bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:28:10
Shi: lamiri ne na namiji tare da cewa Alllah (SW) ba namiji bane kuma ba mace ba, a yaren larabci a kan yi amfani da lamirin namiji don kiran sunan sa maɗaukakin sarki, harma mala'iku da sauran su don girmamawa.
Lambar Labari: 184
سورة الإخلاص
SURTUL IKHLAS (SURA TA 112)
Sura ce da ake ce mata suratut tauhid, surace mai muhimmanci gaske cikin littafi mai tsarki, tana da ayoyi huɗu, haka nan yana daga cikin falalar ta cewa karanta ta sau uku na daidai da ladan karanta al'ƙurani mai girma kamar yadda yazo daga wasu ruwayoyi.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Da sunan Allah mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ (1)
Ce shi Allah ɗaya ne.

Shi: lamiri ne na namiji tare da cewa Alllah (SW) ba namiji bane kuma ba mace ba, a yaren larabci a kan yi amfani da lamirin namiji don kiran sunan sa maɗaukakin sarki, harma mala'iku da sauran su don girmamawa.
Shi: arifai na fassara ta da cewa wata marhala ce ta farko a samuwarsa maɗaukakin sarki a duniyar huwiyya duniyar samuwar da ba wanda zai iya bayanin ta baki ɗayan halitta sai shi tal, don haka ba mai labarin ta daga annabawa, mala'iku dss, sabida bamu da ikon sanin ta, a irfani haramun ne yin magana kanta sabida baka da sadarwa da ita ta kowacce hanya.
Shi: yahudawa na kiranta yahwa ta inda su ka iya fitar da sunan yahoo daga wannan kalma, a wajan su ba mai furta wannan kalma sai mai tsarki don haka ma idan mutum ya furta sai ya yi kaffarar wanka, amman wajan mu musulmai ba wannan, ma'anar ta dai na nuni da cewa: shi ne wanda ya mamaye tare da sallaɗuwa kan dukkan komai babba da ɗarami duk ba bambanci.
Ahad na nufin bashi da ɓangarori, wahid na nufin shi kaɗai ne a samuwa ba wanda su ke tare da shi a matsayin samuwar sa, duk da cewa ahad ya bayyana kusan a matsayin wahid nan wajan.

اللَّهُ الصَّمَدُ (2)
Allah shi ne abin nufi da buƙata.
Assamad: shine wanda komai ke jingina zuwa gare shi, duk wani abu na buƙatar sa, farkon samuwa, mai ɗauke da komai, duk samad na iya ɗaukar wannan ma'ana, ma'ana ce kusa da ƙayyum, duk da cewa a wata ma'anar tafsiri ce ta ahad.

لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ (3)
Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba.
Duk da yake haihuwa a nan na nufin ba abinda ke fita daga shi, sannan shi ma baya fita daga komai ba, ba kamar yadda mu ka fi taƙaituwa da haihuwa irin ta jiki ba, ma'ana ce mai faɗin gaske, ɗaya daga misalai kamar haske da ke fita daga fitila, ko mu iya sanya shi cikin tunanin mu (kwakwalwar mu) mu san shi haƙiƙanin sani.

وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ (4)
Wani bai zama tamka/tsara gareshi ba.
Idan aka samu tsaran sa ya samu iyaka kenan, shi kuma ba mai iyaka bane.


Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: