bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:36:24
wacce itace cibiyar musulunci a wannan lokacin tare da kashe dubban musulmi, a sannan ne ya kawo kashen shugabancin Abbasiyawa a shekara ta 656BH,
Lambar Labari: 186
Wani babban abun baki ciki bayan musulmai basu murmure daga yakin da su yi na Kods tsakanin su da kiristoci ba, sai ga Magul karkashin jagorancin Cangiz su ka kawo wa al'ummar musulmai hari ta yadda duk abinda su ka hadu da shi a kasashen muslmai sai sun ga bayan sa ko su dauka a matsayin ganima da bursunan yaki, bayan shekara hamsin da wannan jikan Cangiz mai suna Holako ya kaiwa Bagdad hari wacce itace cibiyar musulunci a wannan lokacin tare da kashe dubban musulmi, a sannan ne ya kawo kashen shugabancin Abbasiyawa a shekara ta 656BH, bai tsaya a nan ba sai ya jagoranci rundunar sa zuwa Sham (Etiopia), ya kai hari kan garuruwan Halab da Mausil ya maimaita abinda ya yi a Bagdad a shekara ta 657 – 660, a daidai wannan lokaci Misra (Egypt) da Sham na matukar fuskantar barazar hare – hare daga rundunar kiristoci ta yadda wani lokacin rundurar kiristoci kan yi dab da shiga Al'kahira babban birnin Misra, mutuwar babban sarkin Magul mai suna Mungokan ya sanya holako ya dawo baya da zuwa Iran, da shan kashin da Holako ya gamu da shi a Palastin, wanda ya maimaita irin abun da Jalut ya hadu da shi a Palastin, banda haka da ba a san ya Misra zata kasance ba.
Wannan hare – haren da Magul su ka yi ta kaiwa daulolin musulmai a farkon karni na bakwai ya baiwa kiristocin yammacin duniya damar kai hare – hare kan daular Andulus cibiyar musluncin turai, don haka ne ma a shekara ta 609 – 889BH su ka fara kai hare – haren su kan Andulus sabida mugun nufin su na shafe duk wata alama ta musulunci a wannan nahiya, a duk tsawon lokacin hukumar Magul sarakunan kasashen turai na kai kawo tsakanin su da masarautar Magul, sabida taimakekeniya tsakanin su don gamawa da al'ummar muslmai, sannan bugu da kari matar holako, commandan sa da ke yakar sham, wannan ya kara fito mana a fili cewar sun yi taimakekeniya tsakanin juna don gamawa da musulmi.
Haka nan sarakuna magul da su ka gaji Holako sun dora kan abinda ya bari na yakar garuruwan musulmi, Aba Khakan da kuma magajin Holako wanda ya yi zamani a shekara ta (663 – 670)BH shi ma ya auri yar sarkin Rom wacce itace babbar daular kiristoci a wanna zamani, ya kuma hada kan sa da sarakunan Faransa da Ingila don yakar musulmi, ta haka ne su ka kai hari zuwa Sham da Misra wadanda su ne manyan garuruwan muhimmai na musulunci a wannan lokacin, bayan Aba Khakan an samu dan sa wanda ya fi shi mugunta mai suna Argun wanda ya yi zamani tsakanin shekara ta (683 – 690)BH ta hanyar bin shawarar wazirin sa wanda ya ke bayahude nemai suna Sa'adu Daula Abhari, har ma ya bashi shawarar ya kai hari Makka ya mayar da dakin Ka'aba wajan bautar gumaka, da haka ne ya ci gaba da tu6e manya – manyan shugabannin musulunci da kashe wasu daga cikin su, da tanadar rundunar da zata kai hari garuruwan Hijaz don cimma wannan mugun nufin, amman cikin ikon Allah bai samu damar aiwatar da wannan nufin ba, wani ikon Allah sai Argon ya kamu da rashin lafiya sannan aka kashe bayahuden wazirin sa, ta haka Allah ya kawo karshen wannan fitinar ta su.
Gazakhan shahararren daya daga cikin sarakunan Ilkhani (Magul) wanda ya musulunta amman duk da haka bai bar tunanin kaiwa Misra da Hijaz hari ba, sabida haka ne tsakanin shekara ta (699 – 702)BH garuruwan sham su ka hadu da yaki mai tsanani wanda ya auku tsakanin sarakunan Magul da na musulmi na Misra, sannan duk nasarar da sarakuna Magul da su ka yi a kan musulmi ya zamo matsayin taya murna da karin karfi ne ga kiristocin da su ke yakar musulmi.
A daidai wannan lokacin ne shi kuma Ahmad ibni Taimiyya ya fara yada wadannan munanan akidu na sa, sabida haka ne manyan malaman musulunci (na sunna da shia) su ka tashi tsaye a wannan lokacin domin yakar wadannan munanan akidu wadanda su ka haifar ba babbar 6araka tsakanin al'ummar muslmi 1.
Domin wannan lokaci na bukatar wani mai karfin zuciya da zai tashi tsaye domin ganin musulmai sun hada kan su wuri daya don ganin sun samu nasara kan mushrikai da kiristocin da ke yakar su a wancen zamanin, amman abun bakin cikin sai duniyar musulmai ta hadu da masifar akidun Ibni Taimiyya.
1-    Don neman karin bayan kan sarakunan Magul a littafin Abbas Ikbal altiyani mai suna Tarihin Magul safuka na 191, 197, 202, 204, 214,237, 245 da 266.
Kashi na Takwas na nan tafe in Allah ya so

Don neman karin bayani kuna iya duba Littafin Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: