bayyinaat

Published time: 25 ,January ,2017      12:13:32
Wahabiyawa da salafawa Magana kan wadannan mutane na da matukar muhimmanci a yau, domin kuwa jama'a ne da ke gudanar da aikace – aikace iri – iri da su ka ja hankalin duniya musamman a kafafen yada labarai, wahabiyawa da salafawa suna da sunaye daban – daban a duniya, Magana kan sun a da muhimmanci sabida yawan hujumi da su ke kan sauran 6angarorin musulman da suka sa6a musu, musamman shia da darikun sufaye tare da kafirta su.
Lambar Labari: 19
Bismillahir rahmanir Rahim, Alhamdu lillahi rabbil Alamiin, Wasallallahu Ala Muhammadin wa a-lih

Wahabiyawa da salafawa Magana kan wadannan mutane na da matukar muhimmanci a yau, domin kuwa jama'a ne da ke gudanar da aikace – aikace iri – iri da su ka ja hankalin duniya musamman a kafafen yada labarai, wahabiyawa da salafawa suna da sunaye daban – daban a duniya, Magana kan sun a da muhimmanci sabida yawan hujumi da su ke kan sauran 6angarorin musulman da suka sa6a musu, musamman  shia da darikun sufaye tare da kafirta su.
Cikin maganganun da zamu yi ya kamata a san su domin wannan ne zai taimaka wajen bada kariya ga shianci da Darika ya kuma amsa shubuhohin da su ke dauke da shi kan sauran musulmi, musamman shia da darika da su ke kafirtawa da sauran musulmi, wahabiyawa musulmi ne wajan sauran musulmai, duk da dais u na kafirta duk wanda ba su ba cikin musulmi, za kuma mu ji dalilan su da yawa da su ke kafirta sauran musulmai da su, a Nigeria wahabiyawa na da sunaye daban – daban sabida samuwar su a kungiyoyi daban – daban, kamar: Jama'atu Izalatul Bidia wa ikamatus sunna {JIBWIS}, Jama'atud Da'awa, Adda'awa Group, Assalafiyya, Alfur'kan, sannan da yawa daga cikin JTI {Jama'atu Tajdidil Islami wasun su wahabiyawa ne, akwai kuma wahabiyawan da ke zaman kansua ba tare da an jingina su da wani 6angare ba, kamar su Ja'afar Mahmud da su Aminu Ibrahim Daurawa, Kabiru Gwambe da makamantan su da yawa daga salafawa da wahabiyawa, Wahabiyawa/salafawa sun yi tasiri a wurare da yawa da ma'aikatun gwamnati, sakamakon kama tashashen yada labarai da makarantu da sauran ma'aikatu a Nigeria, sun a tare da manyan ma'aikata da madafun iko ko dai wahabiyawa ne ko kuma sun cika da tuanin wahabiyawa sabida yadda su ka kewaye su har da kamar gwamnoni, ministoci da masu manyan mukamai daban – daban, har ta kai ka ga miutum na Magana sak irin ta wahabiyawa kai kace bawahabiye ne sabida ya dauki abubuwa daga malaman wahabiyawa yana tunani yanda wahabiyawa ke tunani ba tare da ya lura ba, ya kuma dauka cewa wannan abun shine musulunci sabida rashin sanin hakikanin addini da inda ya dosa, wahabiyaci duk da asalin sa daga Hambalanci ne amman a yau kusan sun tashi daga Hambalanci sabida kare – kare masu yawa da su ka samu sais u ka zama wani 6angare na daban, har yanzu akwai hambalawa na daban kamar kurdawa za mu ga Hambalawa a cikin su, har a Saudiyya da wasu daga mutanen Egypt, sun samu wannan suna na wahabiyawa sabida sunan Muhammad bin Abdulwahab wanda ya assasa daular Saudiyya, kowa ya san tarihin su da yanda turawan England su ka taimaka masa wajan kafa wannan dauaa ta hanyar taimakawa sarakunan A-li Sa'uud, suka sanya musu sharudda cewa duk wani malamin addini kada ya shiga lamarin siyasa shugabanni kuma kada su shiga lamarin malamai, sabida haka kowa ya kare kowa, malami yak are siyasa siyasa kuma ta kare malami, shi ya sa yanzu haka lamarin ya ke a Saudiyya.
Kashe – kashen wahabiyawa/salafawa a duniya na da aiyyuka kala – kala, za mu ga wasun su na daukar makami wasun su kuma basa dauka, masu daukar makami su ne wadanda su ka yi adopting din tunanin brotherhood {ikhwan} sais u ka zama hadari, sabida sun a ganin cewa dole su kau da hukuma don su kafa daular musulunci a kowacce kasa ga kuma tunanin wahabiyanci na kafirta mutane, sabida haka idan wannan abu biyun su ka hadu dole ka ji tashin bomb da bindiga, wannan mummunan aikin na kasha – kasha ne ya sanya zaka sun jawo hankalin duniya, Taliban dubi Al'kaida wadanda a yau zaka gas u na da karfi a wasu kasashen musulmi irin su, Afganistan, Yemen, Syria, kuma wannan Al'kkaidar dai itace ta kara rabuwa a wadannan kasashen da su ke musamman a Syria, wasu sun zama Jaishush Sham, wasu ISIS wasu su ka zama Jauhatun nusra da Al-shabab a Somalia haka nan ma wasu a Nigeria {Jama'atu ahlus sunna lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko haram}sai ya zama a ko ina akwai wahabiyawan da basu riki makami ba, kamar a Nigeria wadanda mu ka kawo a sama har da ma wadanda bamu kawo ba kamar Jama'atu Nasrul Islam kungiya ce da kae kiranta da kungiyar musulmi amman baki daya tunanin wahabiyanci/salafanci ne ke aiwatar da ita, shugaban ta na kafirta Shia da dukkan sauran 6angarorin musulmi alhalin ya kamata a ce kowanne musulmi na ciki sabida kiranta da sunan kungiyar muslmai, gasu nan dai dayawa, amman dukkanin su sun a komawa zuwa ga mutum daya shi ne Ibni Taimiyya, sabida dukkan wadannan kungiyoyi idan za su yi wani aiki zaka ji su ce Ibni taimiyya ya ce domin shi ne hanyar su zuwa ga sanin gaskiya, don haka sanin Ibni Taimiyya da Muhammad Ibni Abdulwahab da abinda su ke cewa [fatawoyin sa] ya zame mana dole.
Kashi na uku na nan tafe in Allah ya so

Ibrahim Al'mu'azzam
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: