bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      22:08:16
Tarihi ya tabbatar mana cewar Shi’anci abu guda ne a da can da kuma yanzu, kuma samun ci gaban da yake faruwa a mas’alolin sa ba komai ba ne sai dai fikirorin da suka vuvvugo daga asalin sa. Kuma da karin wasu babobin da suke samuwa sakamakon alaqoqin waxannan fikirori da kuma haxa wasu mas’aloli da wasunsu da a kan samu a tarihin binciken ilimi na kowane addini ko mazhaba
Lambar Labari: 162
بسم الله الرحمان الرحيم
وصلي الله على محمدوءاله
Tarihi ya tabbatar mana cewar Shi’anci abu guda ne a da can da kuma yanzu, kuma samun ci gaban da yake faruwa a mas’alolin sa ba komai ba ne sai dai fikirorin da suka vuvvugo daga asalin sa. Kuma da karin wasu babobin da suke samuwa sakamakon alaqoqin waxannan fikirori da kuma haxa wasu mas’aloli da wasunsu da a kan samu a tarihin binciken ilimi na kowane addini ko mazhaba.
A yanzu zamu koma zuwa ga farkon Shi’anci da kuma asalin faruwar sa da nuna yadda yake haxuwa da cewa shi ne haqiqanin musulunci. Sannan kuma sai mu ga yadda yake tun farkon samuwarsa da kuma yadda aka samu share fagen kasancewarsa, kuma shin ya faru ne sakamakon ayyukan tausayi ko soyayya, ko kuma sakamakon ayyuka ne masu dogaro da hankali da masu riqon wannan mazhabi suka yi riqo da shi bisa tirjiya da dagewa kan wahalhalu suna masu faxaka da hakan.
Idan muka koma wa waxannan lamuran da aka sava a cikin su muna masu bibiyar abin da masu bahasi suka fitar da abin da ya rigaya, da kuma dukkan abin da suka rinjayar a bahasin su, to dole ne mu gabatar da wasu misalai na wasu ra’ayoyi a wannan fagage waxanda zasu kasance tanadaddu, sannan sai mu bar wa mai karatu fage domin ya fitar da haqiqanin gaskiya da kansa, ya kawo wani ra'ayi nasa da zai yi qoqarin da ya kasance ya dogara bisa ilimi. Yayin da masu tarihi da bincike suke iyakance lokacin faruwar Shi’anci suna iyakance shi ne da lokacin da ya fara tun lokacin Annabi (S.A.W) ne, qarshen sa kuma ya qare da lokacin da aka kashe Imam Husain (A.S), kuma zamu kawo maka wasu daga ra’yoyin su, sai mu bar maka nawa ra'ayi a qarshen fasali.
a- Ra’ayin da suke ganin Shi’anci ya fara daga lokacin wafatin Annabi (S.A.W), kuma waxanda suka tafi a kan wannan ra'ayi sun haxa da:
Na farko: Ibn Khaldon: ya na cewa: "Shi’anci ya bayyana yayin da Manzo Muhammad (S.A.W) ya yi wafati sai Ahlul-baiti (A.S) suka ga su ne suka fi cancanta da wannan lamari kuma halifanci ya na ga mazajen su ne banda wani daga quraishawa, kuma yayin da wasu jama’a daga sahabbai suke miqa jagoranci da biyayya ga Imam Ali (A.S) kuma suna ganin shi ne ya fi cancanta a kan wanin sa yayin da suka ga an kauce masa zuwa ga wanin sa sai suka qi yarda da hakan..." (Tarihin Ibn khaldon: J 3, shafi: 364).
Na biyu: Dakta Ahmad Amin ya ce: Farkon irin da ka shuka Shi’anci da shi su ne waxanda suka ga cewa bayan wafatin Annabi (S.A.W) Ahlul-baiti (A.S) su ne suka fi cancanta da halifancinsa fiye da wasunsu. (Fajarul islam: Shafi: 266)
Na uku: Dakta Hasan Ibrahim ya ce: Ba mamaki, a bisa haqiqa musulmi sun yi savani bayan wafatin Annabi (S.A.W) game da wanda zai yi halifanci bayansa, sai dai lamarin ya tuqe da jagorancin Abubakar wanda ya kai al’umma ta kasu gida biyu na jama’ar al’umma masu yawa da kuma ta Shi’anci (Tarihul islam: J 1, shafi: 371).
Na huxu: Ya’qubi ya ce: Ana ganin jama’ar da ta sava wa bai’ar Abubakar su ne xigo na farkon na Shi’anci, wanda suka fi shahara a cikin su, sun haxa da: Salman Farisi, da Abuzar Gifari, da Miqdad xan As’wad, da Abbas xan Abdul Muxallib (Tarihul Ya’qubi: J 2, shafi: 104).
Bisa bayanin masu sava wa da bai’ar halifancin Abubakar ne, Dakta Ahmad Mahmud Subhi ya ce: Abubuwan da suka haifar da wannan savani da suka sanya wasu barin bai’a ba zai yiwu a kafa dalili da su a kan cewa dukkaninsu Shi'a ba ne. Tayiwu abin da ya faxa ya kasance gaskiya, amma masu tarihi sun qarfafi cewa waxanda suka sava da bai’ar Abubakar cewa su Shi'a ne, kuma da sannu zamu yi nuni da hakan yayin bayanin game da hakan (Nazariyyatul imama shafi: 33).
Na biyar: Mustashriq Julad Tasihar ya ce: Shi’anci ya fara ne bayan wafatin Annabi (S.A.W) kuma kai-tsaye bayan lamarin Saqifa (Al’aqida wasshari’a: Shafi: 174).
b- Ra’yin da ya tafi a kan cewa Shi’anci ya fara ne lokacin Usman kuma waxanda suka tafi a kan hakan: Sun haxa da wasu malaman tarihi da marubuta daga cikinsu akwai Ibnu Hazam, da wasu jama’a da Yahaya Hashim Fargal ya faxe su a cikin littafinsa dalla-dalla (Awamilu wa ahdafu nash’ati ilmil kalam, j 1, shafi: 105).
c- Ra’ayin da yake ganin an kafa Shi’anci ne lokacin halifancin Imam Ali (A.S) kuma daga waxanda suka tafi a kan wannan ra'ayi akwai Nubkhati a littafinsa na "Firaqus Shi'a" (Firaqus Shi'a, shafi: 16), da Ibn Nadim a littafin "Alfihrast", yayin da ya ayyana lokacin faruwar Shi’anci da yaqin Basara da kuma abin da suka gaba ce ta, na lamuran da suka yi tasiri kai-tsaye wajen havakar jama’ar Shi'a da kafuwar su (Alfihrast Ibn Nadim, shafi: 175).
d- Ra’ayin da ya tafi a kan cewa Shi’anci ya bayyana ne lokacin da aka yi yaqin Xuff bisa savanin yadda hakan ya faru, wasu sun tafi a kan cewa dukkan abubuwan da suka faru kafin wannan yaqin ba su iya kai wa ga faruwar Shi’anci ba, amma ya faru ne lokacin da aka samu aukuwar yaqin Xuff, (wato Karbala). Yayin da wasu suka tafi a kan cewa Shi’anci kafin yaqin Xuff bai wuce lamarin gina ruhi ba (Assila bainat tasawwuf wat tashayyu’, shafi: 23), kamar sufanci da zuhudu da siffantuwa da kyawawan siffofi na halaye na gari, amma bayan yaqin Xuff sai ya samu motsi na siyasa da kafuwa cikin zukatan mutane, kuma ya samu faxaxa, kuma da yawa daga mustashriqun sun tafi a kan wannan ra'ayi ne, da kuma da yawa daga marubutan wannan zamani. Dakta Kamil Mustapha ya na cewa: Wannan samun ma’ana ta Shi’anci kamar yadda yake a yau, ta samu ne bayan kashe Imam Husain (A.S) yayin da ya kasance wani tsari na mazhaba ta musamman.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: