bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      01:05:17
Xaya daga mafi muhimmancin abu akan batun Imam Mahadi (a.s) shine sauraron bayyanarsa. Shiri da sauraro a rayuwar mu ta xai xai ku da kuma rayuwarmu ta ijtima’in mutane akan Imam Mahadi (a.s) tanada tasiri ta yadda hakan yazo a cikin ruwayoyin Imamai ma’asumai, sauraron yayewa shine mafi girman ibada kuma shine mafi girman aiki.
Lambar Labari: 171
BAYANI AKAN SAURARON IMAM MAHADI (A.S)
Xaya daga mafi muhimmancin abu akan batun Imam Mahadi (a.s) shine sauraron bayyanarsa. Shiri da sauraro a rayuwar mu ta xai xai ku da kuma rayuwarmu ta ijtima’in mutane akan Imam Mahadi (a.s) tanada tasiri ta yadda hakan yazo a cikin ruwayoyin Imamai ma’asumai, sauraron yayewa shine mafi girman ibada kuma shine mafi girman aiki. A nan zamu shiga bayani ne akan wannan sha’anin ta yadda zamu fahimci haqiqanin sauraro da kuma aikin da ya kamata muyi lokacin sauraron wato lokacin gaibar Imam zaman (a.j).
                MA’ANAR INTIZARI ( SAURARO) YAYEWA.
     Wannan kalma ta INTIZARI a loga tana nufin idon da yake duban hanya kuma yake jiran wani da sukayi wata magana dashi ko wani alkawari da shi, wato jiran wani wanda kayi alkawarin haxuwa dashi, ma’ana sauraron zuwan wanda ake jira(1) . Amma kuma a Isxilahi, INTIZAR FARAJ, yana nufin zauraron jiran bayyanar zuwan Imamin karshen zamani,wanda zuwanshi zai tseratar da mutane daga bakin zaluncin da azzalumai suka cika Duniya dashi. Domin  hakane ma sahabbansa suke sauraron zuwan shi domin kafa hukumar adalci a duk Duniya.
     Saboda haka an haska mana ma’anar INTIZARI gaba xaya; saboda mutane sun kasance suna kuskuren yima wannan kalma fassarar kuskure a tsawun Tarihi ana kuskuren fassara akan batun INTIZARI akan wannan bayanin da mukayi, ko kuma ya zama ana yi mata wata fassarar ta daban:
                      INTIZARIN KUSKURE DA TASIRINSA.
    Wasu daga cikin xai xai ku suna yiwa wannan kalma fassarar kuskure akan Imam Mahadi (a.s) musamman akan lokacin bayyanarsa, sukan ce wai dole ne surinka aikata munanan ayyuka saboda hakan shi zai sa Imam xin ya gaggauta bayyana, a wajarsu kuwa wai tunda an ce Imam Mahadi (a.s) ba zai bayyana ba sai kasa ta cika da zalunci da ja’irci, saboda haka domin gaggauta wannan fata, sai su dukufa wajen aikata ayyuka marasa kyau, suna ganin wannan shine aikin da zasuyi domin sauraron bayyanar Imam xin, yana nufin muyi kokari wajen yin zalunci da varna domin gaggauta bayyanar Imamin zamani (a.j) ko kuma idan ba haka ba mafi karancin aikin da zamuyi shine kada muyi faxa da zalunci mu kauda kai daga zaluncin azzalumai. A wani bayanin nadaban kuma akan wannan asasin shine wai ma’anar sauraro dinnan shine mu hadu kawai mu tsaya kallo akan zaluncin dake faruwa a wannan Duniya batarae da wani aiki ba, wato hakikanin wanda yake yana sauraro shine wanda ya tsaya yana kallo kawai akan abinda ke faruwa a wannan Duniya batareda tavuka komai ba.
    Wannan Magana akan batun sararo tabbas kuskure ce, bayan munsan cewa mafi muhimmacin abinda yasa Imam zaman yin gaiba shine saboda zaluncin mutane da kauda kai da sauran zaluncin da wasu keyi. Saboda haka daga lokacin da mutane suka zama haka ko kaxan Imam Mahadi (a.s) bazai tava bayyana ba. A wani bayanin na daban kuma zamu iya cewa: wanda zai iya kasancewa xaya daga cikin sahabban Imam xin shine wanda ya hana kanshi zalunci ya kuma tashi domin yaki da zaluncin da ake yiwa sauran mutane, kamar mutumin da yasan zaiyi bako ya tashi ya gyara gida ya tsaftace shi kuma yayi abinci na musamman domin tarar wannan bakon nashi wannan a hakika shine wanda yake sauraro. Ba wai wanda yasan da zuwan  bako ba amma ya kasa tsaftace gidansa bama haka ba a a wai bakon yake jira idan yazo ya gyara masa gidan sannan ya zamo masu da abinda zasuci  wannan wani duk aikin bakonne, kaga wannan bazumuce yana jiran bako ba bane.
              INTAZARI NA GASKIYA DA KUMA KO KARI A KAI
     A wani yanayin kuma bayan wacen fassara ta kuskure akwai kuma wacce take sahihiya wacce irinta ake so wanda manya suka ayyanata. A wannan asasi dai dai kun mutane da kuma majmu’arsu suke ko kari domin wannan aikin mai girman gaske, kuma domin isa ga wannan hadafi suke aiki iya bakin ko karinsu. Hakanan dai dai kunsu da kuma majmu’arsu sun yadda suyi aikin don cika wasiyyar Manzon Allah (s.a.w) inda ya ce:  
كلكم راع و كلكم  مسئول عن عيّته ( Dukkanin ku masu kewune kuma za a tambaye ku akan abinda kuke kiwu). Wannan ya zama tamkar sauke nauyi ne tunda an ce anbaku kiwune , saboda yin ko kari da yin umarni da aiki kyakkyawa da kuma yin hani da aiki mummuna ya zama wajibi garemu domin share hanyar zuwan Imami zaman (a.s).
                  WAZIFAR MASU SAURARO DAGA RUWAYOYI
     Ya zo a ruwayoyi daga ma’asumai cewa abinda yafi muhimmaci daga wajen masu sauraro gashi kamar haka: Na farko shine sanin Imami zaman.
    Daya daga cikin wazifa a ko wane zamani a lokacin gaibar Imam Mahadi (a.s) a wurin ‘yan shi’a shawara ko Karin sanin Imamin zamani akan kin kansa, saboda hakane ma Imam Sadiq (a.s) saboda muhimmancin wannan lamari yake cewa:  اعرف امامك فانّك اذا عرفت لم يضرّك تقّدّم هذاالأمر أو تأخّر)))) kasan Imaminka tabbas idan kasan shi bazaka cutuba wajen gabatuwa ko jinkiri akan wannan al’amarin ba(2) .
      Tabbas munsamu haske akan abinda yahau kanmu lokacin sauraron Imam zaman (a.s) tunda bamu san yanda yake yin rayuwarsa ba kawai dai munsan cewa yana raye kuma shi magajin Annabi ne kuma yanada mukamin manzila na kalifancin Ubangiji a doron kasa, saboda haka da wannan ne zamu iya saninsa kuma ta hakane zamuyi ayyukan da suka hau kanmu.
        Abu na biyu kuma shine ko kari da yin takawa wato yin aiki don Allah: Yin aiki tareda takawa yanada cikin hukuncin Ubangiji wanda a ko wanne zamani ya zama dole a kuma lokacin gaiba yafi muhimmanci sosai, duk da dai cewa wannan aiki na sauraro shine jarabawa mafi wahala ta hanyar rashin bayyanar Imam (a.s) laifuka sukayi yawa a tsakankanin mutane, hanya xaya wajen cin nasara akan wannan matsalar shine yin takawa wato yin aiki don Allah, Imam Sadik ya ce: { Duk wanda yake son zama daga cikin sahabban ka’im , dole ya zama mai takawa kuma lokacin sauraron Imam ya zama mai aklak, saboda haka idan ya mutu kafin bayyanar ka’im kamar wanda ya rayune tareda ka’im(3) .
     Abu na uku kuma shine yawaita addu’a akan bayyanar Imam zaman:  Duk wanda ya shirya akan sauraron Imam (a.s) kuma yake so Ubangiji ya kasance tareda dashi to ya yawaita addu’a akan lafiyar Imam zaman, karya yadda kuma ya gafala daga yin wannan addu’ar domin da yin wannan addu’a Imam yana shiryar dashi da kuma sauran mutane. Imam da kanshi yayi umarni ga ‘yan shi’arsa da yin hakan. Inda ya ce: ku yawaita addu’a sosai akan gaggauta yayiwar faraji.
  Manufar Imam akan wannan shawara ko kuma mu ce umarni ba wai kawai mai maita kalmomi da mutsa harshe ne kawai ba, a a addu’a a koda yaushe tanada lada sosai, kai bama haka ba wannan shine ainufin sauraro idan munfahimci abinda addu’ar ke nufi, domin idan muna son wani abu daga wajen Allah madaukakin sarki addu’ace muke yi don ya biya mana mukatunmu.
   Na hudu zama cikin shiri a koda yaushe: Daya daga mafi muhimmanci abinda yahau kan mai sauraro lokacin gaiba shine shiri a koda yaushe. Wannan ma’ana itace ya kamata  ta zama wazifar ‘yan shi’a a koda yaushe a rayuwarsu saboda a koda yaushe Imamin zamaninsu zai iya bayyana.
  Wannan shine dan abinda zamu iya kawuwa muku akan batun Imam Mahadi (a.s) munyi muku mayani tundaga haihuwarshi harzuwa batu akan bayyanarshi, muna fatan za a amfana da wannan rubutu da mukayi, insha Allah zamuci gaba da kawu muku ire-iren wadanan rubuce-rubucen domin ilimantarwa da cigaban al’ummar mu baki daya. Aminci ya tabbata ga wadanda sukaji gaskiya kuma suka bita.
   
Aliyu Abdullahi Yusuf: Whatsapp, Telegram, Instagram, da sauran Media Number: +2348037493872.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: