bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:18:40
Kafin saki ya zama na karshe, a wasu lokutan dole miji ya furta sakin a lokuta uku mabanbanta kamar yadda za a bayyana nan gaba. Ma’ana: saki na farko da na biyu suma saki ne,
Lambar Labari: 183
Shi’a sun tafi a kan cewa saki na bidi’a baya tabbata. Sakin bidi'a ya hada har da sakin da miji ya yi sau uku a cikin kalma daya a take.(Sharhul lum'a 5i, 31 – 32 Riyad, 11 176).
A wasu yanayin kuwa hukuncin ya saba, misali, mutum zai iya sakin matarsa ko wanne lokaci idan har ba jima’i tsakaninsu, ko kuma idan matar yarinya ce ba ta balaga ba, ko matar da ta daina haila da mace me ciki. A mazhabobi uku, wannan irin sakin ana daukarsa na sunna, Shafi’i da Hanbali kuwa sun ce ba sa cikin kashe-kashen saki. (Fikhu, 4, 305, da 307). A mahangar mazhabobin uku sun ce sakin da mace ta fare shi (khul'i da mubarat), saki dalilin rantsuwar kin takar mace, (ila’i) da sakin da Alkali ya umarta, ba su da sharuda na zahiri. Amma maliki da Shi’a sun  ce wadannan saki suna da sharudda na zahiri.(Ibid, 302 Sharhul Lum'a 5i, 36 – 37 Riyad 11, 176).
Kafin saki ya zama na karshe, a wasu lokutan dole miji ya furta sakin a lokuta uku mabanbanta kamar yadda za a bayyana nan gaba. Ma’ana: saki na farko da na biyu suma saki ne, sai dai ana iya kome (wato raj’i ne). Don haka saki ana iya kasa shi gida biyu: wanda ake kome da wanda ba a iya kome, shi sakin kome ba ya yiyuwa a irin wadannan sakin da za a ambata, ga su:
1) Sakin matar da mijinta bai tara da ita ba.
2) Sakin matar da ba ta balaga ba.
3) Sakin matar da ta daina haila.
4) Sakin da mace ta nema (khul’i da mubarat) a sake na (khul'i da mubarat).
5) Saki na uku bayan guda biyu na kome.
Mutukar aka saki mace (wato saki uku) mijin ba shi da damar sake aurar ta har sai ta auri wani sun tare (ya tade ta, ma'ana ya san ta a `ya mace), doh haka idan mijin ta na biyu ya sake ta to ta hallata ga mijin farko, mijin na biyu ana kiransa mahallil (wato mai hallataw ko mahalacci), kamar yadda ya gabata a baya, a wannan yanayin ba matsala idan matar da mijin suka yi alkawarin zama ko rabuwa. Bugu da kari ba a yarda a sanya sharadi yin saki a cikin auren ba, dole ne auren ya zama kamar yadda ake yin tabbaceccen aure. (kamar yadda yake yin aure yau-da-gobe). (Al-Kur'ani sura ta: 2 Aya ta: 230 yana cewa: "Idan wanin ku ya saki matar sa saki (3) to ta zama haramtacciya gare shi har sai ta yi wani auren, sannan kuma an saketa, to a wannan lokacin babu laifi suyi kome (wato ya mayar da ita)").  
Macen da aka saka sakin kome tana nan tamkar matar mijin da ya yi sakin domin mijin zai iya dawo da ita, ya yi jima’i da ita in ya so. Amma malikiyya sun ce dole ya kudurce niyyar dawowa da ita a zuciya kafin ya kusance ta, Shafi’i kuma ya ce dole ya gayawa ita matar kafin hakan ta faru.(Fikhu, 4, 435 – 41).
A wasu lokutan ya halatta a sanya sharadin da ka iya jawo rabuwar aure yayin daura auren. Misali, matar na iya sanya sharadin idan mijin ya kara wata matar to tana da ‘yancin ta kashe auren.
Duk da cewa mijin ne ke da hakkin sakin, amma matar tana iya neman saki ta hanyar khul'i da mubarta. Wadannan kalmomi suna kama da juna, duk da cewa sun saba da yanayin jina, domin shi "khul’i”, dole sai mace na cikin tsananin kiyayya ga mijin, shi kuwa "mubarat” sai an sami kiyayyar juna tsakanin su. A kowanne daga ciki mace tana amincewa za ta ba mijin wani adadi na kudi ko wani abu mai kima da za a iya chanza shi ya zama kudi. Dangane da mubarat kuwa, a fatawar Shi’a, abin da za ta ba shi ka da ya fi kudin sadaki, amma a "kul’i” ba a iyakance abin da za ta ba mijin ba. Wadannan nau’o’in sakin ba kome a cikin su. Amma a fadar Shi’a ba haka ba ne, su sun tafi a kan cewa; lokacin da take zaman idda, tana da damar karbo kayanta (wato abin da ta ba shi) kuma mijin na da damar yin jima’i da ita. (Sharhul Lum'a 5i, 104 – 07 Riyad, 11, 196). Hambali ya tafi a kan cewa khul'i wani yanayi ne na warware aure, ba saki ba ne. (Fikhu 4, 424).
Tun da wadannan nau'o'in na saki, disa hakika wani nau'i ne na yarjejeniya; don haka yana bukatar Kalmar kullawa da kuma ta karba, lalle ne mace ta fadi wani abu makamancin haka: 'ka sake ni amaimako abu kaza da kaza', shi kuma mijin sai ya ce: 'na yarda' ko 'na sake ki'. Sunna sun tafi a kan cewa miji na iya yin amfani da ko wace irin kalma a wajen yin sakin, kamar kalmar saki ko kuma wata kalma da asalin ta ke kumawa ga kuhl'i, ko mubarati. Shi'a sun ce dole ne ayi amfani da ita kanta kalmar sakin. (Sharhul Lum'a, 5i 87 – 89 da 111 – 13; Riyad 11, 107).      
Mazhabobin sunna sun halatta cewa; wani mutun da (ba mijin ba ba matar ba) na iya farar 'sakin kul’i', ma’ana, ya dauki nauyin biyan kudin kul’in, domin mijin ya saki matarsa. Amma Shi’a sun haramta wannan.
Mazhabobin nan sun tattauna dalla-dalla a kan irin dukiyar ko kayan da za a iya bayarwa a kan 'kul’i' da mubarat, inda suka sassaba a kan wasu `yan kananan abubuwa. A takaice dole su zama na halak, kuma suna da daraja a kan kansu, kamar abubuwan da suka dauka a matsayin sadaki. In ba haka ba, sakin zai tabbata, amma bisa sabnin cewa ko sakin na kome ne ko ban a kome ba ne.(Sharhul Lum'a 5i, 90 – 95).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: