bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      21:59:57
Ya mai mallakar buqatun masu roqo, ya san abin da ke cikin zukatan masu shiru, a kowace mas’ala kana da ji mai halarta, da amsa mai qarfi; Ubangiji muna neman alqawuranka na gaskiya
Lambar Labari: 161
Rajab

اعمال شهر رجب

دعاء كل يوم من شهر رجب
يَا مَنْ يَمْلِكُ حَوَائِجَ السَّائِلِينَ، وَيَعْلَمُ ضَمِيرَ الصَّامِتِينَ، لِكُلِّ مَسْأَلَةٍ مِنْكَ سَمْعٌ حَاضِرٌ وَجَوَابٌ عَتِيدٌ؛ اللهم وَمَوَاعِيدُكَ الصَّادِقَةُ وَأَيَادِيكَ الْفَاضِلَةُ وَرَحْمَتُكَ الْوَاسِعَةُ، فَأَسْأَلُكَ أَنْ تُصَلِّيَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ، وَأَنْ تَقْضِيَ حَوَائِجِي لِلدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَي‏ءٍ قَدِيرٌ.

Ayyukan Watan Rajab
Addu’ar Kowace Rana a Watan Rajab
Ya mai mallakar buqatun masu roqo, ya san abin da ke cikin zukatan masu shiru, a kowace mas’ala kana da ji mai halarta, da amsa mai qarfi; Ubangiji muna neman alqawuranka na gaskiya, da taimakonka mai falala, da rahamarka mai yalwa, to ina roqon ka yi aminci ga Muhammad da alayen Muhammad, ka biya mini buqatar duniya da lahira, lallai kai mai iko ne kan komai.
***

خَابَ الْوَافِدُونَ عَلَى غَيرِكَ وَخَسِرَ الْمُتَعَرِّضُونَ إِلاّ لَكَ، وَضَاعَ الْمُلِمُّونَ إِلاّ بِكَ، وَأَجْدَبَ الْمُنْتَجِعُونَ إِلاّ مَنِ انْتَجَعَ فَضْلَكَ، بَابُكَ مَفْتُوحٌ لِلرَّاغِبِينَ، وَخَيرُكَ مَبْذُولٌ لِلطَّالِبِينَ، وَفَضْلُكَ مُبَاحٌ لِلسَّائِلِينَ، وَنَيلُكَ مُتَاحٌ لِلْآمِلِينَ، وَرِزْقُكَ مَبْسُوطٌ لِمَنْ عَصَاكَ، وَحِلْمُكَ مُعْتَرِضٌ لِمَنْ نَاوَاكَ، عَادَتُكَ الْإِحْسَانُ إِلَى الْمُسِيئِينَ، وَسَبِيلُكَ الْإِبْقَاءُ عَلَى الْمُعْتَدِينَ؛ اللهم فَاهْدِنِي هُدَى الْمُهْتَدِينَ، وَارْزُقْنِي اجْتِهَادَ الْمُجْتَهِدِينَ، وَلا تَجْعَلْنِي مِنَ الْغَافِلِينَ الْمُبْعَدِينَ، وَاغْفِرْ لِي يَوْمَ الدِّينِ.

Masu zuwa ga waninka sun tave, masu bijirewa sun yi hasara sai dai gare ka, masi naci sun tozarta sai dai gun ka, mai su neman falalarka sun sare sai dai masu neman falalark. Qofarka buxaxxiya ce ga masu kwaxayi, alherinka abin bayarwa ne ga masu nema, falalarka halar ce sai ga masu roqa, nemanka mai yalwa ne ga masu buri, arzikinsa abin shimfixawa ne ga wanda ya sava maka, haqurinka mai gabatowa ne ga wanda ya neme ka, ala'darka ce kyautayi ga masu munanawa, ala'darka ce qyalwa ga masu shisshigi; Ubangiji ka shiryar da ni shiriyar masu shiryuwa, ka arzuta ni qoqarin masu qoqari, ka da ka sanya ni daga gafalallu da aka nesantar, ka gafarta mini a ranar sakamako.
***

اللهمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ صَبْرَ الشَّاكِرِينَ لَكَ، وَعَمَلَ الْخَائِفِينَ مِنْكَ، وَيَقِينَ الْعَابِدِينَ لَكَ؛ اللهم أَنْتَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ، وَأَنَا عَبْدُكَ الْبَائِسُ الْفَقِيرُ، أَنْتَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ، وَأَنَا الْعَبْدُ الذَّلِيلُ؛ اللهم صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ، وَامْنُنْ بِغِنَاكَ عَلَى فَقْرِي، وَبِحِلْمِكَ عَلَى جَهْلِي، وَبِقُوَّتِكَ عَلَى ضَعْفِي، يَا قَوِيُّ يَا عَزِيزُ؛ اللهم صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ الْأَوْصِيَاءِ الْمَرْضِيِّينَ، وَاكْفِنِي مَا أَهَمَّنِي مِنْ أَمْرِ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، يَا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ .

Ubangiji ina roqonka haqurin masu godiya gare ka, da aikin masu jin tsoronka, da yaqinin masu bauta maka; Ubangiji kai ne maxaukaki mai girma, kuma ni ne bawanka mai rashi talaka, kai ne mawadaci abin yabo, kuma ni ne bawanka qasqantacce; Ubangiji ka yi tsira ga Muhammad da alayensa, ka yi baiwa da wadatarka ga talaucina, da haqurinka ga jahilcina, da qarfinka kan raunina, ya mai qarfi ya mabuwayi; Ubangiji ka yi tsira ga Muhammad da alayensa wasiyyai yardajju, ka isar mini abin da ya dame ni na lamarin duniya da lahira, ya mafi jin qan masu jin qai.
***

اللهمَّ يَا ذَا الْمِنَنِ السَّابِغَةِ، وَالْآلاءِ الْوَازِعَةِ، وَالرَّحْمَةِ الْوَاسِعَةِ، وَالْقُدْرَةِ الْجَامِعَةِ، وَالنِّعَمِ الْجَسِيمَةِ، وَالْمَوَاهِبِ الْعَظِيمَةِ، وَالْأَيَادِي الْجَمِيلَةِ، وَالْعَطَايَا الْجَزِيلَةِ، يَا مَنْ لا يُنْعَتُ بِتَمْثِيلٍ، وَلا يُمَثَّلُ بِنَظِيرٍ، وَلا يُغْلَبُ بِظَهِيرٍ، يَا مَنْ خَلَقَ فَرَزَقَ، وَأَلْهَمَ فَأَنْطَقَ، وَابْتَدَعَ فَشَرَعَ، وَعَلا فَارْتَفَعَ، وَقَدَّرَ فَأَحْسَنَ، وَصَوَّرَ فَأَتْقَنَ، وَاحْتَجَّ فَأَبْلَغَ، وَأَنْعَمَ فَأَسْبَغَ، وَأَعْطَى فَأَجْزَلَ، وَمَنَحَ فَأَفْضَلَ، يَا مَنْ سَمَا فِي الْعِزِّ فَفَاتَ نَوَاظِرَ الْأَبْصَارِ، وَدَنَا فِي اللُّطْفِ فَجَازَ هَوَاجِسَ الْأَفْكَارِ، يَا مَنْ تَوَحَّدَ بِالْمُلْكِ فَلا نِدَّ لَهُ فِي مَلَكُوتِ سُلْطَانِهِ، وَتَفَرَّدَ بِالْآلاءِ وَالْكِبْرِيَاءِ فَلا ضِدَّ لَهُ فِي جَبَرُوتِ شَانِهِ، يَا مَنْ حَارَتْ فِي كِبْرِيَاءِ هَيبَتِهِ دَقَائِقُ لَطَائِفِ الْأَوْهَامِ، وَانْحَسَرَتْ دُونَ إِدْرَاكِ عَظَمَتِهِ خَطَائِفُ أَبْصَارِ الْأَنَامِ، يَا مَنْ عَنَتِ الْوُجُوهُ لِهَيبَتِهِ، وَخَضَعَتِ الرِّقَابُ لِعَظَمَتِهِ، وَوَجِلَتِ الْقُلُوبُ مِنْ خِيفَتِهِ، أَسْأَلُكَ بِهَذِهِ الْمِدْحَةِ الَّتِي لا تَنْبَغِي إِلا لَكَ،

Ubangiji ya mai baiwa cikakka, da ni'imomi abin rabawa, da rahama mai yalwa, da qarfi tararre, da ni'ima gaggausa, da baiwowi manya, da ni'imomi kyawawa, da kyautuka masu yawa. Ya wanda ba a siffanta shi da misaltawa, kuma ba a misalta shi da tamka, kuma ba ya rinjayrsa da qarfi, ya wnda ya halitta sai ya arzuta, kuma ya yi ilhama sai ya furta, ya qirqira kuma ya farar, ya xaukaka sai ya yi sama, ya qaddara sai ya kyautata, ya sauwara sai ya qayata, ya kafa hujja sai ya isar, ya ni'imta sai ya cika, ya bayar sai ya yawaita, ya yi bayiwa sai ya yi falala. Ya wanda ya xaukaka a buwaya, kallon idanuwa sun gaza ganin sa, ya yi matuqar kusanta ta hanyar luxufin sa, ya ya qetare dukkan tunanunnuka, ya wanda ya kaxaita da a mulki, ba wani mai sarauta a da ke kishiyantar sa cikin ikon sa, ya kaxaita da ni'imomi da girma, bashi da kishiya cikin xaukakar sha'nin sa, ya wanda kwarjinin sa ke ruxa duk masu kwarjini da zurfin mara misaltuwa, wanda ba a gane girman sa hatta da hasken ganin/kallon masu hange, ya wanda fusaku su ka rusunawa kwarjinin sa, wuyayu su ka sunkuyawa girman sa, zukata su ka raurawa da tsoron sa, ina roqon ka da wannan yabon da ba wanda ya cancance shi sai kai.
***

وَبِمَا وَأَيتَ بِهِ عَلَى نَفْسِكَ لِدَاعِيكَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ، وَبِمَا ضَمِنْتَ الْإِجَابَةَ فِيهِ عَلَى نَفْسِكَ لِلدَّاعِينَ، يَا أَسْمَعَ السَّامِعِينَ، وَأَبْصَرَ النَّاظِرِينَ، وَأَسْرَعَ الْحَاسِبِينَ، يَا ذَا الْقُوَّةِ الْمَتِينَ، صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ خَاتَمِ النَّبِيِّينَ وَعَلَى أَهْلِ بَيتِهِ، وَاقْسِمْ لِي فِي شَهْرِنَا هَذَا خَيرَ مَا قَسَمْتَ، وَاحْتِمْ لِي فِي قَضَائِكَ خَيرَ مَا حَتَمْتَ، وَاخْتِمْ لِي بِالسَّعَادَةِ فِيمَنْ خَتَمْتَ، وَأَحْيِنِي مَا أَحْيَيتَنِي مَوْفُوراً، وَأَمِتْنِي مَسْرُوراً وَمَغْفُوراً، وَتَوَلَّ أَنْتَ نَجَاتِي مِنْ مُسَاءَلَةِ الْبَرْزَخِ، وَادْرَا عَنِّي مُنْكَراً وَنَكِيراً، وَأَرِ عَينِي مُبَشِّراً وَبَشِيراً، وَاجْعَلْ لِي إِلَى رِضْوَانِكَ وَجِنَانِكَ مَصِيراً، وَعَيشاً قَرِيراً وَمُلْكاً كَبِيراً، وَصَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ كَثِيراً.

Da abin da ka tanadar wa masu roqon ka daga bayin ka muminai, da abin da ka ruvanya amsar sa wajan muminan da su ka ambace ka, ya mafi jin masu ji, ya mafi ganin masu gani, ya mafi saurin masu hisabi, ya ma'abocin cikakken qarfi, ka yi salati ga Muhammad cikamakin annabawa da iyalan gidan sa, ka sa ni cikin mafi samun alherin rabon da ka ke rabawa cikin wannan wata, ka zava min mafi kyan abinda na cancance shi wajan ka, ka cika min da dacewa daga waxanda ka cikawa, ka rayani da cikakkiyar rayuwa, ka kashe ni ina mai farin ciki abin gafartawa,ka zamar min kuvuta daga tambayar qabari/barzahu, ka zamar min mafaka daga Munkar da Nakir, ka haxa idanu na da Mubashshir da Bashiir, ka sanya ni zuwa ga yardar ka da aljannonin ka, ka zava min qayatacciyar rayuwa da babban mulki, ka yi salati mai yawa ga Annabi Muhammad da iyalan sa tsarkaka.
***

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ؛ اللهم إِنِّي أَسْأَلُكَ بِمَعَانِي جَمِيعِ مَا يَدْعُوكَ بِهِ وُلاةُ أَمْرِكَ، الْمَامُونُونَ عَلَى سِرِّكَ، الْمُسْتَبْشِرُونَ بِأَمْرِكَ، الْوَاصِفُونَ لِقُدْرَتِكَ، الْمُعْلِنُونَ لِعَظَمَتِكَ، أَسْأَلُكَ بِمَا نَطَقَ فِيهِمْ مِنْ مَشِيَّتِكَ، فَجَعَلْتَهُمْ مَعَادِنَ لِكَلِمَاتِكَ، وَأَرْكَاناً لِتَوْحِيدِكَ وَآيَاتِكَ وَمَقَامَاتِكَ، الَّتِي لا تَعْطِيلَ لَهَا فِي كُلِّ مَكَانٍ، يَعْرِفُكَ بِهَا مَنْ عَرَفَكَ، لا فَرْقَ بَينَكَ وَبَينَهَا إِلاّ أَنَّهُمْ عِبَادُكَ وَخَلْقُكَ، فَتْقُهَا وَرَتْقُهَا بِيَدِكَ، بَدْؤُهَا مِنْكَ وَعَوْدُهَا إِلَيكَ، أَعْضَادٌ وَأَشْهَادٌ، وَمُنَاةٌ وَأَذْوَادٌ، وَحَفَظَةٌ وَرُوَّادٌ، فَبِهِمْ مَلَاتَ سَمَاءَكَ وَأَرْضَكَ، حَتَّى ظَهَرَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، فَبِذَلِكَ أَسْأَلُكَ وَبِمَوَاقِعِ الْعِزِّ مِنْ رَحْمَتِكَ، وَبِمَقَامَاتِكَ وَعَلامَاتِكَ، أَنْ تُصَلِّيَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ وَأَنْ تَزِيدَنِي إِيمَاناً وَتَثْبِيتاً، يَا بَاطِناً فِي ظُهُورِهِ، وَظَاهِراً فِي بُطُونِهِ وَمَكْنُونِهِ، يَا مُفَرِّقاً بَينَ النُّورِ وَالدَّيجُورِ، يَا مَوْصُوفاً بِغَيرِ كُنْهٍ، وَمَعْرُوفاً بِغَيرِ شِبْهٍ، حَادَّ كُلِّ مَحْدُودٍ، وَشَاهِدَ كُلِّ مَشْهُودٍ، وَمُوجِدَ كُلِّ مَوْجُودٍ، وَمُحْصِيَ كُلِّ مَعْدُودٍ، وَفَاقِدَ كُلِّ مَفْقُودٍ، لَيسَ دُونَكَ مِنْ مَعْبُودٍ، أَهْلَ الْكِبْرِيَاءِ وَالْجُودِ، يَا مَنْ لا يُكَيَّفُ بِكَيفٍ، وَلا يُؤَيَّنُ بِأَينٍ، يَا مُحْتَجِباً عَنْ كُلِّ عَينٍ، يَا دَيمُومُ يَا قَيُّومُ، وَعَالِمَ كُلِّ مَعْلُومٍ، صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ، وَعَلَى عِبَادِكَ الْمُنْتَجَبِينَ، وَبَشَرِكَ الْمُحْتَجِبِينَ، وَمَلائِكَتِكَ الْمُقَرَّبِينَ، وَالْبُهْمِ الصَّافِّينَ الْحَافِّينَ، وَبَارِكْ لَنَا فِي شَهْرِنَا هَذَا الْمُرَجَّبِ الْمُكَرَّمِ، وَمَا بَعْدَهُ مِنَ الْأَشْهُرِ الْحُرُمِ، وَأَسْبِغْ عَلَينَا فِيهِ النِّعَمَ، وَأَجْزِلْ لَنَا فِيهِ الْقِسَمَ، وَأَبْرِرْ لَنَا فِيهِ الْقَسَمَ، بِاسْمِكَ الْأَعْظَمِ الْأَعْظَمِ الْأَجَلِّ الْأَكْرَمِ، الَّذِي وَضَعْتَهُ عَلَى النَّهَارِ فَأَضَاءَ، وَعَلَى اللَّيلِ فَأَظْلَمَ، وَاغْفِرْ لَنَا مَا تَعْلَمُ مِنَّا وَمَا لا نَعْلَمُ، وَاعْصِمْنَا مِنَ الذُّنُوبِ خَيرَ الْعِصَمِ، وَاكْفِنَا كَوَافِيَ قَدَرِكَ، وَامْنُنْ عَلَينَا بِحُسْنِ نَظَرِكَ، وَلا تَكِلْنَا إِلَى غَيرِكَ، وَلا تَمْنَعْنَا مِنْ خَيرِكَ، وَبَارِكْ لَنَا فِيمَا كَتَبْتَهُ لَنَا مِنْ أَعْمَارِنَا، وَأَصْلِحْ لَنَا خَبِيئَةَ أَسْرَارِنَا، وَأَعْطِنَا مِنْكَ الْأَمَانَ، وَاسْتَعْمِلْنَا بِحُسْنِ الْإِيمَانِ، وَبَلِّغْنَا شَهْرَ الصِّيَامِ، وَمَا بَعْدَهُ مِنَ الْأَيَّامِ وَالْأَعْوَامِ، يَا ذَا الْجَلالِ وَالْإِكْرَامِ .

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, Ubangiji ina roqon ka da dukkan ma'anonin da majivinta lamarin ka su ka roqe ka da da shi, amintattun sirrin ka, abin yi wa bushara da lamarin ka, masu siffantuwa da ikon ka, maxaukaka da girman ka, ina roqon ka don girman abin da ka furta game da su a tafarkin ka, ka sanya su ma'ajin kalmomin ka, rukunnan tauhidin ka da ayoyin ka da matsayan ka, wacce baka bada ita a ko'ina ba, wacce duk wanda wanda ya san ka ke sanin ka da ita, ba bambanci tsakanin ka da su saidai dai kawai su halittun ka ne kuma bayin ka ne, ka xinke su kuma ka buxe su, daga gareka su ke kuma gareka za su koma, ba komai su ka zama ba saimasoya kuma shaidu, masu buqatuwa gareka masu kariya (ga addinin) ne, masu kiyayewa (ga dokokin ka) ne masu sadaukarwa ne ga wasun su sabida kai, da su ne ka cika saman ka da qasan ka, har ta bayyana babu wani ubangiji sai kai, ina roqon ka don girman xaukakar rahamar ka, don girman ka da xaukakar alamar ka, ka yi salati ga Annabi Muhammad da iyalan sa ka qara min Imani da tabbata, ya voyayye cikin bayyanar sa, ya bayyananne cikin vuyan sa da samuwar sa, ya mai banbancewa tsakanin haske da duhu, ya wanda ya siffantu siffantuwa wacce ba irin ta wanin sa ba, sananne ba tare da kishiya ba, iyakar dukka mai iyaka, mai shaidar dukkan abin shaidawa, mai samar da dukkan samammu, mai kiyaye dukkan adadi, makomar dukkan komamme, ba wanin ka da ya cancanci ibada sai kai, ma'abocin girma da baiwa, ya wanda tambaya a kan ya yake bata amsuwa, kuma baya ganuwa da wuri, ya voyayye daga dukkan idanuwa, ya dauwamamme matabbaci, ya mai sanar da dukkan masani, ka yi salati ga Annabi Muhammad da iyalan sa, haka nan ma bisa bayin ka zavavvu, da voyayyun mutanen ka, da makusantan mala'ikun ka,da mala'ikun ka waxanda ka sanya kewaye sahusahu, ka yi mana al'barka cikin wannan wata mai girma da cika, da watannin da ke bayan sa masu girma, ya shimfixa ni'imar sa gare mu, ka yalwata mu da albarka, ka amsa mana wannan fata, don sunayen ka mai girma da xaukaka, wanda ka sanya shi a kan rana ta haskaka, ka sanya shi kan dare ya yi duhu, ka gafarta mana cikin abinda mu ka sani da waxanda ma bamu sani ba, ka kare mu daga zunubin da mu ka san shi da wanda bamu sani ba, ka tsare mu da isar ikon ka, ka amintar da mu da kyan duban ka, kada ka bar mu zuwa ga wanin ka, kada ka hana mu alheran ka, ka al'barkace mu cikin abinda ka rubuta mana a rayuwar mu, ka gyara mana niyyoyin mu, ka amintar da mu da amintarwar ka, kaa sanya mu yin aiki tare da kyautata imani, ka bamu ikon alhairai cikin watan azumi, da ma ranaku da shekarun da ke bayan sa, ya ma'abocin girma da xaukaka.
***

اللهم إِنِّي أَسْأَلُكَ بِالْمَوْلُودَينِ فِي رَجَبٍ، مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيٍّ الثَّانِي وَابْنِهِ عَلِيِّ بْنِ مُحَمَّدٍ الْمُنْتَجَبِ، وَأَتَقَرَّبُ بِهِمَا إِلَيكَ خَيرَ الْقُرَبِ، يَا مَنْ إِلَيهِ الْمَعْرُوفُ طُلِبَ، وَفِيمَا لَدَيهِ رُغِبَ، أَسْأَلُكَ سُؤَالَ مُقْتَرِفٍ مُذْنِبٍ، قَدْ أَوْبَقَتْهُ ذُنُوبُهُ، وَأَوْثَقَتْهُ عُيُوبُهُ، فَطَالَ عَلَى الْخَطَايَا دُءُوبُهُ، وَمِنَ الرَّزَايَا خُطُوبُهُ، يَسْأَلُكَ التَّوْبَةَ وَحُسْنَ الْأَوْبَةِ، وَالنُّزُوعَ عَنِ الْحَوْبَةِ، وَمِنَ النَّارِ فَكَاكَ رَقَبَتِهِ، وَالْعَفْوَ عَمَّا فِي رِبْقَتِهِ، فَأَنْتَ مَوْلايَ أَعْظَمُ أَمَلِهِ وَثِقَتِهِ؛ اللهم وَأَسْأَلُكَ بِمَسَائِلِكَ الشَّرِيفَةِ، وَوَسَائِلِكَ الْمُنِيفَةِ، أَنْ تَتَغَمَّدَنِي فِي هَذَا الشَّهْرِ بِرَحْمَةٍ مِنْكَ وَاسِعَةٍ، وَنِعْمَةٍ وَازِعَةٍ، وَنَفْسٍ بِمَا رَزَقْتَهَا قَانِعَةٍ، إِلَى نُزُولِ الْحَافِرَةِ، وَمَحَلِّ الْآخِرَةِ، وَمَا هِيَ إِلَيهِ صَائِرَةٌ، فَطَالَ عَلَى الْخَطَايَا دُءُوبُهُ، وَمِنَ الرَّزَايَا خُطُوبُهُ، يَسْأَلُكَ التَّوْبَةَ وَحُسْنَ الْأَوْبَةِ، وَالنُّزُوعَ عَنِ الْحَوْبَةِ، وَمِنَ النَّارِ فَكَاكَ رَقَبَتِهِ، وَالْعَفْوَ عَمَّا فِي رِبْقَتِهِ، فَأَنْتَ مَوْلايَ أَعْظَمُ أَمَلِهِ وَثِقَتِهِ؛ اللهم وَأَسْأَلُكَ بِمَسَائِلِكَ الشَّرِيفَةِ، وَوَسَائِلِكَ الْمُنِيفَةِ، أَنْ تَتَغَمَّدَنِي فِي هَذَا الشَّهْرِ بِرَحْمَةٍ مِنْكَ وَاسِعَةٍ، وَنِعْمَةٍ وَازِعَةٍ، وَنَفْسٍ بِمَا رَزَقْتَهَا قَانِعَةٍ، إِلَى نُزُولِ الْحَافِرَةِ، وَمَحَلِّ الْآخِرَةِ، وَمَا هِيَ إِلَيهِ صَائِرَةٌ.

Ya ubangiji ina roqon ka domin girman waxanda aka haifa cikin watan rajab, Muhammad xan Ali na biyu da xan sa Aliyyu xan Muhammad al'munajib, ina neman kusanci zuwa gare ka mafi kusanci domin girman su, ya wanda kowa ya san wajen sa ake nema, kuma abin da ke wajan sa kowa ke kwaxayi, ina roqon ka roqon waxanda ke amsa zunuban su, wanda zunuban sa su ka wanzu tare da shi, aibin sa ya nauyaya, wanda ya duqufa kan aikata zunuba, cututtukan zunubai su ka yanyame shi, yana mai tuba zuwa gareka tare da dawowa zuwa gareka, yana mai nemar fansar kansa daga azabtarwa, yana neman a 'yanta shi daga wuta, ka yafe masa laifukan da ke wuyan sa, kai ne mafi girman burin sa da zavin sa ya majivinci na, ya Ubangiji ina roqon ka da abubuwan da ke wajan ka maxaukaka, da hanyoyin ka maxaukaka, ka qunshe ni cikin yalwatacciyar rahamar ka mayalwaciya cikin wannan wata, da yalwatacciyar ni'imar ka, ina mai gamsuwa da duk abinda ka azurta ni da shi, har zuwa ramin qabari da mazaunina na lahira, har zuwa makomar qarshe.
***

الْحَمْدُ للهِ الَّذِي أَشْهَدَنَا مَشْهَدَ أَوْلِيَائِهِ فِي رَجَبٍ، وَأَوْجَبَ عَلَينَا مِنْ حَقِّهِمْ مَا قَدْ وَجَبَ، وَصَلَّى اللهُ عَلَى مُحَمَّدٍ الْمُنْتَجَبِ، وَعَلَى أَوْصِيَائِهِ الْحُجُبِ؛ اللهم فَكَمَا أَشْهَدْتَنَا مَشْهَدَهُمْ، فَأَنْجِزْ لَنَا مَوْعِدَهُمْ، وَأَوْرِدْنَا مَوْرِدَهُمْ، غَيرَ مُحَلَّئِينَ عَنْ وِرْدٍ فِي دَارِ الْمُقَامَةِ وَالْخُلْدِ، وَالسَّلامُ عَلَيكُمْ إِنِّي قَصَدْتُكُمْ وَاعْتَمَدْتُكُمْ، بِمَسْأَلَتِي وَحَاجَتِي، وَهِيَ فَكَاكُ رَقَبَتِي مِنَ النَّارِ، وَالْمَقَرُّ مَعَكُمْ فِي دَارِ الْقَرَارِ، مَعَ شِيعَتِكُمُ الْأَبْرَارِ، وَالسَّلامُ عَلَيكُمْ بِمَا صَبَرْتُمْ، فَنِعْمَ عُقْبَى الدَّارِ، أَنَا سَائِلُكُمْ وَآمِلُكُمْ فِيمَا إِلَيكُمُ التَّفْوِيضُ، وَعَلَيكُمُ التَّعْوِيضُ، فَبِكُمْ يُجْبَرُ الْمَهِيضُ وَيُشْفَى الْمَرِيضُ، وَمَا تَزْدَادُ الْأَرْحَامُ وَمَا تَغِيضُ، إِنِّي بِسِرِّكُمْ مُؤْمِنٌ، وَلِقَوْلِكُمْ مُسَلِّمٌ، وَعَلَى اللهِ بِكُمْ مُقْسِمٌ، فِي رَجْعِي بِحَوَائِجِي، وَقَضَائِهَا وَإِمْضَائِهَا، وَإِنْجَاحِهَا وَإِبْرَاحِهَا، وَبِشُئُونِي لَدَيكُمْ وَصَلاحِهَا، وَالسَّلامُ عَلَيكُمْ سَلامَ مُوَدِّعٍ، وَلَكُمْ حَوَائِجَهُ مُودِعٍ، يَسْأَلُ اللهَ إِلَيكُمُ الْمَرْجِعَ، وَسَعْيَهُ إِلَيكُمْ غَيرَ مُنْقَطِعٍ، وَأَنْ يَرْجِعَنِي مِنْ حَضْرَتِكُمْ خَيرَ مَرْجِعٍ، إِلَى جَنَابٍ مُمْرِعٍ، وَخَفْضِ عَيشٍ مُوَسَّعٍ، وَدَعَةٍ وَمَهَلٍ إِلَى حِينِ الْأَجَلِ، وَخَيرِ مَصِيرٍ وَمَحَلٍّ، فِي النَّعِيمِ الْأَزَلِ، وَالْعَيشِ الْمُقْتَبَلِ، وَدَوَامِ الْأُكُلِ، وَشُرْبِ الرَّحِيقِ وَالسَّلْسَلِ، وَعَلٍّ وَنَهَلٍ، لا سَأَمَ مِنْهُ وَلا مَلَلَ، وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ وَتَحِيَّاتُهُ عَلَيكُمْ، حَتَّى الْعَوْدِ إِلَى حَضْرَتِكُمْ، وَالْفَوْزِ فِي كَرَّتِكُمْ، وَالْحَشْرِ فِي زُمْرَتِكُمْ، وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيكُمْ، وَصَلَوَاتُهُ وَتَحِيَّاتُهُ، وَهُوَ حَسْبُنَا وَنِعْمَ الْوَكِيلُ .

Ina godiya ga Ubangijin da ya sanya mu ziyarar makwancin waliyyan sa cikin watan Rajab, ya wajabta mana abinda ya wajaba garemu na daga haqqin su, Allah ka yi salati ga Muhammad zavavven, da wasiyyan sa masu girma, ya Allah kamar yadda ka bamu ikon ziyarar makwantan su, ka cika mana alqawarin su, ka sanya mu tare da su, kada ka sanya mu tare da waxanda baza su sha daga qoramun su ba, cikin gidan matsayi da dawwama, amincin Allah ya tabbata gare ku, ina mai aminta da ke tare da riqo da ku, cikin roqo na da biyan buqata ta, shi ne a 'yanta ni daga wuta, da zama tare da ku a makoma, tare da kuvutattun shiar ku, aminci ya tabbata gareku da haqurin ku madalla da gidan qarshe!!
***

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: