bayyinaat

Published time: 20 ,July ,2018      01:59:24
Wanda ya rasa gane ruwan al'walansa a takanin zallan ruwa (maa'ul muɗ'laƙ)da ruwan da aka jingina shi ga wani abu (maa'ul mudaaf) to ya wajaba da yayi al'wala da dukkan ruwan biyu bisa ga ih'tiyaɗi. ko kuma wanda yake kokonton akan sallar da ta wuce wacce bai yiba a tsakanin sallar asuba da azahar, to ya wajaba da yayi dukkansu biyun bisa ga ih'tiyaɗi.
Lambar Labari: 179
ZAƁAƁƁUN HUKUNCE HUKUNCE KASHI NA 2

بسم الله الرحمـٰن الرحيم

اللهم صل على محمد وآل محمد.

Mas'alata 12: Akin ba'aame {wanda ba mujtahidi ba} wanda bai yi akan taƙalidi ba kwata kwata, ko wanda ya yi a kan vaceccen taqalidi, duk ana musu hukunci ne da ɓaci, sai dai idan yayi dai dai da waƙi'in al'amarin a wurin Allah Ta'ala, ko ya yi dai dai da ihtiyaaɗi, ko yayi dai dai da fatawar mujtahidin da ya wajaba ya yi mar taƙalidi.

Mas'alata13: Yana halasta ga mukallafi ya yi rabi da rabi a farawan taƙalidi, wato ya ɗauki wasu mas'aloli ko wasu babobi daga wani mujtahidi, wasu mas'alolin da wasu babobin na daban kuma ya ɗauka daga wani mujtahidin na daban, kai yin hakan ma yana wajaba bisa ga ihtiyaaɗi idan ya kasance kowanne ɗaya daga cikinsu mujtahidan biyu ya fi ɗayan sani akan mas'aloli ko babobin da yake son yin taƙalidi da shi a cikinsu.

Mas'alata 14: Bai halasta bisa ga ihtiyaaɗi canjawa daga rayayyen mujtahidin da ya cika sharuɗ'ɗan ijtihadi, zuwa ga wani mujtahidi na daban, musamman idan ya kasance na farkon shi yafi ilimi.

BANBANCI TSAKANIN IHTIYAAƊI ISTIHBABI DA WUJUBI:

Mas'alata 15: ih'tiyaɗi is'tih'baabi shi ne: wanda fat'wan mujtahidi ya rigaye shi zuwa ko ya rigayi fat'wan zuwa, akan saɓani, don haka mai taƙalidi yana da zaɓi na yin aiki da fat'wan ko ih'tiyaɗin, mai taqalidi ba zai koma zuwa ga wani mujtahidi na daban ba.
misali akan haka shi ne: Butan da ya najastu ana wanke shi ne: da ruwan kur sau ɗaya, amma bisa ga ih'tiyaɗi a wanke sau uku.

Ih'tiyaɗi Wujubi shi ne: ih'tiyaɗin da kafin shi ko bayan shi babu fat'wa da ya zo wanda ya saɓa masa, don haka mai taƙalidi a wannan yanayin ko dai kayi aiki da wannan ih'tiyaɗin ko ya yi aiki da shi (ih'tiyaɗin) ko ya koma zuwa ga wani marja'in da ba nashi ba, tare da dubi zuwa ga a'alam (mafi ilimi) bisa ga ih'tiyaɗi.
Misalin haka shi ne:
Bisa ga ih'tiyaɗi rashin yin sujada akan ganyen inabi idan ba busash'she bane.

Mas'alata 16: Akwai wani nau'in na ihtihaɗi shi ne: fat'wa da ih'tiyaɗin na daban, wanda shi sau da yawa yana kasancewa ne a ɓangaren (ilmul ijmali bittaklif) wato ilimin taklif a dunƙule, a wannan yanayin yana wajaba akan mukallafi yayi aiki da ih'tiyaɗin da mujtahidin yake bi yayi, bai halasta ya koma zuwa ga wani mujtahidi na daban ba. misali akan haka shine:
Wanda ya rasa gane ruwan al'walansa a takanin zallan ruwa (maa'ul muɗ'laƙ)da ruwan da aka jingina shi ga wani abu (maa'ul mudaaf) to ya wajaba da yayi al'wala da dukkan ruwan biyu bisa ga ih'tiyaɗi. ko kuma wanda yake kokonton akan sallar da ta wuce wacce bai yiba a tsakanin sallar asuba da azahar, to ya wajaba da yayi dukkansu biyun bisa ga ih'tiyaɗi.

Mas'alata 17: jahili muƙassiri shi ne: jahilin da yasan shi jahili ne, kuma yasan hanyoyin da zai bi don yaye wannan jahilcin amma bai bi hanyar ba.

Jahili qaasiri shine: jahilin da kwatakwata bai san shi jahili bane, ko kuma bai san hanyar da zai bi don yaye jahilcin da yake fama da shi ba.

Mas'ala ta 18: ma'anar kalmar: baya halasta [laa yajuzu] dai dai yake da ma'anar haramci [haraam] a bigiren aiki. Ma'anar kalmar: ba matsala  a cikinsa [laa ish-kaala fihi] ma'anarta dai dai take da fatawa akan halasci. Ma'anar kalmar: akwai matsala a cikinsa, [fihi ish-kaal] ko [fihi ta'ammul] ko [taraddudun] ma'anar su dai dai  yake da ih'tiyaaɗi wujubi a bigiren aiki.

{hukunce hukuncen wilaayatul faqih}

Mas'alata 1: wilaayatul faqih ma'anarta, hukumar faqihi adili masanin hukunce hukuncen addini don jagoranci da gudanar da shugabancin al'umma a qadiyoyi da al'amura mabanbanta.

Mas'alata 2: abinda ake nufi da wilaayar faqihi a sake (muɗ'lak) sh ine: lallai addinin musulunci miƙaƙƙe wanda shi ne cikamakin addinai, kuma wanzajje zuwa ranar al'kiyama, shi addini ne na hukunci da gudanar da sha'anin al'umma, don haka babu makawa akan samun shugaba a dukkan matakan al'ummar wanda zai tsayar da adalci a cikinsu kuma ya kawar da zalunci, kuma yana gudanar al'amuransu bisa ga mabanbantan matsayoyinsu.
zai yiwu umurnin waliyul faqih a yayin zartar da shi a aikace ya cin karo da 'yancin wasu mutane ko da manfa'arsu ko da kwadayinsu, sai a gabatar da buƙatun waliyu

l faƙih akan buqatun sauran mutanen, domin buqatun waliyul faqih tana goge nasu buƙatun.

Mas'alata 3: ya wajaba akan dukkan musulmi yin biyayya ga umurce umurce da hukunce hukuncen da suka gangaro daga waliyul faƙih, kuma bai halasta a saɓa masu ba, kai yana wajaba ma a miƙa kai ga umurninsa da hanuwa ga haninsa, hatta akan mujtahidai da marja'ai masu girma-allah ya ƙarfafasu- ballantana ga masu yi musu taƙalidi

Mas'alata 4: bai halasta a saɓa ma umurce umurce da shawarwarin da suka gangaro daga wakilin waliyul faƙih, idan ya kasance akan iya hurumin da ya samu ne daga waliyul faqih.

Mas'alata 5: ya wajaba ayi ɗa'a da biyayya ga shugaban musulmi (waliyul faqih) a wurarenda aka samu saɓanin ra'ayi a tsakaninsa da marja'an taƙalid, idan ya kasance saɓanin yana ɗanfare ne da gama garin al'amura na jagorancin jama'a, ko qadiyoyin da suka shafi dukkan musulmi, kamar:
Abin da ya shafi kariya ga musulunci da musulmi daga ɗagutai da masu ƙetare haddi.

Mas'alata 6: a cikin mafaahim ɗin  musulunci babu maf'huminda ake kira da: wulayar gudanar da mulki (wulayatul idariyya) sai dai bai halasta a saɓa ma umurce umurcen shugabanci da suka gangaro akan asasin tabbatattun dokoki.

Mas'alata 7: baya halasta a saɓa ma umurce umurce da shawarwarin da suka gangaro daga wakilin waliyul faƙih, idan ya kasance shawarwarin da suka wajabta ne, kuma ya kasance a cikin hurumin da ya samu ne daga waliyul faƙih

Wassalam.

Tahir Umar Sulaiman.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: