bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      01:42:26
A wanna lokacin Manzo ya sa aka yi shela aka tsayar da dukkanin waxanda suka wuce gaba daga ayarin da waxanda suke tare da shi kuma aka jira waxanda suke baya sanna yasa aka yi masa minbari.
Lambar Labari: 177
Kafin in kai ga bada wannan amsar zan Xan guzurce mu da wata babbar hadisa ta atrihi, wacce take mashhuriyar gaske!!!
A shekkara ta 23 bayan hijira Manzo (SAWW) ya yi hajjin bankwana wanda a cikin sa ya bayyana hukunce – hukuncen addini a dunqule kuma ya gayawa musulmi abubuwanda idan har suka yi riqo da su har abada baza su vace ba, kuma dukkanin sihahus sitta sun rawaito wannan hadisin da lafuzza mabanbanta, a inda Manzo (SAWW) yake cewa: "Lalle ni mai bar muku abubuwa biyu ne a baya na nauyaya (masa girma) littafin Allah da kuma Tsatso na, `Yan gigana, lalle Allah maxaukaki ya bani labari cewa baza su tava rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, don haka kuyi duba (nazari) bisa yadda zaku halifce ni a cikin su a baya na” a cikin wasu ruwayoyin a kwai qarin "Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana! Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana!! Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana!!!”.
  Bayan da Manzo ya  baro maka kafin ya yi nisa, a ya yin da ya karaso wajen wani Xan tafki wanda yake a mararrabar hanyar garuruwa daban- daban, wamda ake kira khum wato GADIR KHUM sai wahayi ya sauka a gare shi daga Allah Ta'ala tare da aya, wacce malaman tarihi da malaman tafsiri suka bayyana cewa itace ayar{یا ایهاالرسول بلغ ما انزل الیك من ربک فانلم تفعل فما باغت رسالته والله یعصمک من الناس  .....} ma’idah aya ta 66. ma,ana: ( Ya kai Manzo ka isar da abinda aka saukar maka daga ubangijin ka idan kuma har baka aikataba to bakaisar da saqon sa ba, kuma Allah zai kare ka daga mutane)
  A wanna lokacin Manzo ya sa aka yi shela aka tsayar da dukkanin waxanda suka wuce gaba daga ayarin da waxanda suke tare da shi kuma aka jira waxanda suke baya sanna yasa aka yi masa minbari, ya tsaya yana mai bayyana abinnda Allah ya umarce shi da shi, Manzo yayi dogon bayani wanda wannan takardar baza ta iya kawo shi a yanzu ba daga ciki akwai cewa "wanda duk  nazama shugaban sa to Ali ma shugaban sa ne, ya ubangiji ka jibinci wanda ya jiving ce shi kuma ka qi wanda ya qi shi, ka karkata gaskiya a duk inda yake…….” Har qarshe, wannan hadisa ce da dukkanin malaman tarihi suka rawaito kuma hakama sahihannan duga shida sun fitar da wannan hadisin da lafuzza mabanbanta bisa ma’ana xaya.
  Bayan da Manzo ya isar da wannan saqon na wahayi sai aka kuma saukar masa da wannan ayar bayan da ya sakko daga kan minbari: {الیوم اکملت لکم دینکم واتممت علیکم نعمتی ورضیت لکم الاسلام دينا....}  suratul ma’idah/3.  (A yau ne na cika muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yardar muku da muslumci addini….)
  Abin mamaki a nan shi ne zaka ga wasu suna ta kokarin su fassara wanna ma’anar da cewa: wai abinda ake nufi shi ne a so Imam Ali kawai! Wata tanbaya a nan shi ne ta ya ya hankali zai karvi wannan maganar! idan har son ne kawai don me zai buqaci sai an tara mutane, a tsakiyar rana da tsananin zafi kuma har Allah ya yiwa Manzo alqawarin zai kare shi gada sharrin mutanen da ba za su yarda da a binda zai faxa ba? Idan har so ne kawai ai ya isa ya gayawa was daga sahabbai su kuma su gayawa sauran kamar yadda misalsalin waxannan hadisan su ke dayawa, kuma ba muji Manzo ya buqaci hawa minbari domin faxar su ba,! Haba!!! Ba muga abinda Allah yake faxi ba; (idan har baka aikata ba to baka ma isar da sakon da aka aiko ka a kan sa bas am- sam,) babu shakka saqon da girman sa yakai ga Allah Ta'ala yayi irin wannan babban hukunci ba Xan qarami ne ba, lalle dole ya zama wani saqo ne wanda zai amintar kuma ya kare sannan ya tabbatar da ci gaban ginin da Manzo ya fara na al’ummar sa waxanda ba su daxe da barin kwanakinsu na jahiliyya da bunne `ya`ya mata da zalunci da kasha-kashen juna da sauran su ba.
  Wani irin hankali ne zai karvi cewa Manzo ya bar duniya bai yi wasicci ba alhali Allah ya wajabta yin wasici, a cikin alqur’ni kuma ya bayyana cewa Annabawan farko sun aikata, sannan a gefe gahadisan Manzo da dama sun zo suna yin umarni da hakan, shin muna so muce Manzo bai yi aiki da abin da Allah ya umarce shi ba, ko kuma shi kaxai ne Manzon da baya so kuma baya tausayin al’ummarsa don haka sai ya tafi ya barta kamar garken dabbobi ba jagora su ci Karen sub a babbaka, a she yanzu hankali zai  yarda da wannan, ina yabon da Allah Ta'ala yayiwa Manzo a cikin Alqur'ani na kyawawan xadi’u da kuma cewa shi mai tausayi ne ga muminai?
  Ina mai kira gare ka ya Xan ‘uwa na mai girma da ka dawo hankalin ka ka riqi hujja da gaskiya tun kafin ranar da dukiya da `ya`ya basa amfana komai sai wanda ya je wa Allah da kyakykywar juciya. Dolle ne idan kana so ka san haqiqa ka xauki gaskiya ka sa ta amatsayin ma’auni da zaka gwada kowa da ita. Ya zo a cikin hadisi daga Imam Ali (da wanna ma’anar) cewa "ka san mazaje da kaskiya kar ka nemi sanin gaskiya da mazaje” ma’ana kayi qoqari kasan mecece gaskiya, sannan sai ka xauke ta a matsayin ma’aunin da zaka xora kowa akan ta domin ka tantance matsayin kowa, ba kariqo wasu mutane su zame maka ma’aunin sanin gaskiya ba. A kwai abubuwa masu yawan gaske a tattare da wannan lamarin na gadir wanda babu lokacin da zan bayyana su, amma ga mai san qarin bayani ya koma littafin gadir na allama amini da kuma sihahus sitta da saurn su.
  [Ka kasance tare damu a fitowa ta gaba don jin amsar tambayar nan ta sama].

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: