bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      00:42:31
KARYA FURE TAKE BA TA 'YA'YA; KUMA DA GASKIYA AKE KOSHI Wani makaryaci, ya sami kitsen dabba ya kai gida ya ajiye sai kullum idan zai fita daga gida sai ya shafa kitsen nan a labbanshi da kan gashin bakinshi, sai ya tafi majlisar masu arziki ...
Lambar Labari: 168
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. LABARIN WANI MAI WASA DA MACIJI
Wata rana lokacin hunturun sanyi dusar kankara na zuba a Bagadaza, sai wani mai wasa da maciji ya ga wani katon maciji a sandare a kan tsauni, duk ya matukar tsorata da ganin wannan maciji, amma duk da haka sai ya yanke shawarar dauko shi domin ya yi wasa da shi a kasuwa domin ya sami kudi kuma domin ya birge mutane tunda za su ce ya yi bajinta.
Dan haka sai ya dauko shi da kyar ya tawo da shi kasuwar Bagadaza ta Iraki. Ya rika cewa da kyar ya samu ya kama wannan maciji wato ya sha matukar wahala kafin ya iya kama shi. Duk mutane sun taru kowa ya na tsammanin matacce ne miciji saboda a sandare yake. Saidai kuwa ba haka bane domin kuwa macijin nan yana da rai kawai tsananin sanyi ne da dusar kankara su ka sa sandare ba ya iya motsi.
Mutumin nan ya kawo macijin nan kusa da wani rafi da ke bakin kasuwa, mutane kuwa suka fara taru wa, ya ci gaba da jinkirta wa saboda jama’a su kara yawa ko ya samu kudi da yawa. Macijin yana kunshe cikin garara daure da wata igiya mai kwarin gaske. Ana nan sai gari ya fara yin dumi rana ta fara yin zafi, sai maciji ya fara maro wa wato ya fara dawo wa hayyacinsa. Sai aka ga ya fara motsi, sai mutane suka fara tsorata, sai suka fara gudu, macijin nan ya tsinka igiyar nan ya fito daga cikin gararar ya fara kai wa mutane hari. Mutane da dama sun mutu sakamakon gudun kwatar rai an tattake su. Mai wasa da macijin nan shima ya razana kuma ya yi nadama da wannan aiki nashi. Kafin kace me sai macijin nan ya yi lauma guda da mai wasan nan ya hadiye shi kawai. Sannan kuma sai ya nannade bishiya ta yadda zai karairaya kasusuwan mutumin da ke cikinsa.
To masu karatu mu sani cewa sha’awarmu kamar manyan macizai irin wannan take, idan ta samu dama, wato idan muna biye mata muna samar da mukaddimar da za ta motsa ta; to haka za ta yunkuro ta lakwame mu.
Kamar yadda Ma'aikin Allah (Sallallahu alaihi wa Alihi wa sallam) yake cewa: Shaidan ya ce, 'na halakar dasu ta hanyar yin sabo su kuma sun halaka ni ta hanyar tuba da neman gafara, da na ga haka sai na halaka su ta hanyar sha'awarsu, sai suka yi tunanin suna kan shiriya sai ya kasance ba su nemi gafara ba'. (al-Targhib wa al-Tarhib, mujalladi na 1, shafi na 87, H 131).

2. KARYA FURE TAKE BA TA 'YA'YA; KUMA DA GASKIYA AKE KOSHI
Wani makaryaci, ya sami kitsen dabba ya kai gida ya ajiye sai kullum idan zai fita daga gida sai ya shafa kitsen nan a labbanshi da kan gashin bakinshi, sai ya tafi majlisar masu arziki ya zauna ya na muzurai da idanu wai a zaman shima mai kudi ne. sai ya rika shafa gashin bakinshi dan ya ankarar da su cewa ya ci abinci mai rai da lafiya kafin ya fito daga gida.
Alhali kuma cikinshi babu komai sai ruwa ya na ta kugin yunwa. -'Allah wadaran makaryaci kun ga da bai cuci kanshi ya yi karya ba, da mai yiwu wa ne a sami wani daga mazauna majlisar ya taimaka mashi da abin da zai yi ya ci da mu, gashinan karyarshi sai azabtar damu take yi, to amma da sannu Allah Zai tona asirin makaryaci'! matarshi tace. ta ci gaba da cewa 'Ya Allah Ka cire wannan gashin baki ko bayinKa masu tausayi sa dube mu'.
Allah Ma ji rokon bawa, Sai adu'ar matar nan ta karbu, sai wata rana wata kyanwa ta zo ta dauke kitsen nan, mutan gida su ka bi ta amma ina! kyanwar nan tuni ta gudu da shi. Sai dan mutumin nan ya shiga damuwa saboda tsoron fuskantar fushin mahaifinsa, dan haka sai ya ruga a guje zuwa majlisar uban, ya same shi cikin abokai ana ta nishadi, cikin razani yace Baba baba! kyanwa ta dauke kitsen nan naka da kake shafa wa a baki kullum da safe idan za ka fito! kuma na yi kokari na karbe amma na kasa.
Ai kuwa sai kowa a majlisar nan ya kece da dariya, daga sannan kuma sai su ka ji tausayin mutumin sai su ka ba shi abinci kuma su ka sama mashi aiki. Daga sannan mutumin nan ya fahimci cewa lallai karya ba abin da za ta iya yi mashi sai dai yunwa; gaskiya ita ce ke cika ciki.
To masu karatu wannan kadan kenan daga illar karya, amma lallai karya tana da illoli masu yawan gaske.
Ma'aikin Allah (sallallahu alihi wa Alihi wa sallam) yana cewa: idan bawa ya yi karya, to Mala'iku suna nisanta kan su daga shi tsawon mil guda saboda warin mummunan abin da ya yi. (Sharh Nahj al-Balagha li ibn Abi al-hadid, mujalladi na 6, shafi na 357).
sannan kuma ya kuma cewa: "karya kofa ce daga cikin kofofin munafunci" (Kanz al-Ummal, H 8212).

3. SIRRIN ZAMAN DUNIYA DUBE GA MA'ANA
A Indiya akwai wata bishiya wadda duk wanda ya ci daga 'ya'yanta to ba zai taba tsufa ko mutuwa ba. Da wani sarki ya ji wannan magana sai ya kamu da son 'ya'yan wannan bishiya, dan haka sai ya tashi daya daga cikin dogaranshi ya tura shi Indiya domin ya nemo mashi wannan itaciya kuma ya zo mashi da 'ya'yanta.
Wannan dogari ya dau tsawon shekaru yana ta binciken wannan bishiya a kasar Indiya. Ya je wannan gari ya je waccan tsibiri da haka har ya karade ko'ina a kasar Indiya amma babu labarin wannan bishiya. Idan ya tambayi mutane ta hanyar sifanta musu bishiyar, sai su rika yi mashi dariya da isgili, wasu ma sai su ce dashi 'lallai wannan mutum masani ne kai saboda akwai sirri a cikin wannan nema naka', dan haka sai su dada kada shi wani gurin ta hanyar kwatancen karya. sai ya kasance dai abin da zai ji wannan mutumi daban yake da abin da wani zai gaya mashi dangane da abin da yake nema.
Shi kuma sarki ta nashi bangare sai kara turo wa dogarin nan kudi da duk abin bukatuwa yake yi, shi kuma shekara da shekaru yana ta nema. bayan tsawon lokaci da matsananciyar wahala sai ya yanke kauna, dan haka sai ya juyo zuwa kasarshi, a hanyarshi ta dawowa sai kuka yake yi cikin karyayyar zuciya, sai ya iso wani gari wadda yake akwai wani malami masani a garin. sai ya tafi gurin malamin yana kuka ya nemi taimako. Sai malamin ya tambaye shi:.... to masu karatu ku biyo mu a fitowa ta gaba wato kashi na shida domin karashen wannan labari mai dadi kuma mai dauke da darsi gwaggwaba.

To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na biyar  a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na shida’.

Hassan Adamu



Littattafan da aka duba sune:
1. al-Kur'ani mai tsarki
2. Sharh Nahj al-Balagah
3. al-Targhib wa al-Tarhib
4. Kanz al-Ummal
5. Labaran Masnavi maulavi

 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: