bayyinaat

Published time: 13 ,July ,2018      22:39:32
imam (as) yana cewa: (أما علمت ان صلة الرحم تخفف الحساب). Ashe baka san cewa sadar da zumunci na saukaka hisabi ba.
Lambar Labari: 166
Na biyu gaggawa zuwa ga lazimtar tsoran Allah:

Imam sadik (as) yana cewa:

 (ليس منا ولا كرامة من كان في مصر فيه مائة الف او يزيدون وفيهم من هو أورع منه)

Baya daga cikin mu babu karamci ga wanda ya kasance cikin wani gari da yake da mutum dubu dari ko ma fiye da haka sannan ace acikin mutane akwai wanda ya fishi tsantseni.

3-kira zuwa ga siyasar tausasawacikin tattalin arziki da rayuwa:
Imam sadik (as) ya ce:

(أيّما أهل بيت أُعطوا حظهم من الرفق فقد وسّع الله عليهم في الرزق، والرفق في تقدير المعيشة خير من السعة في المال، والرفق لا يعجز عنه شيء، والتبذير لا يبقى معه شيء، ان الله عز وجل رفيق يحب الرفق).

Duk wasu ahlin gida da sukai kyautar rabonsu daga tausayi tabbas Allah ya yalwata kansu cikin arziki, tausayi cikin kaddara rayuwa shi yafi alheri daga yalwar dukiya.

Tadabburi cikin karshen al'amura:
 
قال الامام الصادق× لرجل: (أوصيك إذا أنت هممت بأمر فتدبّر عاقبته فأن يك رشداً فأمضه وإن يك غيّاً فانته عنه)

Imam sadik (as) ya cewa wani mutum: ina maka wasiyya idan ka himmatu kan wani ala'amari to ka lura ka kalli karshensa idan ya ksance shiriya ne to ka zartar da shi idan kuma ya zamanto bata to ka bar shi.

5- kwadaitarwa kan umarni da kyakkyawa da hani da mummuna:

قال الامام الصادق×: (الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر واجبان على من أمكنه ذلك ولم يخف على نفسه ولا على أصحابه)

Imam sadik(as) ya ce: umarni da kyakkyawa da hani da mummuna  wajibai ne guda biyu kan wanda ya samu damar yi bai kuma kasance yana tsoranma kansa ko abokansa ba.

Cikin sauke wannan farali an shardanta ilimi da adalci da tausasawa.

-Izza babu zilla da kaskantuwa: 6
قال الامام الصادق×: (ان الله فوّض الى المؤمن كل شيء إلا إذلال نفسه)
Imam sadik (as) ya ce: tabbas Allah ya fawwala komai ga mumini in banda kaskantar da kansa.

وقال×: (لا ينبغي للمؤمن ان يذل نفسه) قيل، كيف يذلّ نفسه؟ قال: (يتعرّض لما لا يطيق).

Imam (as) ya ce: bai kamata mumini ya kaskantar da kansa ba, aka ce masa ta yaya zai kaskantar da kansa? Sai ya ce: bijira ga abin da ba zai iya ba.

7-girmama alkawali:
قال×: (المسلمون عند شروطهم، إلا كل شرط خالف كتاب الله فلا يجوز)
Musulmai suna kan sharuddansu sai dai dukkanin sharadin da ya sabawa kur'ani bai halasta.

8-fuskanin aiki don neman arziki tare da abin da za a rayu a mutunce:

عن أبي عمرو الشيباني: رأيت أبا عبد الله× وبيده مسحاة وعليه إزار غليظ يعمل في حائط له والعرق يتصابُّ عن ظهره فقلت: جعلت فداك أعطني أكفك فقال لي: إني أحبُّ أن يتأذّى الرجل بحرّ الشمس في طلب المعيشة)

An karbo daga abu amru shaibani: nag a baban Abdullah (as) yana dauke da shebur din aikin gini yana sanye da kakkauran abin damara yana aiki cikin gona gomi na kwarara daga gadon bayansa sai nace: raina fansarka bani in dauke maka nauyin wannan aiki sai ya ce mini: lallai ni ina son in mutum na shan zafin rana cikin neman abin da zai rayu.

9- hakuri da iko kan gaba da gaba:

Haka nan imam ya koyar da sahabbansa hakuri da kuma shiri da yin tanadi don fuskantar bala'I hanyar shi'anci hanya ce mai wahala da `kaya babu sauki cikinta, duk lokacin aka ambaci bala'I wajensa sai imam (as) ya ce:
 
سئل رسول الله| من أشد الناس بلاء في الدنيا؟ فقال: النبيون ثم الأمثل فالأمثل، ويبتلى المؤمن بعدُ على قدر ايمانه وحسن أعماله فمن صحّ ايمانه وحسن عمله اشتد بلاؤه ومن سخف ايمانه وضعف عمله قل بلاؤه)

An tambayi manzon Allah (s.a.w) wadanne mutane ne sukafi tsananin fuskantar bala'i cikin duniya? Sai ya ce: annabawa sannan misalsalinsu* ana jarrabtar mumini da bala'i bisa gwargwadon imaninsa da kyawuntar ayyukansa duk wanda imaninsa ya inganta aikinsa ya kyawunta to bala'insa zai fi tsananta* duk wanda imaninsa ya raunana aikinsa ya yi rauni jarrabawarsa zata karanta.
وقال×: (إنّا لنصبر، وان شيعتنا لأصبر منّا)

Imam (as) ya ce: lallai mu muna hakuri lallai shi'armu sunfi mu hakuri.

Wannan riwaya tana bayyana kasantuwa shi'a suna yin hakuri kan abin da basu sani ba sabanin a'imma (as)
10- gargadi kan fifita kan cikin bugun kirji da jagoran tar al'umma:

قال الامام الصادق×: (من دعا الناس الى نفسه وفيهم من هو أعلم منه فهو مبتدع ضال)

Imam sadik (as) ya ce: duk wanda ya kira mutane zuwa ga kansa alhalin cikin wadannan mutane akwai wanda ya fi shi ilimi tabbas shi `dan bidi'a batacce.

11- tsara iyali:
Imam (as) ya kirga sadar da zumunci daga cikin kyawawan halayen zamantakewa da wannan sadarwar iyali ke tsayuwa wadanda sune tushen al'ummar musulmi da tsarinta na dokoki wanda bai da kwatankwaci cikin al'ummomin da ba musulmi ba awani wurin imam (as) yana cewa:
 
 (أما علمت ان صلة الرحم تخفف الحساب).
Ashe baka san cewa sadar da zumunci na saukaka hisabi ba.
Haka ma a wani fadin yana cewa:

 (خمسة لا يعطون شيئاً من الزكاة، الأب والأم والولد والزوجة والمملوك لأنهم عياله ولازمون له)

Mutane biyar ba a basu wani abu daga zakka, sune uwa da uba da `da da mata da bawa domin su iyalinsa ne wajibinsa ne.
Ciyar da wadannan mutane biyar farilla ne, wannan na bayyana matsayin iyali cikin gina al'umma mai girma.

12- karfafa igiyar `yan'uwantaka da abokantaka:

Babu banbanci cikin kasantuwa cikin iyali ko kuma cikin tafkin al'umma babba

. قال الامام الصادق×: (من حب الرجل دينه حبه لأخوانه).

Imam sadik (as) ya ce: daga cikin soyayyar mutum ga addininsa shi ne nuna soyayyarsa ga `yan'uwansa.

Imam (as) ya kasa `yan'uwa kashi uku:
Mai bada taimamko da jikinsa, mai bada taimamkon dukiyarsa, biyun su masu gasgatawa ne cikin `yan'uwantaka, na ukun shi ne wanda zai karbi guzuri daga hannunka ya nufe ka zuwa ga sashen dadi to kada ka kidaita wannan daga cikin wadanda zaka aminta da shi.
 
Matukar kulawa ga mace cikin aure da saki da gado bisa la'akari da ita rukunin iyali kafafunta tare da `dan'uwanta namiji:

قال الامام الصادق×: (اتقوا الله في الضعيفين: اليتيم والنساء).

Imam sadik (as) yana cewa kuji tsoran Allah cikin raunana guda biyu: maraya da mace.

وقال×: (البنات حسنات والبنون نعم، الحسنات يثاب عليها، والنعم مسؤول عنها).

Imam (as) ya ce: `ya`ya mata kyawawan ayyuka ne su kuma `ya`ya maza ni'imam ce, ana bada lada kan kyawawan ayyuka ana tambaya kan ni'imomi.

وقال×: (ان المرء يحتاج في منزله وعياله الى ثلاث خلال يتكلفها وإنْ لم يكن في طبعه ذلك: معاشرة جميلة، وسعة بتقدير، وغيرة بتحصّن).

Imam (as) lallai mutum yana bukatar halaye uku da zai dau nauyinsu ko da kuwa a dabi'arsa babu hakan: zamantakewa mai kyau, yalwatawa da kaddarawa, kishi tare da katangewa.
Imam (as) yana gabatar da ita kan waninta idan ta kasance ta gari cikin fadinsa:

 (الأنس في ثلاثة: الزوجة الموافقة، والولد البار، والصديق الصافي)

Debe haso yana cikin abubuwa uku: mace mai bda hadin kai da yarda, `da mai biyayya, aboki mai tace soyayya.

14-dawwama cikin yin addu'a:
Ita addu'a itace bargon ibada hakika ahlul baiti (as) sun koyar da musulmi da jama'a ta gari yawaita yin addu'a cikin jawabin imam (as) ga wasu mutane da suka kai masa kukan rashin amsa addu'arsu sai ya ce musu:

 (لأنكم تدعون من لا تعرفونه).
Saboda kuna kiran wanda baku sani ba.
Ita addu'a tasrkake zuciya ce kuma hanya ce zuwa mahaliccinta lokacin da ita addu'ar ta kasance tsarkakakkiya. Har sai da imam (as) ya kasance yana cewa:

 (ان الدعاء يرد القضاء وإن المؤمن ليذنب فيذهب بذنبه الرزق)

Tabbas addu'a tana tunkude kaddara lallai mumini yana aikata zunubi sai arziki ya tafi zunubinsa.

Natijoji da mukaraba:

1 ta farko:
Ta yaya zamu iya samar da jama’a ta gari cikin babbar al’umma bisa koyarwar imam sadik (as)
2- mukaraba ta biyu: tunkude ishkalin nesantar dandalin siyasa me yasa?
3 mukaraba ta uku: jagaban rukunai cikin harkar zamantakewa a wurin imam sadik (as)

1 mutum.
2 iyali da alakoki.
3 mace.
4 matsaya daga nizam din hukuma
5 sasannin ruhi
6 manzumar kimomin akhlak
7 alaka tsakankanin daidaiku.
8 alaka tsakanin bawa da ubangijinsa.
9 alaka tsakanin mutum da halitta
10 neman halaliya.

4  mukaraba ta hudu:
Gini kan layi hudu na karshe-karshe daga mukaraba ta uku mahangar addini na hadewa da ittifaki don bayanin sinadarai jigon al’umma na asasi da motsinta. Sune: mutum da dabi’ar kasa, da alakar da take tsakaninsu, kari zuwa nisa ko kuma sinadari na hudu wanda shi ne Allah ga al’umma masu imani da Allah da dayanta shi ko kuma biyewa son zuciya ya yinda take zama abin bautawa ga wanda suka biye mata.
(أرأيت من اتخذ إلهه هواه)
Ashe baka gani ba wanda ya riki son ransa ubangjinsa.
A cikin al’umma ta karshe, shi addini wata sunna ce daga sunnonin tarihin `dan adam wanda ke jagorantar matafiyar motsin `dan adam da tarihi.

5 mukaraba ta biyar: nassoshin da suka zo daga imam sadik (as) a fagen `dan adam da al’umma sun kwarara kan mahangar gina al’umma ma’abota tauhidi.
6 mukaraba ta shida.
Manufa ta tushe da asasi kan saukar da kur’ani shi ne: samar da canji cikin zamantakewa ta hanyar samar da wata ka’ida masu aiki da zasu samar da canjin karkashin koyarwar kur’ani, mutum shi ne gundarin da za samarwa canjin kuma shi ne maudu’in daidai lokacin ragowar tsari suke kallon wasu abubuwa kamar jari da jinsi da wasunsu.
Daga nan ne himmar imam sadik (as) ke bayyana da wannan unwani wanda shi ne `dan adam cikin al’umma
7- mukaraba ta bakwai,
Cikin al’ummar danniya da zalunci kungiyoyi shida suna bayyana:
1-azzalumai masu girman kai.
2-azzalumai raunana
3-tarin yuyuwu marasa tunani
4-masu inkarin zalunci a cikin kawukansu suna kame bakinsu.
5-sufanci kagagge.
6-raunana.

Al’ummar musulmi a wancan zamani sun kasance suna shan wahala karkashin zalunci da danniyar umayyawa da abbasiyawa, akrkashin hasken sunnonin tarihi cikin harkar al’ummomi sai misalsalin wadannan kungiyoyin shida su bayyana a fage, imam sadik (as) bai bar wata kungiya kadai dai ya yi ta’ammuli da su baki daya, bias tasowa daga taklifinsa da wilayarsa kan al’umma imam ya kasance yana nasiha ga masu mulki yana kawo gyara cikinsu gwargwadon yadda ya sawwaka daga damammaki kan janibin kungiyoyi shida  ma’ana kungiyar raunana wadanda sune maudu’in harkar zamantakewa da siyasa da kawo gyara kai hatta ilimi.
Dukkanin wadannan suna dacewa tare da motsin imam mai gamewa don gina jama’a ta gari.   



MULAHAZOZI
Marubucin bai kawao:
•    Unwanin rubutun wanda da shi ne za a auna rubutun.
•    Babu mukaddimar da za ta bayyana mana ina rubutun ya dosa.
•    Ya kawo abubuwa na tarihi amma bai kawo masdari dangane da sub a.
•    Ya kawo ruwayoyi masu yawa, kuma ya tarjama su amma bai kawo masdarorin da ya ciro ruwayoyin ba.
A karshe bai bayyana wacce natiya ya kai gareta a wannan rubu

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: