bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:14:12
Shi’a sun tafi a kan: cewa ginshiqan su ne; (1) miji da mata. (2) sigar sakin. (3) shaidu biyu (Sharhul Lum'a 5i, 11, Riyad 11, 168 – 75).
Lambar Labari: 182
(3)    SAKI (XALAQ)
Ginshiqan saki sun bambanta tsakanin mazhabobi, mazhabar Hanafi da Hambali sun tafi a kan ginshiqi guda xaya ne kawai. Wato sigar aiwatar da shi. A ra’ayin Shafi’i da Maliki kuwa, ginshiqan su ne: (1) Samuwar miji da mata. (2) Sigar sakin. (3) Niyya.(Fiqhu, 4, 280).
Shi’a sun tafi a kan: cewa ginshiqan su ne; (1) miji da mata. (2) sigar sakin. (3) shaidu biyu (Sharhul Lum'a 5i, 11, Riyad 11, 168 – 75).
Miji na iya sakin matarsa amma mace ba ta iya sakin majinta. Savanin xaura aure, kuma ba a neman yardar mata a saki.
Dole namiji ya zama cikin hankalinsa kuma baligi, kafin zartar da sakin da ya yi. Ya tabbata kuma ya zartu a hukunce a mahangar duk malaman mazhabobin nan in banda mahangar Hambali, kuma dole ya zama ba tilasta masa aka yi ba, a faxin dukkani malaman in banda Hanafi.
Hanbali ya tafi a kan cewa matashin da bai balaga ba amma ya san ma’anar sakin aure da sakamakon da zai haifar, zai iya sakin aure a kan kansa, Hanafi ya ce ko da an tilasta mutum a kan furta saki to sakin ya tabbata.(Fiqhu 4, 284). A ra’ayin da Shi’a suka yi tarayya da sauran mazhabobin, Shi’a sun qara da cewa dole mijin ya furta sigar sakin da kuma niyyyar yin sakin, duk da cewa shafi’i da maliki su ba su xauki wannan a cikin ginshiqin saki ba.(Sharhul Lum'a 5i, 14-21; Riyad, 11, 172).
Lalle ne matar ta zama `ya, wacce aka aura auren da'imi kuma mai amana, tun da babu zancen saki ga baiwa da matar da aka yi mutu'a da ita (a mazhabar Shi’a) ko kuma mazinaciya.
A cikion sigar saki dole namiji ya yi amfani da kalmomin da za su yi nuni zuwa saki kai tsaye ko ba kai tsaye ba, ko da yake Shi’a sun  tafi a kan cewa dole ayi amfani da kalmar saki (wacce shari'a ta sanya domin yin saki). Kurma zai iya sakin matarsa ta hanyar alama ko ishara. Maliki da Hanafi sun ce mutum zai iya sakin matarsa a rubuce.
Dole a furta sigar sakin sau uku ta kamar yadda za mu bayyana nan gaba:
Saki ya kasu kaso biyu, ya danganta da lokacin da mutum ya zava domin furta sigar: Sakin sunna wato 'saki na asali', wanda shari'a ta yarda da shi. Da Saki mara kyau 'na bidi'a' wanda aka hana.
Shi saki ko na sunna ne ko na bidi’a, ya danganta da yanayin tsarkin da matar ke ciki a lokacin da mijin ya furta sakin da yadda ya furta sigar. Yayin jinin haila ko biqi mace ba ta cikin tsarki kuma ba za ta tava zama cikin tsarki ba har sai jinin ya tsaya ta yi wanka. Kafin saki na sunna dole ya tabbata cewa ta kasance cikin tsarki kuma dole sai in mijinta bai sadu da ita ba bayan ta yi tsarkin. A faxar Shi’a, idan mace tana samun matsalar haila (mustaraba), wato tana samun tsaiko wajen ganin jini, za ta iya zama mai ciki ko kuma mara shi, a wannan halin dole mijinta ya jira har watanni uku domin ya tabbatar da cewa ba ta da ciki, sannan ya sake ta.(Riyad, 11, 171). Dole mijin ya furta sigar sakin a mabambantan lokuta kuma a mabambantan yanayoyi guda uku kamar yadda bayani zai zo a qasa.
Duk da cewa sakin aure na bidi’a haramun ne in banda wasu kevattantun hukunce-hukunce, amma a faxar wasu mazhabobin, zai iya tabbata.
Saki na bidi’a ya kasu daban-daban: daga ciki a kwai Sakin aure a lokacin da mace take. (1) cikin jinin haila (2) naquda. (3) sakin aure ta hanyar furta sakin har guda uku a lokaci xaya, a nan shafi’i ya tafi a kan ingancin wannan sakin.(Fiqhu, 4, 297). (4) sakin aure yayin da mace ta yi tsarki bayan haila, amma kuma aka samu jima’i kafin sakin, maliki ya ce: wannan sakin ba a hana shi ba kuma ba haramun be ne, sai dai an aikata (makaruhi).
Duk da cewa an hana saki na bidi’a, sunna sun ce furta sigar da aka yi ya isar wajen tabbatar da sakin da kuma zartuwarsa. Amma Hanafi da Maliki sun ce dole mijin ya komar da matarsa kuma ya xauki kansa a matsayin mijinta, idan duk da haka yana so ya sake ta, dole ya jira ta yi tsarki na biyu daga lokacin da ya furta sakin, sannan sai ya ce ya sake ta. Idan mutum bai komar da matarsa ba, to sakin ya tabbata, amma fa ba makawa wannan mutum ya yi zunubi, sai dai ba wani hukunci da za a yi masa a wannan duniya.( Ibid, 310).

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: