bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      00:17:47
Idan mukayi duba da yanayin yanda muke yin addu`oi zamu fahimci wasu mas`aloli da suka shafi ita kanta addu`ar ta bangarori mabanbanta.abinda nake so inyi nuni akanshi
Lambar Labari: 167
Da sunan Allah mai rahma mai jin qai tsira da aminci su qara tabbataa ga shuganmu Annabi Muhammadu (s.a.w.
            da iyalan gidansa tsarkaka da sahaabbansa zavavvu.

MANUFAR ADDINI SHINE RAYA ZUQATA:  Idan mukayi duba da yanayin yanda muke  yin addu`oi zamu fahimci wasu mas`aloli da suka shafi ita kanta addu`ar ta bangarori mabanbanta.abinda nake so inyi nuni akanshi,shine;yaya kamata muyi Addu`a,meye manufar Addu`a?lokuta da dama muna kasancewa masu yawan Addu`oi,amma muna kuskure a tsarin da Addu`a ya kamata ta kasance,da kuma yanda ya kamata mai Addu`a ya   kasance tsakaninsa da wanda yake nema a farfajiyarsa(Allah subhanahu wa ta`ala).
  Kafin mu bayyana manufar wannan gajeruwar muqalar,bari muyi tsokaci kan ma`anar ita kanta Addu`ar a taqaice.zamu iya cewa Addu`a a ma`anar harshe(lugga)itace;neman wani abu agurin wani.zai iya kasancewa neman abu a wajen tsaranka(Aboki),ko nema a gurin wanda ya fika,ko nema a gurin wand aka fi,(wanda a mafi yawancin lokuta ba kasafai ake amfani da ma`anar qarshe ba).Idan muka ambaci Addu`a muna nufin alqanta manufarmu da ma`ana ta biyu,wato neman wani abu a gurin wanda ya fika,wanda ta bangaren tarbiyyar Addini muna jingina batun izuwa ga neman buqatu a gurin mahaliccin kowa da komai,Allah(swt),shine makomar dukkanin mai buqata.
  Don haka abune mai matuqar mahimmanci mu lura sosai lokacin da zamu yi Addu`a da lokacin da muke yinta.Qololuwar manufar Addu`a shine samun kusanci gurin mahallicci da neman biyan buqatunmu.don haka ba zai zama mu riqi ibadar Addu`a kara zube ba,ya kamata ya kasance a lokacin da muke yin Addu`a mu karkatar da tunaninmu gaba daya izuwa ga abinda muke karantawa ko furtawa,koda kalama daya zata buqaci muyi ta maimaita ta sama da sau goma har ta shiga cikin jikinmu na baxini da cikin zuciyarmu,mu aikata hakan domin kaiwa ga sakamako mai kyau.Babu mahimmanci wajen yawan shafukan da ka karanta,abin buqata ba shine zahirin karatun Addu`a ko yawan shafukan da ka karanta ba.Addu`ar da ake buqata itace wadda take daga zuciyar mai karantawa,babu mahimmanci ga wadda take fitowa daga doron harshe ba tare da komawar zuciya zuwa ga Allah ba a lokacin da ake yinta.
   Muyi duba mana ga yanayinmu a lokutan sallolinmu,mun mayar da salla ta koma kamar motsa gavobinmu kawai,mun mayar da Azuminmu kamar hanyar rage qiba,mun mayar da aikin Hajji kamar yawon shaqatawa ko kasuwanci,duk sun  kasance kamar yanda muke Addu`oi.Alhali Addu`a itace ka roqi ubangijinka da zuciyarka kafin harshenka ya furta.Yazo a hadisi cewa:Addua itace qwaqwalwar ibada(bisa ma`anar hadisin),kamar misalin qwaqwalwa mutum da gangar jikinsa,babu wata qima ga jiki matuqar ba qwaqwalwa,idan ya zamanto ta kasance daskararriya to hakanan jiki ma zai zamz makamancinta.A irin wannan halin zamu rasa rayuwar Ruhi ingattacciya,ya zama akwai ruhin amma babu cikakkiyar alaqa,babu a cikin tunaninmu, babu a cikin gudanarwarmu ta yau da kullum,alhali Addini ya kamata ya zamo a ruhi kafin ya zamo a fikra(tunani),da gaskene cewa Addininmu shine siyasarmu da tattalin arziqinmu da zamantakewarmu,sai dai      shi Addini shine zuzzurfar alqar Dan adam da mahalccinsa wadda take tabbata ta hanyar ruhi wajen mu`amalarsa da wadancan ginshiqan (ukku)da muka ambata.Ba za a cimma manufa ba idan ya kasance wani Musulmi yana da fikra (tunani)amma ruhinsa bashi da alaqa mai inganci da mahaliccinsa.Qimar ayyukanmu shine gwargwadon abinda ya jivinta na daga rayuwar zamantakewarmu tare da  tunaninmu da zuciya kyakkyawa mai vuvugowa da Allah zuwa ga Allah.
  A cikin sallolinmu na dare ko Addu`oinmu ko sallolin da muke sallata ya kasance muna xan zubar da hawaye domin tsoron azabar mahliccimu saboda kura-kuranmu,wannan hawayen suna wanke zuqata,kuma sune mafi kyawun abun wanke zuqatan.Sabda haka ya zama wajibi musamman ga matasa su mahimmantar da kansu bangaren gyara ruhi wanda zai samar da kyakkyawar alaqa tsakaninsu da Allah,duk sadda suka zurfafa wajen neman kusanci da Allah zasu zamo musulmi abin alfahari da tinqaho,amma in suka riqi gundari dokokin musulunci ba tare da gyaran ruhi ba,ba abinda zaa samu face suna kawai.Saboda haka gwargwadon iko mu qoqarta wajen gyaran zuqatanmu,don mu kasance tare da Allah(a ma`ana)a rayuwar Duniya da Lahira domin samun dacewa ta har abada.
    Muna roqon Allah kasancewa cikin yardarsa albarkacin mafifitan bayinsa(a.s)a cikin haittu.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: