bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:40:54
An rawaito cewa yayin Manzo (SAW) ya ga jaririn watan Sha'aban sai ya umarci mai kira ya yi kira cikin Madina cewa: ya Ahalin Yathrib! Ni xan aike ne daga Manzo (SAW) zuwa gareku,
Lambar Labari: 187
اعمال شهر شعبان

مستحبات شهر شعبان العامة
- روي أن رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم كان إذا رأى هلال شعبان أمر مناديا ينادي في المدينة: يا أهل يثرب! إني رسول رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) إليكم ألا إن شعبان شهري، فرحم الله من أعانني على شهري، ثم قال أمير المؤمنين (عليه السلام): ما فاتني صوم شعبان منذ سمعت منادي رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) ينادي في شعبان ولن يفوتني أيام حياتي صوم شعبان إن شاء الله تعالى .
- أن يقول في كل يوم سبعين مرة:
أَسْتَغْفِرُ اللهَ وَأَسْأَلُهُ التَّوْبَةَ.
    
- أن يقول في كل يوم سبعين مرة قائلا:
أَسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لا إِلَهَ إِلا هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ الْحَيُّ الْقَيُّومُ وَأَتُوبُ إِلَيهِ.
وفي الروايات أن من استغفر في كل يوم من هذا الشهر سبعين مرة كان كمن استغفر الله سبعين ألف مرة في سائر الشهور .
- أن يتصدق في هذا الشهر ولو بنصف تمرة ليحرم الله تعالى جسده على النار .
سئل الإمام الصادق عليه السلام ما ثواب من صام يوما من شعبان فقال: الجنة والله؛ فقال الراوي ما أفضل ما يفعل فيه قال: الصدقة والإستغفار، ومن تصدق بصدقة في شعبان رباها الله تعالى كما يربي أحدكم فصيله حتى يوافى يوم القيامة وقد صار مثل أُحُد.
- أن يقول في شعبان ألف مرة:
 لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَلا نَعْبُدُ إِلا إِيَّاهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ.
ولهذا العمل الشريف أجر عظيم ويكتب لمن أتى به عبادة ألف سنة .
- أن يصلي في كل خميس من شعبان ركعتين يقرأ في كل ركعة بعد فاتحة الكتاب (قل هو الله أحد) مائة مرة، فإذا سلم صلى على النبي (صلى الله عليه وآله وسلم) وآله مائة مرة، ليقضي الله له كل حاجة من أمور دينه ودنياه، ويستحب صيامه أيضاً ففي الحديث تتزين السموات في كل خميس من شعبان، فتقول الملائكة: إلهنا إغفر لصائمه وأجب دعائه . وفي النبوي من صام يوم الإثنين والخميس من شعبان قضى الله له عشرين حاجة من حوائج الدنيا وعشرين حاجة من حوائج الآخرة .
- الإكثار في هذا الشهر الشريف من الصلاة على محمد وآله .
عن الرضا عليه السلام قال: من صام ثلاث أيام من آخر شعبان ووصلها بشهر رمضان كتب الله تعالى له صيام شهرين متتابعين . وعن أبي الصلت قال: دخلت على الإمام الرضا عليه السلام في آخر جمعة من شعبان فقال لي: يا أبا الصلت! إن شعبان قد مضى أكثره، هذا آخر جمعة فيه فتدارك فيما بقي تقصيرك فيما مضى منه، وعليك بالإقبال على ما يعينك وأكثر من الدعاء والإستغفار وتلاوة القرآن وتب إلى الله من ذنوبك ليقبل شهر رمضان إليك وأنت مخلص لله عز وجل ولا تدعن أمانة في عنقك إلا أديتها ولا في قلبك حقدا على مؤمن إلا نزعته ولا ذنبا أنت مرتكبه إلا قلعت عنه واتق الله وتوكل عليه في سرائرك وعلانيتك ومن يتوكل على الله فهو حسبه إن الله بالغ أمره قد جعل الله لكل شيء قدرا، وأكثر من أن تقول في ما بقي من هذا الشهر:
اَللّـهُمَّ اِنْ لَمْ تَكُنْ غَفَرْتَ لَنا فيما مَضى مِنْ شَعْبانَ فَاغْفِرْ لَنا فيما بَقِيَ مِنْهُ.
فإن الله تبارك وتعالى يعتق في هذا الشهر رقابا من النار لحرمة هذا الشهر .

AYYUKAN WATAN SHA'ABAN
MUSTAHABBAN WATAN SHA'ABAN BAKI XAYA
- An rawaito cewa yayin Manzo (SAW) ya ga jaririn watan Sha'aban sai ya umarci mai kira ya yi kira cikin Madina cewa: ya Ahalin Yathrib! Ni xan aike ne daga Manzo (SAW) zuwa gareku, ku sanio cewa watan Sha'abana wata na ne, Allah ya yi rahama ga duk wanda ya taimake mu cikin wannan watan, sannan Imam Ali (AS) ya kasance yana cewa: azumin watan Sha'aban bai tava wuce ni ba tunda na ji mai yekuwar Manzo (SAW) yana faxa cikin Madina, kuma in Allah ya yadda cikin rayuwa ta wani azumin Sha'aban ba zai wuce ni daga cikin sa ba.
- Mutum ya karanta astagfirullaha wa as'aluhuttauba (أَسْتَغْفِرُ اللهَ وَأَسْأَلُهُ التَّوْبَةَ) Qafa saba'in kowace rana.
- Mutum ya karanta astagfirullahallazy la'ilaha illahuwar rahmanurraheemul hayyulqayyum wa atuubu ilaihi (أَسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لا إِلَهَ إِلا هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ الْحَيُّ الْقَيُّومُ وَأَتُوبُ إِلَيهِ) qafa saba'in kowace rana.
Ya zo cikin ruwaya cewa duk wanda ke yin istigfari cikin kowace rana cikin wannan wata sau saba'in kamar yana yi yi ne a kullum tsawon sauran watannin cikin wannan shekara.
- Ya yi sadaqa cikin wannan watan koda kuwa da rabin dabino ne da niyyar Allah ya haramtawa wuta jikin sa.
An tambayi Iman Sadiq (AS) meye ladan wanda ya azumci rana cikin watan Sha'aban sai ya ce: al'janna ce wallahi, mai ruwaya ya ce menene ainda ya fifici komai da zai yi cikin wannan wata sai ya ce: sadaqa da istigfari, wada ya yi sadaqa cikin sha'aban Allah (SW) zai ta raya ta kamar yadda xayan ku ke rayuwa har su haxu lokacin wafatin sa zuwa ranar alqiyama ya zama abin faxa.
- Ya karanta la'ilaha ilallahu wala na'abudu illa iyyahu mukhlisina lahuddeen wa lau karihal mushrikuun (لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَلا نَعْبُدُ إِلا إِيَّاهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ) sau xari.
Akwai lada babba ga duk wanda ya aikata wannan maxaukakin aiki za'a rubuta wa duk wanda ya yi ladan ibadar shekara xaya.
- Ya yi salla raka'a biyu cikin kowace alhamis xin cikin sha'aban, cikin kowace raka'a ya karanta Fatiha da Qulhuwallahi (suratul ahad) qafa xari, idan ya yi sallama sai ya yi salati ga Manzo (SAW) xari, Allah zai biya masa buqatun sa na duniyar da da addinin (lahirar) sa, an so ma ya yi azumi domin ya zo cikin hadisi cewa sama na adontuwa cikn kowacce alhamis xin sha'aban, sai mala'iku su ce: ya Ubangijin mu ka gafartawa duk wanda ya azumci wannan rana ka amsa buqatun sa. Cikin Nabawy kuma ya zo cewa: duk wanda ya azumci ranar litinin da alhamis na watan sha'aban Allah zai biya masa buqatu ishirin daga buqatun duniya ishirin kuma daga na lahira.
- Yawaita salatin Manzo (SAW) da iyalan sa (AS).
Ya zo daga Imam Ridha (AS) cewa: duk wanda ya azumci kwanakin qarshe na wata sha'aban ya sadar da ita zuwa Ramadan Allah zai rubuta masa ladan azumin wata biyu a jere. Daga Abus Salt ya ce: na shiga wajan Imam Ridha (AS) ranar Juma'ar qarshen watan sha'aban, sai ya ce min Ya Abas salt! Haqiqa mafiya yawan kwanakin sha'aban sun wuce, wannan ce juma'ar qarshe a cikin sa, ka samu abinda ya rage na daga cikin sa, kai aikata abinda zai samu cikin sa, wanda mafi yawan sa Addu'a ne da istigfari da Karatun Al'qurani, Allah zai tavar da zunuban ka don ya karvi ramadanan ka kana mai tsarkakewa ga Alahha mai girma da buwaya, kada ka bar wata amana a kanka har sai ka bayar da ita, kada kuma ka bar qulli a zuciyar ka ga mumini har sai ka cire shi, kada ka aikata wani abu da ka san zunubi ne, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron sa a sararin ka da zuciyar ka, haqiqa duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa, Allah ya isar masa lamurran sa,Allah ya sanya komai gwargwadon qaddarar sa, ka yawaita karanta wannan addu'ar cikin abinda ya rage maka na cikin wannan watan:
Allahumma in lam takun gafarta lana fi ma madha min sha'ban fag fir lama fi ma baqiya minhu (اَللّـهُمَّ اِنْ لَمْ تَكُنْ غَفَرْتَ لَنا فيما مَضى مِنْ شَعْبانَ فَاغْفِرْ لَنا فيما بَقِيَ مِنْهُ). Haqiqa ubangiji maxaukakin sarki ya na 'yanta bayi daga wuta cikin wannan wata don girman watan.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: