bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      01:40:21
Saidai abu xaya da baya canzawa duk da wannan ruguntsumin na waxannna canje- canjen masu sauri irin saurin mizayel da kuma yalwa da faxi irin ta satlayit shi ne; Xan Adam,
Lambar Labari: 176
Da sunana Allah mai rahama mai jin qai

Ina muka kwana?.
Game da Musulumci da koyarwar sa dawwamammiya!!!
A yau ne na kammala muku addinin ku kuma na cika muku ni’ima ta.

 
   A wane karni muke rayuwa?  Ta yadda har yanzu wahala kawai muke sha ba mu fara amfana da abin da muke shukawa ba, wai shin meye sunan waxannan shekarun waxanda xan Adam yake shuxe su  yana mai fama da kunci da raxaxin jiki ?
  Wannan shi ne qarni na ishirin da xaya!
 Qarnin miza’ail da satlait da kuma yin safara zuwa dunuyar wata, qarnin da ilimi ya kai qololuwar sa wajen cigaban xan Adam da kuma qere- qere, qarnin da tunanin xan Adam da wayewar sa suka kai qololuwa kuma koya ya fara jin cewa shi wani vangare ne na Al’ummar sa yana da hakki kamar yadda kowa yake da shi, kuma mutane suke bashi girman sa.
  Wai shin manenen wannan qarnin na ishirin da xayan ne!!!?
  Haqiqa shi wani gutsure ne daga cikin zamanin da Xan Adam yake rayuwa a doron qasa wanda yake shuxewa a kan rayuwar mutane, ba abin da ya shafe shi, shin mutane sun kasance a cikin ci gaba a cikin tunani ne ko kuma ci baya, shin sun haxa kan su ne ko kuma sana ta fama da rarrabe-rarrabe da kuma faxace –faxace, babu ruwansa zai ci gaba ba tare da la’akari da abin da yake gudana a cikin rayuwar Xan Adam ba.
  Kuma da sannu qarni na ashirin da biyu zai zo kuma rayuwa zata xaukaka a cikin sa sama da yadda yake a yanzu, kuma da sannu ci gaban cikin sa zai qaru da gaske, sanna zamu dawo muna kallon ci gaban da ya ke cikin qarni na ashirin da xaya ba wani abin a zo a agani ba. Alhali a farkon bayyanar su mun kasance muna ganin su wani babban lamari wanda ya girmama a cikin qwaqwalen mu.
  Kuma da sannu zamu maimaita ainihin abin da muka faxa a yayin da qarni na ashirin da uku ya zo, kuma hakan zai ta faruwa mutuqar motar rayuwar Xan Adam tana garawa a doron kasa.
  Saidai abu xaya da baya canzawa duk da wannan ruguntsumin na waxannna canje- canjen masu sauri irin saurin mizayel da kuma yalwa da faxi irin ta satlayit shi ne; Xan Adam, shi ne wannan Xan adam xinnnan wanda yake kawo sauyi da canje-canje ya kuma ci gabantar da shi da irin wannan saurin, kama yana mai kwatanta rayuwar sa daidai da waxannan canje- canjen a cikin hanzari da sauqi da kuma kaifin basira, amma shi kansa a daidai wannan lokacin ba zai yiyu ya canji ya shige shi ba (ba zai yiyu ya canza ba).
  Tabbataacce ne shi  ta vangaren xabi’arsa ta mutumtaka, ta vangaren garizar sa, haka ma ta vagaren dangogin axifofin sa, kuma tabbatacce ne shi ta vangaren ginin sa na jiki dana hankali.
  Hanyar da yake qosar da sha’awar sa bata canzawa har abada, kuma haka lamarin yake game da son mallaka da iko, hakama game da yunwa da ci da kuma qishirwa da sha, hakama game da jinsi da kuma jin daxi da wani jinsin, haka ma game da kosawa, da jin daxin kallon abubuwan kallo na xabi’a ko waxanda aka kera da kuma shaqar daddaxar iska da kuma kanshi.
  Kamar yadda ta bangaren axifar sa babu wata sabuwar axifa da ta haifu a cikin xabi’ar sa ta xan Adam watan waxanda aka saba da su, na daga fushi da yarda da baqinciki da farinciki da raxaxi da buri.
  Kamar yadda babu wani zamani da zai zo da tsarin jikin mutum zai cenza a cikin sa ko mu same shi da wani yanayi wanda ba lafiya ba kuma ba rashin lafiya ba ko kuma wanin daqiqanci da kaifin basira ko kuma mutunm ya shuxe bisa kan matakan rayuwa waxanda ba yarinta da samarta da manyanta da tsufa a cikin su.
  Hakama ta bangaren hankali babu wani zamani da zai zo da mutum baya neman rabauta a cikin sa, ko kuma baya ganin fifici a matsayin alkhairin da ya cancanta a aikata shi, kuma qasqanci sharri ne wanda ya wajaba a nisance shi, kamar yadda daidai da rana bai tava barin yin sa’ayi a bisa nema kamala ba.
  Waxannan dukkanin lamura ne waxanda suke xamfararru a cikin rayuwar mutum, waxanda basa bukatar wani bayani mai yawa, kuma a kafe suke a cikin xabi’ar Xan Adam tun asalin zamanin da aka halicci mutumtaka, kuma da sannu ba za su mutu ba sai da mutuwar sa. Kuma mutum ba shi da wata hanya ta ci gabantar da su ko wadatuwa daga gare su, kuma daga ainihin waxannan abubuwan ne ci gaba ya samo asali, kuma a kan su ne ya ginu kuma har yanzu yake ginuwa, kuma a kan su yake tsaye a iya gwargwadon mutuqar sa, kuma bai isa ya wuce su ba har abada a fagen faxaxar sa, da yalwatuwar sa da kuma ambaliyar sa. [zamu ci gaba]

Daga cikin hadisan hikima na sayyadina Ali (AS)

* An halicci duniya domin wanin ta kuma ba’a halicce ta ba domin kanta.
* Ku tuna da yankewar jin daxi da kuma wanzuwar sakamakon ayyuka.
* Mutane maqiyan abin da suka jahilta ne.
* Babu wani gari da yafi cancantuwa da kai fiye da wani, mafi alhairi gari wanda yake xauke da kai.
* Wanda ya ke yin kasuwanci ba tare da masaniya (sanin hukuncin sa) ba haqiqa ya kutsa cikin cin riba.

Hajjin ban kwana
A yau ne na kammala muku addinin ku kuma na cika muku ni’ima ta.

  Menene amfanin yin bahaci ko Magana a kan halifanci bayan Manzo? kuma waye ma’abocin sa?
 Wannan tambaya ce da take ta maimaituwa a bakunan da yawa daga ciki malamai musamamn masu yin kira izuwa haxin kai!


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: