bayyinaat

Published time: 21 ,July ,2018      15:09:46
Sau da yawa mukan ga samari da ‘yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin idan mutum ya balaga yakan zama kamar danyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe.
Lambar Labari: 181
Sau da yawa mukan ga samari da ‘yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin idan mutum ya balaga yakan zama kamar danyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe. Sau da yawa wannan al’amari na halitta ya sanya wasu suka kasa juriya, suka gajiya gaban sha’awarsu, suka sallama mata, al’amarin da yakan janyo fasadi mai girma a cikin al’umma. 
Daga cikin irin wannan fasadi zamu yi kokarin kawo misalin abin da yake daya ne daga ciki da ake cewa da shi istimna’i. Istimna’i wata mummunar dabi’a ce da takan samu samari ko ‘yan mata masu tashen balaga da sukan yi amfani da jikinsu ko hannunsu ko kayansu ko wani abu domin fitar da maniiyi daga gare su. Babbar musifar da istimna’i yake jawowa ta hada da: 
1- Rauni da rashin karfin jiki;
2- Raunin kwakwalwa da kasa rike karatu ko kadan;
3- Rasa gani da makancewa daga karshe;
4- Karkarwar jiki;
5- Rashin nutsuwa;
6- Yawan tunani;
7- Son warewa waje daya, da kebewa;
Maganin Istimna’i
Malamai sun kawo wasu abubuwa da suke maganin wannan mummunan ciwo mai haifar da miyagun halaye da munanan dabi’u kamar haka.
1- Nisantar duk wani abu mai kawo sha’awa, kamar kallon fila-falai da mata suke rawa ko suke sanya kayan da bai dace ba da duk abin da ya san yana sanya shi jin sha’awa. 
2- Shagaltar da kansa da wasu abubuwan, kamar tsara lokutansa na karatu da na zuwa filin wasa, ya kuma rika yin wasan motsa jiki da karanta littattafai kamar na ilimi ko jaridu, da zuwa wajan hutawa da shakatawa domin ya samu saukin kuncin ransa, da ware lokacin da zai rika yin yawace-yawace a lokacin da ba shi da komai, da yawan karanta Kur'ani koda fatiha ce a kan hanyarsa, da zuwan wajen tarurrukan wa’azi da shirya irinsu, da yawaita zuwa masallaci a lokacin kowace salla. 
3- Sanya wa kansa aiyukan da zasu cike lokacin hutawarsa. 
4- Kula da wasannin motsa jiki kamar gudu a filin wasa, daga abubuwa masu nauyi, iwo a ruwa, da sauransu;
5- Idan akwai lokutan da ya saba aikata wannan mummunan hali a cikinsu sai ya kirkiro wa kansa wani abu daban da zai shagaltar da shi a irin wadannan lokutan kamar zuwa hawan sukuwar doki ko iyo da sauransu. 
6- Ya nisanci zama shi kadai har abada koda bacci zai yi to ya kasance cikin mutane ta yadda idan ba wani abu na lalura ba kamar kama ruwa da bahaya to ba yadda za a yi ya kasance shi kadai. 
7- Da zarar ya samu yalwa da dama to ya yi maza ya yi aure kada ya jinkirta ko kadan. 
8- Raya karfin ruhinsa ta hanyar jin cewa zai iya maganin wannan halin da taimakon Allah. 
9- Nisantar masu irin wannan halin nasa. 
10- Cin abinci mai kyau da tsara lokutan cinsa ta yadda ba ko da yaushe ne zai ci wani abu ba, da kuma wanka da ruwan sanyi a wasu lokuta, da nisantar sanya tufafi masu matse masa jiki. 
11- Addu’a da neman taimakon Allah, da jin cewa Allah yana ganin sa duk inda yake koda ya shiga daki ya rufe ne shi kadai, ya ji cewa kuma Allah zai yafe masa abin da ya yi, kuma ya daukar wa Allah alkawarin ba zai sake ba .
Wasu Hanyoyin
Wasu malamai sun kawo hanyar maganin wannan mummunar dabi'a ne kamar haka: 
1- Ya san cewa istimna’i yana daga zunubai da aka yi alkawarin azaba ga mai yin sa . 
2- Ya san cewa mutane zasu kyamace shi idan suka san yana yin sa . 
3- Ya taimaka wa kansa da yin azumi domin dawo da karfin iradarsa. 
4- Ya shagaltu da mudali’ar littattafai da nau’o’in wasanni kamar wasan gudu da tseran doki da sauransu. 
5- Iyaye su kula da tarbiiyar ‘ya’yansu tun farkon rayuwarsa ta yanda zasu kula da duk halayensu domin gyara da ba su tarbiiya ta gari. 
6- Dole ne al’umma da hukuma su bayar da muhimmanci na musamman kan sha’anin aure. 
7- Mai wannan halin ya duba irin bala’in da yake fada masa na cututtukan ruhi da na jiki kamar cututtukan fata, rashin jin cikakken dadin kusantar mace, rashin matsayi a al’umma saboda matsalar jijiyoyi da gajiyawar jiki da sauransu . 
Mu sani yawan duba littattafan hikima da na ilimi , da yawan tafiye-tafiye , da wasannin motsa jiki , da koyon harbe-harbe, da koyon sukuwar doki, da iyo a ruwa, suna daga cikin abubuwan da suke karfafa ruhin mutum , kuma suna kawo lafiyar jiki da ta ruhi da nishadi ga rayuwar mutum kamar yadda suna kawo farin ciki da annashuwa. 
Sha’awa Mai Yawa
Daga cikin shawarwari da aka bayar ga mai yawan sha’awar da ta fita daga al’ada, musamman wadanda sha’awarsu ta kai su ga lalacewa da babu wani haramun da ba zasu iya bari ba ta hanyar biyan bukatarsu ta haram, sun hada da: 
1- Tunawa da munin wannan hali, da abin da yake haifarwa na cututtukan ruhi da jiki da jawo wa mai wannan hali saurin tsufa da mutuwa a rayuwarsa ta duniya. 
2- Karya karfin sha’awarsa da yawaita yin azumi, da zama da yunwa, da karanta cin abinci . 
3- Kokarin ganin ya yi maganin duk wata hanya da takan iya kai shi ga jin sha’awa, kamar; tunanin abubuwan da sukan jawo masa sha’awa, da magana da mata, da kallon mata, da kebewa da mace, da kallon fila-filan banza, da duk wani abu da zai iya sanya shi jin sha’awa. 
4- Yin amfani da hanyoyin da zasu hana shi aikata haram da sha’awarsa kamar gaggauta yin aure da zaran ya samu dama; auren da’imi ne ko kuma na mutu’a. 
5- Tuna ni’imar da Allah yake ba wa wanda ya bar sha’awarsa ya ki aikata haramun da ita saboda Allah. 
6- Sanin cewa wannan siffa ce ta dabbobi shi kuwa mutum ne bai kamata ba ya zama kamar dabba domin shi an halicce shi ne domin kamala. 
7- Ya yi duba da tunani da lura zuwa ga ayoyin Kur'ani da ruwayoyi da suka kwadaitar da tuba suka kuma zargi mai wannan hali . 
8- Ya yawaita karatun Kur'ani da karanta litattafan ilimi na hikima, da yawaita addu’a da jin cewa shi zai iya barin wannan hali, hada da matakan da muka ambata a sama. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
Telegram)
hfazah@hotmail.com
www.haidarcenter.com
www.maiceto.com
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: