bayyinaat

Published time: 25 ,January ,2017      11:36:04
Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa. Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa: "Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa.
Lambar Labari: 17
Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa.
Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa:
"Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa1.
Lalle babban nauyin da ke kan mutum dangane da kan kansa shi ne ya kiyaye abin da zai zubar masa da mutumcinsa cikin al'ummar da yake raye a ciki. Don kuwa ayyukansa suna nan a kan idanuwan al'umman da yake tare da su, kada ya aikata wani abin da zai zubar masa da mutumcinsa ta yadda shi ma da kansa zai yi dan da-na-sanin wannan aiki.
Kamar yadda hanyoyin girmama zatin dan'Adam da kuma samar da daukaka ga mutumcinsa suke da yawa, haka ma hanyoyin ha'intar kai da kuma zubar da mutumci suke da yawa....
Misali, karya da ta'addanci a kan al'umma, ya kan haifar da wulakantar da kai, haka ma aikata muggan ayyukan da suka saba wa dabi'u na kwarai, yarda da wulakanci ko don saboda neman kudi, jin dadi ko matsayi, duk hakan suna haifar da wulakanci, munafunci, tsoro.....da dai sauransu.
 Haka nan kuma jin kaskanci da kuma sanya wa zuciya tunanin gajiyawa ta rashin iya aikata wani aiki, hada kai cikin aikin alheri da kuma hidima ga al'umma, duk hakan sukan kashe zuciyar mai yin su. 
Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta dukkan 'yan'Adam da karfi da kuma iyawa, don haka ya rage musu ne kawai su yi amfani da su wajen cimma manufarsu ta rayuwa. Don haka ba ya halalta gare su da su yi wasa da karfi da ikon da Allah Ya ba su..... 
Hakika Allah Madaukakin Sarki ba Ya haramta wa bayinSa ni'imominsa....wasu suna da karfin fahimtar ilimin magani, wasu kuwa ilimin yare, wasu kuma karfin kirkiro abubuwa suke da shi. Sannan wasu kuma karfin kasuwanci suke da shi, wasu kuma na ayyukan hannu suke da shi, wasu kuma na iya gudanar da mulki suke da shi, sannan wasu kuma karfin siyasa da ayyukan soji suke da shi....da dai sauransu. 
 Haka lamarin yake, don kuwa dan'Adam yakan gano iko da karfin da Allah Ya yi masa ne ta hanyar gwaji, don haka kada mutum ya wulakantar da abin da Allah Ya arzurta shi na daga karfi da kuma iko. 
Sau da dama mutane sukan wofantar da kwarewa da kuma karfin tunani da kuma na aiki da Allah Ya ba su saboda yanke kauna da kuma jin gazawa. Ta hakan sai ka ga sun lalata karfin da suke da shi da kuma hana kansu hakkin da ya 
 dace da ita da kuma hana ta damar ci gaba da kuma samun nasara. 
 Lalle babu shakka, yarda da kai, buri da kuma kokari sukan karfafa rai da kuma ba ta dukkan abin da take bukata wajen ci gaba da kuma gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace. Don kuwa dogaro ga Allah da kuma yarda da kai, mabudi ne na aiki da kuma cimma nasara a rayuwa. 
 Dan'Adam Da Al'ummarsa
 Al'umma, adadi ne na wasu mutane ko kuma zuriya wadanda suke da alakoki daban-daban a tsakanin junansu, kamar alaka ta akida ko kuma ta kusanci, ko kuma suna da manufa iri guda, ko kuma alaka ta tarihi da dai sauransu. 
 Kowane mutum yakan ji kusanci ko kuma jinginuwa ga zuriyarsa ko kuma al'ummar da ya fito daga cikinta, hakan kuwa don shi wani sashi ne na wannan zuriya ko kuma al'umma.... 
 Mutum da al'ummarsa sukan yi musanyan amfanoni da suke samu a tsakaninsu. Haka nan ma ta hanyar al'umman da yake rayuwa a cikinta yakan iya tabbatar da hanyar rayuwarsa, dabi'u da kuma tunaninsa..... 
 Lalle ba makawa dan'Adam yana da manufofi da yanayi masu cin gashin kansu, kamar yadda al'umma ma take da tata manufofi da yanayi masu cin gashin kansu. A lokuta da dama akan sami rashin jituwa tsakanin manufofin mutum da na al'ummarsa; don haka ne dokokin mutane da na Ubangiji suka ba da muhimmanci wajen tsara irin wadannan alakoki da kuma magance irin wadannan karo da juna da ake samu tsakanin manufofin guda biyu: na mutum da na al'umma.... 
 Koyarwar addinin Musulunci ta ba da muhim-mancin gaske wajen kyautata rayuwar mutum da ta al'umma; don kiyaye hakkokin wajibi na dan'-Adam, kamar yadda kuma ilmummukan kyawawan dabi'u da na zamantakewa suka ba da muhimmanci wajen gyara rayuwar mutum da ta al'umma, da kuma tabbatar da su  bisa asasin kyawawan dabi'u da kuma 'yantaccen shu'uri.....  Ko da yake wasu daga cikin mutane sun fi damuwa da tabbatar da manufofin  kansu, ba tare da la'akari da manufofi da matsalolin sauran mutane ba....  Misali, dan kasuwan da ke boye abinci da kuma masu sanya kayayyaki su yi  tsada, ba sa wani tunani in ban da yadda za su sami riba mai yawa. Ba sa  tunanin irin halin da fakirai marasa abin hannu za su shiga saboda tsadar  kayayyakin bukatun yau da kullum, su dai babban burinsu shi ne samun riba.... 
 Haka nan mabukaci, ba ya tunanin kome face yadda zai biya wannan bukata ta sa ba tare da tunanin bukatun sauran mutane ba. A wasu lokuta, hakan kuwa yakan sabbaba wa mutane matsaloli masu yawan gaske..... Haka nan ma mutumin da yake da wata manufa ta siyasa, ba ya barci har sai  ya cimma wannan manufa ta sa, ko kuma isa ga wani matsayi na siyasa da yake bukata. To amma idan har ya samu biyan wannan bukata, sai ka ga ba abin da ya dame shi na daga irin matsaloli da wahalhalun da sauran mutane za su shiga na rayuwa da kuma siyasa..... Haka kuma manomin da ya mallaki wata gona, ba ya hada kai da sauran manoma wajen samar da ruwan da za su yi amfani da shi a gonakin nasu matukar dai  gonarsa ta samu ruwan. 
 Irin wadannan mutane ba sa dubin lamurra da kuma matsaloli face in suna da manufa da maslaha a cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi bayani kan wannan matsala ta zamantakewa mai matukar muhimmanci, da kuma kan wannan son kai wanda yake matukar cutar da maslahohin al'umma. Inda yake ce wa: 
 "Babu wanda zai yi imani daga cikinku (musulmai) har sai ya so wa 
 dan'uwansa abin da yake so wa kansa na alheri2.
 Ta haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya hada tsakanin tunani kan maslahohin al'umma da kuma fita daga son kai na mutum guda. Don mutum ma'abucin son kai wanda ba ya tunanin maslahohin al'umma, ba mumini ne na gaskiya ba. 
 Kana kuma duk wanda ba ya tunanin maslahar sauran mutane, to babu wanda zai yi tunanin maslaharsa....to hakan kuwa zai kasance babbar kafar ungulu ga hadin kan al'umma da kuma ci gabanta. 
 Matukar dai ingantaccen shu'urin taimakekke-niya bai tabbata ga mutum da al'umma ba, kana kuma matukar babu wasu dokokin da za su kiyaye maslahohin mutum da na al'umma.... to ba makawa al'umma za su zamanto cikin rashin tsari da son zuciya, kana kuma da yawa daga cikin mutane za su kasance cikin wahalhalu. Daga nan kuma sai masu karfi su samu daman cutar da marasa karfi da kuma takura masu rayuwa.
Hakika shu'urin taimakekkeniya da kuma na kyawawan dabi'u da suke tare da mu, bugu da kari kan ka'idoji na Ubangiji madaukaka, suna kiranmu zuwa ga kiyaye maslahohin al'umma, kamar yadda kuma suke kiranmu zuwa ga kula da maslahohin da suka kebanta gare mu. Kuma a lokuta da dama maslahohin mutum guda sukan cutar da maslahohin al'umma, don haka ya zama wajibi mu nesance su. 
 A matsayin misali, lalatawa da kuma kara kudi a kan takardun kudi (rasidin kudi) yakan samar da makudan kudade ga masu wannan mummunan aiki, sai dai kuma hakan yakan haifar da mummunan gibi ga tattalin arzikin al'umma. To don haka ne ma dokokin Musulunci suka haramta wannan aiki da kuma hukumta masu yin sa. 
 To amma cikin ayyukan tsarkakakkun mutane muna iya ganin daidaituwa kan maslahar mutum shi kadai da kuma ta al'umma.
 Daga cikin irin wadannan kyawawan ayyuka shi ne abin da aka ruwaito daga Shugaban musulmi, Abu Abdullah, Ja'afar bin Muhammad al-Sadik (a.s.). An ruwaito daya daga cikin sahabbansa (sunansa Mu'attab) wanda shi ne mai kula da harkokin cikin gidansa yana cewa: "Wata rana Abu Abdullah ya ce min, a lokacin kuwa farashin kayayyaki ya tashi a garin Madina,: ya ya yawan abincin da muke da shi?, sai na ce masa: muna da abin da zai ishe mu na tsawon watanni. Sai ya ce: Fitar da shi ka sayar wa mutane, sai na ce masa: babu abinci a garin Madina fa. Sai ya ce: ka sayar dai, to lokacin da na sayar, sai ya ce min: je ka dinga saya tare da mutane rana-rana. 
 Sai Imam Sadik ya ce: Ya Mu'attab, ka sanya abinci iyalaina ya zamanto rabi sha'iri rabin kuwa alkama, hakika Allah Ya san cewa ina da karfin ciyar da iyalaina da alkama, to amma ina son Allah Ya gan ni ina kyautata rayuwa gwargwadon bukatata3() ". 
 Wannan kissa tana nuna mana irin yadda Musulunci yake ba da muhimmanci a aikace ga al'amurran da suka shafi al'umma. 
 Don Imam Sadik (a.s.) ya ki yarda ya ajiye abincin da zai ci na watanni ga iyalinsa, a daidai lokacin da sauran al'umma suke cikin rashi da kuma kuncin abin da za su ci na rana guda. Kana kuma ya aikata hakan ne don wanda yake da karfin sayan abinci da yawa ya tara a gidansa ya nesance yin hakan don a samu kayayyakin abincin a kasuwa da yawa, ta yadda kudinsu za su sauko kasa kuma marasa karfi su sami daman saya. 
 A nan za mu ga ce wa Imam Sadik (a.s.), kamar yadda ya ba da muhimmanci ga al'amarin al'umma, to haka ma a bangare guda ya bai wa lamarin kula da iyalansa nasa muhimmancin shi ma. To wannan shi ne cikakken imani na gaskiya. 
 A nan yana da kyau a fahimci cewa, abu mai wahalar gaske ga mutumin da ya cutar da al'umma shi ma ya tsira daga zafin wannan cutarwa, don kuwa a dabi'ance mutum yana so ya rayu cikin al'umma wacce take cikakkiya wacce ta tsira daga dukkan cutarwa. To don haka matukar dai al'umma ba su tsira daga cutarwa ba, shi ma ba zai tsira ba, don kuwa shi ma cikin wannan al'umma yake raye. 
1 Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 3 / (al-Zilla(
 2 - Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 1 / (Hakikat al-Imam), shafi na 395.
 3 Al-Kafi na Kulaini / juzu'i na 5/ shafi na 166, Darul Kutub 
 al-Islamiyya.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: