bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      00:59:58
Saboda haka batu akan sha’anin Imam Mahadi (a.s) ba wai batune da ya kevanta da ‘yan shi’a kawai ba, baki xayan Mazhabobin musulunci sun yadda dashi harma da sauran addinai sunyi Imani da wannan batun kuma suna sauraron wanda zaiyi wannan ceton a qarshen zamani
Lambar Labari: 170
                                   

                           MAHADI A SAURAN ADDINANAI
      Aqida akan bayyanar wanda zai ceci duniyar nan daga zaluncin da ya cikata aqarshen zamani, aqida ce ta duniya data haxa dukkanin addinan da suka zo daga sama, kuma a littattafai masu tsarki anyi alkawarin hakan, misali littattafan indiyawa dana zartush anyi bushara da zuwan mai ceto a qarshen zamani. Tabbas kowace al’umma da irin sunan da take kiran wanda zai bayyana don ceton duniya da shi da kuma irin savanin dake akwai, amma a asalin bayyanar mai ceto xin babu wani savani akan hakan.
   Hakama a vangarorin mazhabobi daban-daban na musulunci akwai kwatankwacin wannan akida xin ta bayyanar mai ceto, daga wasu ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w) zai cika qasa da adalci bayan ta cika da zalunci, wannan mas’alar gaba xaya tsakanin musulmai anyi musharaka.Bugu da kari kuma Manyan malaman ahlussunnah suma sun ruwaito hadisai akan batun Imam Mahadi (a.s), sun rubuta littattafai mustaqillai akan batun Imam Mahadi (a.j) sannan harma sun amsa shubuhuhi akan wannan batun, akwai wata ruwaya daga Sunan na abi Dawud daga Manzon Allah (s.a.w) da aka ruwaito:   لولم يبق من الدنيا الا يوم لطوّل الله ذلك اليوم حتّى يبعث رجلا من أهل بيتى يملأ الارض قسطا وعدلا كما ملئت ظلما وجورا))             
    {{ Da Duniya zata rage saura kwana xaya ta kare da Ubangiji ya tsawaita wannan ranar har sai an aiko wani mutum daga Iyalen gidana wanda zai cika qasa da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da ja’irci}}(1) .
     Saboda haka batu akan sha’anin  Imam Mahadi (a.s) ba wai batune da ya kevanta da ‘yan shi’a kawai ba, baki xayan Mazhabobin musulunci sun yadda dashi harma da sauran addinai sunyi Imani da wannan batun kuma suna sauraron wanda zaiyi wannan ceton a qarshen zamani.
                                GAIBAR IMAM ZAMAN (A.J)
      Xaya daga cikin abu mafi mahimmanci akan zancen Imam Mahadi (a.s) shine batu akan gaibarsa. Manzon Allah (s.a.w) da Imaman Shi’a goma sha biyu ko wanne lokaci suna magana akan wannan batun, sannan suna ishara akan batun gaibarsa da kuma ‘yan shi’arsu koda yaushe suna shiri akan zuwansa. A nan zamu kalli wasu batutuwa ko kuma mu ce wasu tambayoyi da kan iya bijirowa akan batun gaibar Imam Mahadi (a.s).
    Na farko: Gaibar Imam Zaman (a.j) wace ma’ana take da shi?
   Na biyu: Meye dalilin yin Gaibar tasa? Na uku: Imam Zaman ya zaiyi aikinsa alhali yana cikin Gaiba?
        MA’ANAR GAIBA:
    Gaiba tana nufin voya daga gani, wanda yayi gaiba shine wanda ya voya daga ganin mutane wato a zahiri ba’a ganinsa. A kuma Isxihahi akan batun gaibar Mahadi da muke magana akai ba wai yana nufin Imam Mahadi (a.s) babu shi bane ko kuma ba a haife shi ba kamar yadda wasu suke tsammani abin ba haka yake ba, abin dai sani akwai shine, shi yana nan sai dai ganinshi ne ba a yi. Idan muka kula da ruwayoyin da suka zo daga Imaman tsira akan batun Imam Mahadi (a.s) zamu iya cewa gani da ma’ar gamewa ce daga shi.
   Boyan jiki: Ma’ana wannan gani ne daga Imam Mahadi (a.s) da jiki irin namu ( maddi) a tsakanin mutane yake rayuwa; sai Allah maxaukakin sarki ya xauke ganin daga idanuwan mutane ta yanda bazasu iya ganin shi ba.
                     DALILAN GAIBAR IMAMI ZAMAN (A.S)
      Tambayar da zata iya bijirowa a nan itace wane daliline yasa Imam xin gaiba? Miyasa Imam xin ba zai zama a filiba kamar sauran Imamai da sukayi rayuwa tsakanin mutane kuma suka shiryar da mutane? amsa wannan tambaya ba abune mai sauki ba duk da dai ‘yan shi’a suna cewa wannan xaya daga cikin sirrin Ubangiji ne, cewar ba wanda yasan haqiqanin lokacin bayyanarsa sai Allah maxaukakin sarki. Amma a yanzu zamu kawu wasu daga cikin ruwayoyin da suka kawu dalilan gaibar Imam Mahadi (a.s).
 Na farko: Tsare Imam din: Idan muka dubi yanda Hukumar banu Abbas kusa rayuwar Imam Kazim (a.s) a  cikin mafi wahalar yanayi ta yanda ba wanda zai iya yayi mashi sallama kai koda ma ishara ta sallama abin ya gagara, a wannan yanayin  rayuwar ‘yan shi’a ta shiga wani yayini ta yadda hukuma tasa musu ido sosai a duk wani mutsi da zasuyi.
    Ubangiji yasa shigar Imam Mahadi (a.s.) gaiba ne domin kare Imam xin daga sharrin miyagu azzalumai saboda shine qarshen hujjar Allah a bayan qasa, kuma babu wani abinda zaiyi saura matuqar hujjar Allah ta qare a bayan qasa . hakika akwai kwatankwacin wannan gaiba xin data faru kafin gaibar Imam (a.s) misalin shigar Manzon Allah (s.a.w) kogo lokacin hijira daga Makka zuwa Madina da kuma gaibar Annabi Isa (a.s), akan wannan zamuyi ishara da maganar  Imam Baqir (a.s) inda yake cewa:
اذ قام القائم تلا هذه الاية:  ففررت منكم لمّا خفتكم فوهب لى بى حكما وجعلنى من المرسلين  
     (( Lokacin da Imam Mahadi zai bayyana zai karanta wannan ayar: Na gudu ne daga gareku saboda inajin tsoronku, har zuwa lokacin da Ubangijina ya bani Hukunci kuma ya sani daga cikin waxanda ya aiko))(2) .
       Na biyu: saboda a jarraba mutane: Xaya daga cikin sunnunin Ubangiji akwai jarraba mutane ta yadda kuwanne daga cikin su zai samu dacewa, kuma gaibar Imam Mahadi (a.s) wasu abubuwa ne wanxanda mutum zai iya samun tarbiya da ita. Tabbas tunda tarbiya tana da irin nata matsalolin, amma akan imanin xai xai ko zamu qarfafa mu kai ga babbar martaba shima akan wannan batun Imam Baqir (a.s) ya ce:     
هيهات هيهات! لا يكون فرجنا حتّى تغربلوا: ثم تغربلوا:حتّى يذهب الكدر ويبقى الصّفو       
    Haihata; Haihata! farajinmu ba zai zo ba, har sai lokacin da  kuka bar tatsuniya, sannan kuka bar tastuniyoyi; sannan kuka bar tatsuniya; har ya zuwa lokacin da ba zai cutu ba kuma ya kubuta daga kaskanci ya zama ba abinda yayi saura. Tabbas waxanda zasuci wannan jarabawar sunada matsayi babba a wurin Allah maxaukakin sarki.
     Manzon Allah (s.a.w) yayi bayani akan waxannan masu kokari akan hanyar Ubangiji inda ya ce:
يا علي!أعجب الناس ايمانا وأعظمهم يقينا قوم يكونون فى اخر الزّمان : لم يلحقوا النبي وحجب عنهم الحجة فامنوا بسواد على بياض........:
   (( Ya Ali! Mamakin Imani da girman yakinin mutanan da zasu kasance qarshen zamani; basu riski Annabi ba, kuma Imaminsu yana gaiba, sai sukayi Imani da abinda aka rubuta da tawada a farar takarda))(3) .
     Akwai ruwayoyi da daman gaske akan wannan batu na gaibar Imam Mahadi (a.s) sai dai a nan zamu taqaita ne saboda yanayin rubutun namu yanzu zamu je kan natija da kuma fa’idar gaibar Imam Zaman (a.j).
       Xaya daga cikin dalilan da yasa Imam Mahadi (a.s) gaiba akwai tarbiyar mutune xai xai ku ta yanda wasu bazasuyi amfani dasu ba wajen cimma wasu manufofinsu akan shi ba. Imam Aliyu bn Abi Xalib yana cewa: ku saurara! Ku sani tabbas kasa ba zata wufinta ba face da hujjar Allah a bayanta, amma saboda dalilin yawan  zaluncin mutane Allah ya haramtawa hujjarsa bayyana. Wannan yana xaya daga cikin natijar ayyukan mutane da suke aikatawa a bayan qasa.
   اذا غضب الله تبارك وتعالى على خلقه نجّانا عن ججوارهم . Idan Allah madaukakin sarki yayi fushi da bayinshi sai dauke ganinmu daga garesu))(4) .
   Saboda haka gaibar Imam Zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya, natijace ta munanan ayyukan mutane.
 Zamuci gaba a kashi na uku akan batun sauraron Imam Mahadi (a.s).
Aliyu Abdullahi Yusuf: Whatsapp, Telegram, Instagram, da sauran Media Number: +2348037493872.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: