bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:33:06
Kadaita Allah wani abu ne wanda dukkan annabawan da Allah ya aiko mana wannan duniya su ka hadu a kan sa, duk sun hadu kan kalma daya, ta kadaita Allah,
Lambar Labari: 185
IBNI TAIMIYYA, TARIHIN SA DA AKIDUN SA A DUNKULE
Tauhidi a ibada akida ce ta dukkan 6angarorin muslmai ba savani cikin ta kafin a haifi Ibni Taimiyya a shekara ta 661 bayan hijira a garin Harran cikin Ethiopia, wato bayan faduwar daular Bagdad da shekara biyar.*
Kadaita Allah wani abu ne wanda dukkan annabawan da Allah ya aiko mana wannan duniya su ka hadu a kan sa, duk sun hadu kan kalma daya, ta kadaita Allah, musamman idan ka dubi Annabi Ibrahim (AS) wanda dukkan addinan nan uku (yahudanci, kiristanci da musulunci) na jingina kansu zuwa gare shi.
Don haka duk wanda zai danganta kansa zuwa wadannan addinai dole ya dauki kalmar kadaita Ubangiji a ingantacciyar koyarwa, wannan kalmar "La'ilaha ilallahu" ta zama taken musulunci, abun nufi "babu wani Ubangiji sai Allah madaukaki" wato shi kadai ne ya cancanci a bauta masa.
Musulmai na da sa6ani kan wadansu abubuwa a tsakanin su, wannan kalma na daga cikin dayan abubuwan da su ka hadu a kanta ba sa6ani, sannan dukkan usulmai sun hadu kan Imani da ceton waliyyan Allah da girmama kaburburan su.
hakan ne ya sanya ma a wannan lokacin kahajjata yayin aikin hajji na yin carbi da kasar kabarin Sayyadina Hamza shugaban shahidai da ke makabartar baki'a, haka halin musulmai ya ke a wancen zamanin har zuwa karshen karni na takwas, a lokacin ne wani mutum mai suna Ahmad Bin Taimiyya ya fara fito na fito da wasu akidun da musulmai su ke a kai a wancen lokaci, ya ke nuna cewar imani da wadannan abubuwa kan fitar da mutum daga Imani zuwa shirka kamar yadda mu ke gani a yau, ya yi imanin akwai ceto a lahira amman haramun ne ka nema daga wajan wani waliyyi tun daga nan duniya.
Ku biyo mu a hankali, nan gaba daya bayan daya za mu dauki wadannan 6atattun akidu na Ahmad Ibni taimiyya daya bayan daya mu yi bayanin su, da yadda kurani mai girma da sunnar Manzo (SAW) su ka tabbatar da su.
Bincike kan rayuwar Ibni Taimiyya da mawuyacin halin da musulmai ke ciki na da muhimmancin gaske domin mu dauki darasi kan abubuwan da su ka faru daga al'ummar da ta gabata.
Ahmad Ibni taimiyya ya zo da wannan ra'ayin nasa na raba kan musulmai ne a daidai lokacin da musulmai ke matukar bukatuwa zuwa ga hadin kai sabida samun kansu cikin tsananini hare – hare daga kiristoci da Magul.
FARKON KARNI NA HUDU ZUWA RABIN KARNI NA BIYAR
Farkon karni na hudu zuwa tsakkiyar/rabin karni na biyar bayan hijira wani lokaci ne mai hadarin gaske a tarihin musulunci, a wannan lokaci ne manya – manyan mutane da su ka yi wa musulunci Aiki su ka bayyana, kamar su Ibni Sina, Abu Raihan Biruni, Firdausi, Sahib Bin Ubbad, Nizamul Mulki, Dusi da sauran su, wadanda su ka taka rawa a fanooni daban na ilimi kamar adabi da abinda ya shafi siyasa, kimiyya da sauran 6angarorin ilimi daban – daban, sakamakon haka ne mu ka samu karfi da damamar bayyanar da ci gaban musulunci a idon duniya, kamar yadda yammacin duniya su ka ambaci lokacin da zamanin sake raya musulunci.
Amma abin mamaki bayan shudewar wannan zamani sai ya zama duniyar musulunci ta samu rkice – rikicen addini da siyasa wanda ke cike da mu a yau, sakamakon haka ne mu ka manta da manyan mutanen da su ka yi wa addini aiki, wannnan ya sanya tauraron da ke haskaka musulunci a idon duniya ya dusashe.
Hadin Kan Kiristoci da masu Bautar Gunki
A yammacin duniya mabiya addinin kiristanci wadanda basu manta da cin nasarar musulmai da su ka yi a Andulus (Spain) ba, da yadda musulunci ya ci gaba a wannan nahiya, sai su ka dauni niyyar fansa kan musulmai a wannan nahiya sakamakon sun fahimci musulmai sun samu rauni a tsakanin su, sakamakon rikicin da ke faruwa tsakanin su na siyasa da akida, sakamakon haka ne a karshen karni na biyar shugaban cocin katolika da ya ke a Rom wanda ke shugabancin kiristocin duniya ya yi uamrnin kaiwa musulmai hari a Palasdinu wato al'kiblar muslmi ta farko, sakamakon haka ne dubban daruruwan kiristocin duniya ke zaune a yammacin duniya su ka yo ca domin amsa kiran wannan shugaban kiristoci a wannan lokaci domin ya tayar musu da tsohuwar gabar su kan musulunci addinin kadaita Allah (SW), su ka mayar da Kudus wani waje na kisan musulmai, yakin da ya shahara tsakanin kiristoci da musulmi ya dauki tsawon shekara 200 ana gwabzawa, ya jawo kisa da raunata dubban daruruwan mutane musulmi da kiristoci, wannan yaki ya fara daga shekara ta 1095 – 1291, wato shekara 196.
Kashi na Bakwai na nan tafe in Allah ya so

Don neman karin bayani kuna iya duba Littafin Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: