bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:52:08
Hadisi daga sunna da shia sun tabbata cewa: Manzo (SAW) ya yi wasiyya ya bar mana littafin Allah da 'ya'yan gidan sa, wadanda su ne wasiyyan sa, duk wanda ya ce Ahlulbait na luga ne
Lambar Labari: 160

Kamar yadda na fada a baya cewa cikin sauki abubuwa kan cakudewa wahabiyawa/salafawa irin wanna ce ta faru dangane da halifancin halifofi sha biyu, wadanda Imam Ali (AS) ne na farkon su, sun kasa ganewa cewa: shi wannan shugabancin da Allah da Manzon sa su ka baiwa Ahlulbait (AS) ba shugabanci ne na hawa kujerar mulkin Madina ko jazeeratu arab ba, shugabanci ne na ci gaba da shiryar da mutane bisa tafarkin sakon annabta da koyarwar addini, shi hawa mulki bayan wafatin Manzo (SAW) kujera ce wacce yau ba mutum daya a duniyar yau da zaka iya nunawa cewa yanzu shi ne a kanta, Da ace wahabiyawa/salafawa za su iya cewa sun yadda su ce abinda muka duka sun zama makomar addini ne, amman ba dole sai sun zama makomar siyasa ba na rike daula (ra'ayin Umar bin Khaddab kenan), sai mu ce musu maganar rike daula wata magana ce ta daban.
Zaka samu duk masu mulkin siyasa a zamanin su na komawa zuwa gare su, musamman komawar Abubakar, Umar da Usman wajan Imam Ali (AS) a dukkan wani abu da ya shige musu duhu na addini, kai hatta Mu'awiya na komawa wajan Imam Ali da Imam Hassan (AS) cikin ma'alolin da su ka rikice masa dayawa idan ya rasa yadda zai yi, sai ya aiko da wasika ta hannun wasu mutane da sunan su na tambaya sai su kai masa ba tare da ya bayyana kan sa ba,  akwai wadannan abubuwan cikin litattafai daban – daban, har ma akwai wata wani ya zo ya yi tambaya sai Imam Ali (AS) ya tambaye shi cewar shin daga daular sa ya ke, ya ce : e, sai Imam Ali ya ce masa: ba daga daula ta kake ba, sai mutumin ya fadi gaskiya ya ke cewa; Mu'awiya ne ya turo shi da wadannan tambayoyin, do haka wannan ya nuna makomar addini dole a sakar musu domin duk wanda ke gaban su a lokacin su ya gaza idan ba su ba.
Wilayar da aka ba halifofi sha biyu ta hada komai, fashin shugabanci aka yi musu, kuma wannan bai hana su zama halifofi ba, kai koda ba wanda ya saurare su, su na nan a matsayin su na halifofi, kawai da wannan al'ummar ta riki sunnar mutanen annabi Musa da Isa (AS) da sauran annabawa, wadanda aka hana wasiyyan su maye gurbin su na shugabanci aka bar musu makomar addini kawai, wannan na nuna cewa: bisa dalili na nassi da hankali babu yadda za a yi wasun su, su fi su cancanta da maye gurbin kakan su Manzo (SAW).
Hadisi daga sunna da shia sun tabbata cewa: Manzo (SAW) ya yi wasiyya ya bar mana littafin Allah da 'ya'yan gidan sa, wadanda su ne wasiyyan sa, duk wanda ya ce Ahlulbait na luga ne sai mu duba mu gani, me Manzo (SAW) ya fassara, mu duba lafuzzan daban – daban da su ka yi musharaka, (duk da mustarakatul lafziyya na cakudewa bawahabiye).
Kashi na shida na nan tafe in Allah ya so

Don neman karin bayani kuna iya duba Littafin Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
 
 
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: