan'uwantaka wacce babu wata cuta a cikinta. Bayanai da kuma kididdigogin da cibiyoyin kula da laifuffuka suka gudanar suna bayyana mana cewa munanan abokai (abokan da ba na kirki ba), ba abokai ba ne, face dai abokan gaba ne. Don kuwa a lokuta da daman gaske mummunar abokantaka takan sanya mutanen kirki cikin halayen banza da muggan laifuffuka. Alkur'ani mai girma yana tsoratar da mu kan yin abota da muggan abokai, don mu samu tsira daga nadama bayan wucewar lokaci. 
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Masoya a yinin nan, sashensu zuwa ga sashe makiya ne, face masu takawa". (Surar Zukhruf, 43: 67) 
Wannan kalami na abokin da yake nadaman zama da abokinsa ya kasance wa'azi da kuma darasi gare mu…haka kuma mun ga yadda abokantaka takan koma ta zama gaba da adawa da kuma fatan da ma mutum bai rayu da wannan mummunan aboki ba…. 
"Sai yace, "da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum". (Surar Zukhruf, 43: 38) 
Don haka zaban aboki, a hakikanin gaskiya zabe ne ga irin nau'in yadda muke so yanayi da kuma mutumcinmu su kasance a idon al'umma, watakila ma muna iya cewa ga rayuwarmu ta nan gaba. Shin mutane nawa ne suka koma suka zama mutanen kirki ma'abuta nasara cikin rayuwa saboda abokansu, sannan kuma mutane nawa ne suka zama mutanen banza kana kuma suka bata rayuwarsu sabobda abokansu... 
Hakika babban kuskure ne mu kulla abokantaka da mutanen da ba mu san yanayin dabi'a da kuma halayensu ba. Me yiwuwa ne mu rudu da zahirinsu, ko kuma maganganunsu masu zaki, ko kuma da taimako da kyaututtukansu na yaudara gare mu, daga nan sai mu sami kanmu cikin abota da su abotar da ba za ta taba kuntuwa ba… 
Don haka dole mu ba da muhimmancin gaske da kuma kulawa ta koli wajen zaben mutanen da za mu yi abota da su bayan sani da fahimtar yanayinsu ta hanyar alaka ta makaranta, ko kuma a masallaci, ko rayuwa waje guda a gida guda, ko wajen aiki. Mai yiwuwa ne kuma mu sadu da wasu mutane yayin tafiya, ko kuma mutanen da suke bayyana kawukansu ta hanyar wasika, ta haka sai mu kulla alaka ta abota a tsakaninmu da su…to irin wannan nau'i na alaka, dole ne mu tabbatar da shi da kuma bincike sosai a kansa kafin mu kulla shi. Don kuwa irin wadannan mutane ba wai mun sansu sosai ba ne a farkon alakar tamu da su ba….a saboda haka dole ne mu zuba idanu sosai da kuma tunani kafin yarda da su. 

Yadda Za Ka Kasance Abokin Kirki
Alaka da sauran mutane fanni ne daga cikin muhimman fannonin rayuwa ta zamantakewa, da yawa daga cikin mutane ba sa kyautata fannin alaka da sauran mutane…don haka ne suke fuskantar rashin nasara wajen samun abokai da kuma lalata alakarsu da sauran mutane. Hakan kuwa saboda ba su san yadda za su jawo hankalin mutane (abokai) zuwa gare su ba ne da kuma yadda za su yi mu'amala da su ba. Hakika ilmummukan sanin dan'Adam, na yau da kullum da kuma uwa-uba shiryarwa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma tsarkakan Imamai (a.s.) duk sun koyar da mu hanyoyin samun abokai da kuma yadda za mu yi mu'amala da su…. 
Wadannan shiryarwa da kuma ilmummuka sun tabbatar mana da cewa mutum mai son kansa ba zai iya samun abokai ba, a duk lokacin da ya kulla wata alaka da wasu mutane ba da jimawa ba alakar za ta yi tsami saboda son kansa. Shi ba ya so musu abin da yake so ma kansa, haka nan ma ba ya ki musu abin da yake ki ma kansa, face dai dukkan kokarinsa shi ne shagaltar da su kan abubuwan da za su amfane shi kawai, don haka suke gudu daga gare shi. To amma a lokacin da aboki ya fahimci cewa abokinsa yana mu'amala da shi cikin soyayya da sadaukarwa da kuma kula da maslahohinsa a matsayinsa na abokinsa, ba makawa zai girmama shi, da kuma kokarin kara kyautata alakar da take tsakaninsu…. 
Don haka dole ka kasance maras son kai matukar kana son samun abokai…kana ka yi mu'amala da su cikin sadaukarwa…sadaukarwa kuwa ita ce gabatar da maslahar waninka a kan maslahar kanka a duk lokacin da ka fahimci yana bukatuwa da ita… 
Lalle Alkur'ani mai girma ya yabi irin sadaukar-war da Muhajirai (mutanen Makka) da Ansarawa (mutanen Madina) suka yi a tsakaninsu a matsayin-su na 'yan'uwa…don kuwa sun rayu rayuwa ta 'yan'uwantaka da abokantaka. An ruwaito cewa bayan hijirar Annabi (s.a.w.a.) zuwa garin Madina, mutanen Madina sun kasance sukan bai wa Muhajirai dukkan abubuwan da suke bukata na daga wajen zama, abinci, aure, tufafi, kai hatta ma ko da shi (mutumin Madinan) yana bukatuwa da wadannan abubuwa. Don haka ne Alkur'ani mai girma ya yabi wannan sadaukarwa da kuma jinjina wa Ansarawan saboda irin wannan taimako da suka yi wa Muhajirai suna masu neman yardar Allah…. 
Saboda girman wannan sadaukarwa da suka yi, har aka saukar da aya don jinjina musu, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: 
"Da wadanda suka zaunar da gidajensu (ga Musulunci) kuma (suka zabi) imani, a gabannin zuwansu, suna son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma basu tunanin wata bukata a cikin kirazansu daga abin da aka bai wa muhajirai, kuma suna fifita wadansu a kan kawukansu, kuma ko da suna da wata larura. Wanda ya saba wa rowar ransa, to, wadannan su ne masu babban rabo". (Surar Hashr, 59: 9)

MU'ASSASAR AL-BALAGH
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: