bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      01:12:23
Yadda za a gane Mauludi baya cikin Addini shi ne: meye Farillai ko Sunnoni ko Mustahabban Mauludi? Amsa:- Shin kuna Nufin Dukkan Abin da ya zamo Addini Dole ya zamo yana da Farillai da da Sunnoni da Mustahabbai? Idan kuka ce
Lambar Labari: 172
HUJJOJIN YIN MAULUDI KASHI NA 2

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinqai, Tsira da Amincin Allah su Tabbata, ga Manzo da Alayensa, Tsarkaka Managarta.

A cigaba da Bada Amsa ga Masu Qin yin Mauludi zamu basu Amsar Shubuharsu ce da suke cewa:
 4-Yadda za a gane Mauludi baya cikin Addini shi ne: meye Farillai ko Sunnoni ko Mustahabban Mauludi?
Amsa:-
Shin kuna Nufin Dukkan Abin da ya zamo Addini  Dole ya zamo yana da Farillai da da Sunnoni da Mustahabbai? Idan kuka ce: E, to Tambayarmu ta Farko ita ce: To Ku Gaya Mana Farillai da Sunnoni da Mustahabban Gasan karatun Al-qur'ani. Ko Farillai da Sunnoni da Mustahabban Wa'azi a Wurin Walima. Ko Farillai da Sunnoni da Mustahabban Wa'azin Qasa da na Jaha da na local government.
Tambaya ta biyu itace: Farin cikin Aure ko Haihuwa Wanda Musulunci ya Yarda a yi, wato yin Farin cikin Aure da Haihuwa yana cikin Addini, ko zaku kawo Mana Farillai da Sunnoni da Mustahabbansa?  Ashe Son Annabi (s.a.w) da Girmama shi* ba wajibi bane? Ashe ba Allah ne ya ce: "Amma bisa Ni'imar da Allah ya Maka ka faɗa" ba? Shin Akwai Ni'imar da ta fi Samuwar Manzon Allah? To Ta ya faɗansa a Ranar Maulud zai zamo laifi?   In dai Har Shekh Bin Baz zai ce:
ينبغي أن يكون اليوم الوطن يوم شكر لله، ولا بد من السمع والطاعة لولاة الأمر.
Ya kamata Ranar 'Yancin Qasa ta kasance Ranar Godiya ce ga Allah, kuma ba Makawa wato Dole a Ji kuma a yi Bi Shuwagabanni.
Tambayarmu ita ce: Yaushe Qasa tafi Manzon Allah? da Har za'a Ware Mata Rana ta Musamman don Bukukuwa da Murna, Amma Ware wa Manzon Allah Rana Don Murnar Haihuwarsa ya zamo Bidi'a?!  Sannan zamu so a Faɗa Mana Farillai da Sunnoni da Mustahabban Biki da Murnar Ranar 'Yanci da ake yi a Saudiyya. Kada Wani ya ce: ai Wannan Biki da ake yi na Ranar 'Yancin Qasa ba Addini bane, Sai Mu Bashi Amsa da cewa: Inda yin Biki a Ranar ba Addini bane da Bai kamata Mafi Girman Mai bada Fatwa ya kira Ranar da Ranar: Godiya ga Allah. Kuma Wajibi ne a Ji kuma a Bi Shuwagabanni ba. Saboda Waɗan nan Abubuwa Biyun Suna cikin Addini.
Muna Cigaba da Bada Amsar Shubuhansu ce inda suke cewa:
 
5- Ana cakuɗuwa Maza da Mata a gun Mauludi, Alhali yin Hakan Haram ne.

Amsa:
Da Gaske cakuɗa Maza da Mata Haram ne a Addinance, sai dai Gaskiya ni ban San waɗan da suke cakuɗa Maza da Mata a Wurin Mauludinsu ba, Abinda na Sani shi ne wurin da Mata suke Zaune daban da na Maza, kamar yadda Masu ƙin Mauludin a Wurin Tahajjud Ɗinsu suke keɓe wa Mata Wurinsu daban da na Maza.  A Taqaice Wannan Dalilin bai kai ga Haramta yin Maulidi ba, sai dai Mun Sani cewa: Haɗuwa Maza da Mata Haram ne a Maulidi ko a Sahun Salla, Amma Hakan ba zai Sa a Haramta yin Salla ba, sai dai a Haramta Haɗuwan ba Sallar ba, Misali akan Haka Shi ne: Yin Riya a Salla Haram ne Amma Haka ba zai Sa ace Yin Salla ya Haramta ba, to Haka ma Maulidi idan aka cakuɗu Maza da Mata ya zama an Aikata Haram Amma Hakan ba zai Sa a Haramta yin Maulidi ba.  Idan baka gane Wannan Misalin ba to ga Wani, Idan kuka ce Cakuɗuwa Maza da Mata zai Sa a Haramta Abinda don shi aka Cakuɗu sai muce: Ai ana Cakuɗa Maza da Mata a Kasuwa don Haka zuwa Kasuwa ya zama Haram kenan?
Ana Cakuɗa Maza da Mata a Hanya, Shin Tafiya a Hanya ya Haramta kenan?
Haka ma Masallaci Musamman na Idi ana Cakuɗa Maza da Mata, Shin  zuwa Sallan Idi ya Haramta kenan???
Muna Cigaba ne da Bada Amsar Shubuhan Masu ƙin Yin Mauludi, Suna cewa:
6-Masu yin biki da murna a ranar Mauludi suna Murana ne da Rasuwar Manzo (s.a.w) saboda a
Ranar da aka Haife shi a Ranar ya yi Wafati.

Amsa:
Muna da Amsoshi kala Biyu kamar Haka:
1-Na Farko Idan Mun ƙaddara cewa: Haka ne a irin Ranar da aka Haifi Manzo (s.a.w) a irin Ranar ne ya yi Wafati, to sai Mu ce: Wannan ba Matsala tunda Ayyuka suna tare ne da Niyyoyinsu, idan ka yi Niyyan yin Mauludi ba za'a Canja Maka da na Wafati ba tunda ba Niyyan Wafati ka yi ba, Misali akan Haka shi ne: Idan Yau Al'hamis Ɗanka ya Rasu sai Wata Ranar Alhamis ɗin Matarka ta Haihu kaga Ranar Alhamis Mai zuwa ne za ka yi Murna na Sunan Ɗan da aka Haifa Maka, to idan aka zo ana Murnan Haihuwan sai ace: a'a Baƙin cikin Rasuwan kake yi tunda a irin Ranar ne aka yi maka Rasuwa???

2-Ballantana ma Mu bai Inganta ba a wurinmu cewa: a irin Ranar Haihuwan Manzo (s.a.w) a irin Ranar ne ya yi Wafati, Sam Hakan bai Tabbata ba a Garemu, mun fi Tafaya akan cewa: Manzo (s.a.w) ya yi Wafati ne a 28 ga Watan Safar. Don Haka kwata-kwata Wannan Dalilin nasu ba Dalili ne da zai Haramta Yin Maulidi ba, Musamma ga Masu Fahimta da kuma Adalci.
Dalilin Masu ƙin Mauludi shi ne:
7-keɓe wani Wata da wani Rana don yin Mauludin
Annabi (s.a.w) Taqaita son da ake masa ne, don ya kamata ne kullun Mutum yana son Annabi (s.a.w).

Amsa:
A haƙiƙa keɓance Wata ko Rana don Baiyyana Soyayya da Girmama Manzon Allah Sam bai nuna Taƙaita Soyayyar Manzo, tunda ba Wai a Wannan Wata ko Ranar ne kaɗai ake Son Manzon Allah (s.a.w) a ciki ba, Sai dai Yin Mauludi a Ranar yana nuna cewa: Ana la'akari da Munasaba ne, kamar yadda za ka ga ana Yawaita yin karatun Al-ƙur'ani a Watan Ramadan fiye da Sauran Watanni Saboda Munasaba bisa la'akari da cewa: a Watan ne Al-ƙur'ani ya Sauka, kaga kuwa don Mutum ya yawaita karatun Al-ƙur'ani a Watan Ramadan bai kamata a zarge shi cewa: Don me ya Aikata hakan ba, kuma har su Masu ƙin Mauldin zaka ga suma suna yin Jam'in Tahajjud a cikin Watan Ramadan ne kawai, ba su yi a Wani Watan da ba Ramadana ba, kenan Muma zamu iya cewa: Ashe kuma kun Taƙaita Sallan (Tahajjud) tunda ba Ku yi Sai a Watan Azumi? Tabbas Ranar Haihuwar Mutum Rana ce Mai Mahimmanci a Gare shi shi da Masoyansa, Mahimmancin Ranar Haihuwa ne tasa  Annabi Isa (a.s) ya ce:

{{ﻭَﺍﻟﺴَّﻠَﺎﻡُ ﻋَﻠَﻲَّ ﻳَﻮْﻡَ ﻭُﻟِﺪﺕُّ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃَﻣُﻮﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃُﺑْﻌَﺚُ ﺣَﻴًّﺎ}}

{{Kuma Aminci ya Tabbata a gareni a Ranar da aka Haifeni, da Ranar da zan Mutu, da Ranar da Za'a Tasheni a Raye}}. To Mahimmancin Ranar Haihuwa, tasa Muke Nuna Soyayyarmu ga Manzo (s.a.w)  a Ranar da aka Haife shi bisa Munasaba. A Cigaba da bada Amsar Shubuhata Takwas cewa suke yi.

8-Anfi Qasar Saudiyya ce son Annabi (s.a.w) meyasa su basu yin Mauludi?.

Amsa:
Na Farako: Dai Babu inda Allah ko Annabi suka ce: ƙasar Saudiyya ita ce: Ma'aunin Inganci ko Rashin Ingancin wani Aiki , Balle har ace tunda ƙasar Saudiyya ba ta yi ba, don haka muma Ya Haramta mu yi, kuma ko su Masu ƙin Mauludin sun San Haka don har Suma Wataran suna faɗin hakan: "Suna cewa: Ai Allah bai turo Maka ƙasar Saudiyya ba" Amma fa sai ka ce musu ai ƙasar Saudiyya tana Jiyarwa a Salla, Amma Ku gashi Baku Jiyarwa a Sallanku, sai su baka Amsa da cewa: Allah bai turo Maka ƙasar Saudiyya ba". to muma muna Baku irin Wannan Amsar, Allah bai turo Mana ƙasar Saudiyya ba".
Don haka idan Saɓama ƙasar Saudiyya laifi ne, kuma kun Saɓa Mata tunda tana Jiyarwa a Salla Ku kuma Baku Jiyarwa, kamar yadda muma muka Saɓa Mata da muke yin Maulud su kuma basu yi a Gwamnatance.
Na Biyu kuma: tunda suna Ganin cewa: Ya kamata a yi Biyayya ga ƙasar Saudiyya akan Rashin yin Mauludi, kuma bai kamata a Samu suna saɓa musu akan wani Al-amari ba, sai gashi kuma suma suna  Sassaɓa Musu akan Abubuwa Masu yawa, Misali:
A Yayinda Qasar Saudiyya ta kori Ash-Shekh Al-bani daga Qasar, Sun Saɓa da su akan koransa da Suka yi.
Hakama Sun Saɓa da Saudiyya akan Dokan da Qasar ta Ɗauka akan Usama da 'Yan Taliban.
Don haka Idan Saɓa ma Qasar Saudiyya kauce Hanya ne, kuma kuna Saɓa Mata Kamar mu.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi.
Tahir Umar Sulaiman.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: