bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      22:35:26
dan shu'umanci yana kasancewa cikin wani to yana cikin harshe* ku taskace harsunanku kamar yadda kuke taskace dukiyoyinku ku yi taka tsantsan da son ranku kamar yadda kuke taka tsantsan da makiyanku.
Lambar Labari: 165

Ta wata fuskar kuma imam ya inganta imamni cikin zukatan sahabbansa da ma'anarsa, hakan ya kasance ta hanyar fayyace siffofin mumini tabbas mumini shi ne wannan mutumin da ma'anar ubangijintaka take bayyana da surarta mai gamewa ga rayuwa, mumini ba shi ne wannan samfuri sallamamme cikin rayuwarsa ba wanda aka rasa hakan cikin iradarsa wanda makiya suke kwadayin cin amfanin karfinsa don biyan bukatunsu.

قال×: «إنّ الله فوّض إلى المؤمن أمره كلّه، ولم يفوّض إليه أن يكون ذليلا، أما تسمع الله تعالى يقول: (ولله العزة ولرسوله وللمؤمنين) فالمؤمن يكون عزيزاً ولا يكون ذليلا).

Imam (as) ya ce: tabbas Allah ya fawwala mumini baki dayan lamarinsa gareshi* bai fawala gareshi ya kasance kaskantacce ba* ashe baka ji fadin Alah madaukaki ba: izza ga Allah take da manzonsa da muminai, shi mumini yana kasancewa cikin izza bai kasancewa kaskantacce.
Sannan imam sadik (as) ya kara cewa:

ثم قال×: « المؤمن أعز من الجبل، والجبل يستقل منه بالمعاول، والمؤمن لا يستقلّ من دينه بشيء

Shi mumini yafi izza daga dutse* domin shi dutse ana cire shi daga mahallinsa ta hanyar amfani da diga* shi ko mumini bai ciruwa daga addininsa da wani abu.
Sannan imam ya karkata ya fuskanci zuciya ta wofinta don tsoran Allah- wanda shi ne ma'aunin kamala da karfin zuciyar mumini- ita zuciya cike take da tsoran Allah mai girma madaukaki ragowar gabban karfi na kaskanta gabansa misalin karfin sarki karfin dukiya da karfin mutumtaka, zuciyar da ba ta jin kiyayewar Allah tana kuma gafalar da kanta daga kiyayewarsa za ta kasance rarrauna fadaddiya duk yadda mai ita ya yi bakin kokarin nuna karfinta da girmama. Tabbas wannan nau'in na alaka mara kyawu tare da Allah yana tukewa zuwa ga girgiza zati da rikicewarta da gazawarta gaban kalubale da ke gangaro daga wadancan gabban karfi halittattu raunana gaban kudirar Allah da girmansa da fin karfinsa.

عن الهيثم بن واقد قال سمعت أبا عبدالله× يقول: «من خاف الله أخاف الله منه كل شيء ومن لم يخف الله أخافه الله من كلّ شيء»

Daga haisam ibn wakid ya ce: na ji baban Abdullah (as) yana cewa: duk wanda ya ji tsoran Allah Allah zai sanya komai ya dinga jin tsoransa* wanda duk bai ji tsoran Allah ba Allah zai tsorata shi da komai.
Kamar yadda imam sadik (as) ya gargadi shi'arsa daga yawan surutu ya umarce su da kame harshe, haka ma ya gargade su daga mika wuya ga son zuciya.

: «إن كان الشؤم في شيء فهو في اللسان، فاخزنوا السنتكم كما تخزنون أموالكم واحذروا أهواءكم كما تحذرون أعداءكم فليس أقتل للرجال من اتّباع الهوى وحصائد السنتهم»

Idan shu'umanci yana kasancewa cikin wani to yana cikin harshe* ku taskace harsunanku kamar yadda kuke taskace dukiyoyinku ku yi taka tsantsan da son ranku kamar yadda kuke taka tsantsan da makiyanku.

Kamar yadda imam (as) ya janyo hankulan shi'arsa zuwa ga watsi da jita jitan da abokan rigimamrsu ke fadi kan kishiyantar abokansu, tana iya dacewa ta zama daidai tana iya zama silar tuhumar kai, yana cewa:

 «من لم يبال ما قال وما قيل فيه، فهو شرك الشيطان، ومن لم يبال أن يراه الناس مسيئاً فهو شرك الشيطان».

Duk wanda bai damuwa da abin da yake fada da kuma abin da ake fadi kansa* to lallai shi abokin tarayyar shaidani ne* duk wanda bai damuwa da mutane su dinga ganinsa mai munanawa tabbas shi abokin tarayyar shaidani ne.

Uslubi na uku: gina al'umma ta gari
Ta yiwu wadanacan yunkurin guda biyu da suka gabata na kawo gyara da na ilimi su kasance masu shimfida hanya zuwa ga gina jama'a ta gari domin su tafi a aikace kan hanyar assasa tsarin zamantakewa cikin al'umma mai girma, hakika imam ya kasance yana fafutika domin karfafa sinadaran gina al'ummar musulmi gwargwadon abin da ya samu, imam bai samu dama da ikon yin juyin-juya hali ba da zai kwato mulki daga hannun lalatattun shugabanni mabarnata sakamakon rashin abubuwan da zasu hukunta aikata hakan, sai ya dogara da uslubin yakarsu ba kai tsaye ba domin gyara ginin da sarakunan zalunci suka rusa da yiwa mutane allurar dakewa gaban karkata da bata  gwargwadon iko a kan wannan sura ne imam sadik (as) ya motsa domin gina jama'a ta gari cikin babbar al'umma ita ce ainahin siyasa da uslubin da a'imma (as) suka ginu kai cikin yin ayyukan gina zamantakewar al'umma.
Hakika shahid Muhammad bakir hakim cikin littafinsa mai suna (daurul ahlul baiti fi bina'I mujtama'I salihi) ya yi bahasi filla-filla za muyi ishara zuwa ga abin da a'imma suka nufa zuwa garseshi daga fafutikarsu kan gina jama'a ta gari wacce ita ce za ta zamanto jama'a mumina mai wilaya mai nisanta daga ta'asirantuwa daga kalubalen tunani da karkacewa ta suluki wacce ta ke buge al'ummar musulmi, sannan daga cikin wadannan haduffa:

Alakar zamantakewa:

Imam sadik (as) yana da wata mahanga bayyananniya cikin gina alakokin zamantakewa don musulmi ya samu damar rayuwa cikin aminci ya kasance yana tasiri cikin inda yake rayuwa tare da dukkanin yanayi da shubuhohi kullallu wacce take kewaye da abokansa da yanayi kebantacce da kuma al'umma da yanayi mai gamewa.
Daga cikin wannan asasi da imam (as) ya yi kira zuwa gareshi wanda shi ne hanya tsasto tsarkaka:
1- yawaita abokai masu amfani:
 
قال×: (اكثروا من الاصدقاء في الدنيا فأنهم ينفعون في الدنيا والآخرة، اما في الدنيا فحوائج يقومون بها، وأما في الآخرة، فأن أهل جهنم قالوا ما لنا من شافعين ولا صديق حميم)

Imam (as) ya ce: ku yawaita abokai cikin duniya lallai su za su amfanar a duniya da lahira* amma cikin duniya zasu tashi cikin biyan bukatu* amma a lahira tabbas mutanen jahannama sun ce mu bamu da masu ceto bamu da aboki mai nuna soyayya.

وقال×: (استكثروا من الاخوان فأن لكل مؤمن شفاعة).

Imam (as) ya ce: ku yawaita `yan'uwa tabbas kowanne zai yi ceto.

وقال×: (التواصل بين الاخوان في الحضر التزاور، والتواصل في السفر المكاتبة)

Imam (as) ya ce: zumunci tsakanakanin `yan'uwa a halarce shi ne ziyartar juna, sannan zumunci cikin tafiya shi ne aikowa da juna wasika.

Daga cikin surar aikatau cikin wannan al'amari shi ne gaisawa da juna da rungumar juna.

فقال×: (تصافحوا فانها تذهب بالسخيمة).
Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: ku gaisa da junanku tabbas ita gaisawa da juna na tafiyar da gaba da kiyayya.

وقال×: (ان المؤمنين اذا اعتنقا غمرتهما الرحمة)

A wani wajen ya ce: lallai su muminai idan suka rungumi juna rahamar Allah tana lullube su.

2- larurar taimamkekeniya tsakanin muminai:

Cikin karfafa ga `yan'uwantaka ta gaskiya tsakanin muminai ya yinda yake cewa:
وفي ذلك تأكيد للاخوة الصادقة بين المؤمنين اذ قال×: (تقربوا الى الله تعالى بمواساة إخوانكم).

 ku nemi kusanci zuwa ga Allah madaukaki ta hanyar taimamkon `yan'uwanku.

وفي كلام له× الى بعض أصحابه: (وأن يعود صحيحهم مريضهم وليعد غنيهم على فقيرهم، وان يشهد جنازة ميتهم وان يتلاقوا في بيوتهم)

.Cikin wani zancensa (as) ga sashen sahabbansa: lallai mai lafiyarsu ya kaiwa mara lafiyarsu ziyara* mawadacin cikinsu ya ziyarci talakansu, ya halarci jana'izar mamacinsu* su dinga haduwa cikin gidajensu.

Don karfafa wannan dangantaka ta zamantakewa imam (as) ya yi gargadi daga wasu ayyuka da suke rushe wannan dangantaka akwai zolaya da jayayya da alfahari da makamantansu.
 
قال×: (إن أردت أن يصفو لك ودّ أخيك فلا تمازحنه ولا تمارينّه ولا تباهينّه)

Ya ce: idan kana son soyayyarka da tare da `dan'uwaka ta tace to kada ka dinga zolayarsa ka da kayi jayayya da shi ka da ka yi masa alfahari.

Kmar yadda ya yi gargadi daga zama tare da masu neman aibobi mutane da masu tsananta kiyayya da makiya da ire-irensu, imam (as) yana cewa:
    
 (من جالس لنا عائباً او مدح لنا قالياً أو واصل لنا قاطعاً أو قطع لنا واصلاً او والى لنا عدواً او عادى لنا ولياً فقد كفر بالذي أنزل السبع المثاني والقرآن العظيم)

Duk wanda ya zauna da mai neman aibobinmu ko kuma ya yabi mai tsananin kinmu ko kuma ya sadar da zumunci da wanda ya yanke zumuncinsa da mu ko kuma yanke zumunci da wanda yake sadar da zumunci da mu ko kuma ya so wanda yake kiyayya da mu ko kuma ya yi kiyayya da wanda yake son mu hakika ya kafircewa wanda ya saukar da saba'a masani da kur'ani mai girma.

Unwanai don gina akidu da tunani:
 
A wannna waje zamu sauko da nassoshi na imam sadik (as) wadanda suke yaye bangarorin himmatuwarsa cikin gina jama'a ta gari daga nan kuma karfafar ginin tunani da na akidu don al'umma da dukkanin shakali mafi fadi, imam (as) baiyi kasa a gwiwa ba bai gaza cikin karfafa aikin tarbiyyar jama'a ta gari don daukakata domin fuskantar kalubale don ya zamnto lamari bai rikice musu ba. Daga cikin daidaikun wannan al'amari akwai:

1- kwadaitarwa kan fahimtar addini:

Imam sadik (as) yana cewa:

 (لا يسع الناس حتى يسألوا ويتفقهوا ويعرفوا إمامهم، ويسعهم أن يأخذوا بما يقول وإنْ كان تقية)

Mutane ba su yalwatuwa su wadatu face sun yi tambaya sun san wanene imaminsu, zai wadacesu su karbi abin da yake fadi ko da kuwa ya kasance takiyya ne.

وقال×: (قال رسول الله|: طلب العلم فريضة على كل مسلم، ألا وأنّ الله يحب بغاة العلم)

Ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: neman ilimi farilla ne akan dukkanin musulmi, ku saurara tabbas Allah yana son masu neman ilimi.

Bisa cewa ilimin ya lazimtu da kyawawan halaye domin idan ya kasance ya wofinta daga kyawawan halaye ma'abocin ilimin zai sauya ya zama hatsari kan al'umma imam sadik (as) yana cewa:
 (طلبة العلم ثلاثة فاعرفوهم بأعيانهم وصفاتهم: صنف يطلبه للجهل والمراء وصنف يطلبه للاستطاعة والختل وصنف يطلبه للفقه والعقل)
Masu neman ilimi sinfi uku suke saboda haka ku san ainahinsu da siffofins: akwai sinfi da suke neman ilimin domin jahilici da jayayya* akwai sinfi da suke neman ilimi don samun iko da takama akwai sinfi da suke neman ilimi don neman fahimta da hankali.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: