bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      22:12:54
Yayin da Dakta Abdul’aziz Adduri ya tafi a kan cewa Shi’anci ya samu tsarin siyasa ne bayan kashe Imam Ali (A.S), kuma wannan ya haxa har zuwa lokacin kashe Imam Husain (A.S), yayin da ya yi la’akari da wannan ci gaban lokutan da suka gabata ne (Muqaddima fi tarikhi sadril islam, shafi: 72).
Lambar Labari: 163


بسم الله الرحمان الرحيم
وصلي الله على محمدوءاله
Yayin da Dakta Abdul’aziz Adduri ya tafi a kan cewa Shi’anci ya samu tsarin siyasa ne bayan kashe Imam Ali (A.S), kuma wannan ya haxa har zuwa lokacin kashe Imam Husain (A.S), yayin da ya yi la’akari da wannan ci gaban lokutan da suka gabata ne (Muqaddima fi tarikhi sadril islam, shafi: 72).
Wannan shi ne ra’ayin Buruklman a cikin tarihin al’ummun musulmi yayin da yake cewa: A bisa gaskiya mutuwar shahada da Imam Husain (A.S) ya samu kuma ba ta da wani tasiri na siyasa kamar yadda yake rayawa- ta taka babbar rawa wajen samun ci gaban addini gun Shi'a rundunar Ali (A.S), wanda ya zama bayan haka ne mahaxar jayayyar dukkan Larabawa –kuwa wannan ba haka yake ba- kuma yau kabarin Husain (A.S) a Karbala ya na daga cikin mafi tsarkin wuri gun Shi'a, musamman Farisawa da ba su gushe ba suna ganin babban burin su ya na cikintattaruwa gun sa (Tarihisshu’ubul islamiyya: Shafi: 128).
Wannan ra'ayi na Buruklman haxa da cewa ya na da wata dasisa da ya qunsa haka nan ya sava wa mafi girman abin da masu faxin ra’ayoyi game da bayyanar Shi’anci sakamakon kashe Imam Husain (A.S) yayin da suka tafi a kan cewa an samukafuwar siyasar mazhabar Shi’anci bayan wannan waqi’a ne, yayin da shi Buruklman yake ganin babu wata haqiqanin gaskiya ta siyasa a cikin wannan waqi’a, lamarin da ya kasance musu ne ga abin da yake sananne qarara.
Kuma wasu mutane sun goya wa Buruklman baya a wannan ra'ayi kamar Yahaya Fargal a cikin littafin sa (Awamilu wa ahdafu nash’ati ilmil kalam, j 1, shafi: 106), da cewa wannan ra’ayoyi huxu da suke bayanin faruwar Shi’anci ba zasu iya tsayawa ba qyam gaban dalilin da yake rusa su, kuma ba ina nufin in gaugauta raddinsu ba, da sannu zan ambaci ra'ayi na biyar wanda da shi ne zai iya tabbatar da cewa waxannan ra’ayoyi suna dogara ne da abubuwan da suka faru waxanda suke bayanin cewa Shi’anci ya kafu ne sakamakon tasirantuwa da wasu abubuwan da suka faru waxanda waxannan ra’ayoyi suka dogara da shi a tarihin da suka kawo na bayyanar Shi’anci sai suka yi tsammanin an same shi a wannan lokacin, alhalin an same shi ne a tun farko. A yanzu lokaci ya yi da zamu kawo maka ra’ayoyin jama’ar Shi'a musamman masana daga cikin su, daga cikinsu akwai:
e- Ra’ayin Shi'a da wasun su na daga marubuta a wasu mazhabobin. Yayin da wasu suka tafi a kan cewa an samu Shi’anci ne lokacin Annabi (S.A.W) kuma Annabi (S.A.W) da kansa ne ya dasa irinsa ta hanyar hadisai da suka zo a harshen Annabi (S.A.W) kuma suka ba wa Ali (A.S) matsayi a wurare daban-daban da suka rauwaito, haxa da cewa akwai amintattu daga malaman Sunna da suka ruwaito kamar Suyuxi a ruwayar sa daga Ibn Asakir gun tafsirin ayoyin nan biyu ta shida da ta bakwai daga surar Bayyina da sanadinsa zuwa ga Jabir xan Abdullah da ya ce: Mun kasance gun Annabi (S.A.W) sai Ali (A.S) ya gaba to, sai Annabi (S.A.W) ya ce: "Na rantse da wanda raina take hannun sa wannan da shi’ar sa su ne masu rabauta ranar qiyama: Sai aka saukar da faxin Allah Maxaukaki "Haqiqa waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Kuma Ibn Udayyi ya karvo daga Ibn Abbas cewa ya ce: Yayin da aka saukar da faxin Allah Maxaukaki "Haqiqa waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Sai Annabi (S.A.W) ya ce da Imam Ali (A.S) kai ne da Shi'ar ka. Kuma Ibn Mardawihi ya karvo daga Imam Ali (A.S) cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin ba ka ji faxin Allah (S.W) ba cewa "Haqiqa waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". To kai ne da kai da shi’arka kuma alqawarin inda zan haxu da ku shi ne tafki, yayin da al’ummu zasu zo domin hisabi, to kai za a kira ku haskaka masu fararen alamomi(AdDurrul Mansur: J 6, shafi: 376), don haka ne ma Abu Hatim Arrazi ya tafi a kan cewa kalmar Shi’anci shi ne farkon suna da ya bayyana a cikin musulunci, kuma wannan laqabi ne da ake gaya wa huxu daga sahabbai da suka haxa da Abuzar da Ammar da Miqdad da Salman Farisi, kuma bayan yaqin Siffaini wannan laqabi ya shahara ga masu goyon bayan Imam Ali (A.S) (Raudanul janan, khunsari: Shafi: 88).
Waxannan hadisai da suka gabata waxanda Ibn Asakir da Ibn Udayyi da Ibn Mardawihi suka ruwaito, kuma bayanin Ahmad Mahmud Subhi ya biyo bayansu a littafin sa na "Nazariyyatul Imama"Yana cewa: Waxannan hadisai da suka zo a harshen Annabi (S.A.W) game da Imam Ali (A.S), ba sa nuna cewa akwai wata jama’a a lokacin Annabi (S.A.W) da tabayyana mai suna Shi'a kamar yadda dai Annabi (S.A.W) ya yi ishara da bayyanar khawarijawa da mariqawa kamar yada yake ce wa Imam Ali (A.S): Zaka yaqi Nakisin (A’isha su Xalha da Zubair) da Qasixin (Mu’awiya) da kuma Mariqin (Khawarijawa). Kuma bai nuna akwai su ba a matsayin wata jama’a wacce take da aqidu mabambanta ko wasu fikirori daban (Nazariyyatul imama: Shafi 31).

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: