bayyinaat

Published time: 10 ,August ,2018      00:05:06
Tabbas waxannan manyan tare da sun tabbatar Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta jam’in tarawihi ba,
Lambar Labari: 199
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA NAI JIN KAI
ALLAH NE YA KEVANTA DA SHAR’ANTAWA
Tabbas waxannan manyan tare da sun tabbatar Manzon Allah (s.a.w) bai sunnanta jam’in tarawihi ba, sun bayyana cewa Halifa ne ya sa wa mutane liman, ma’anar hakan kuwa ka ga wato yana da haqqin sunnantawa da shar’antawa kenan, hakan ya savawa ijma’in al’umma, don ba wani mutum da yake da haqqin kutsawa cikin al’amarin shari’a, bayan kammalata, saboda ayar da Allah (TA) ya ce: (Yau na cika muku addininku na cika muku ni’ima ta na yardar muku da Musulunci shi ne Addini)( ). Maganarsa ta savawa Qur’ani da Sunna, tabbas shar’antwa haqqin Allah ne (SWT) bai fawwalawa kowa ba, Annabi mai girmamam ai isar da saqo ne.
Bugu da qari idon an bawa Halifa damar shar’antawa da sunnantawa, to me zai hana ragowar Sahabbai ma ba za a basu hakan ba, tare da cewa wasunsu sun fi shi karatun Qur’ani, kamar Ubayyu xan Ka’ab, Zaidu bn Sabit kuma ya fi shi sanin ilimin gado, Aliyun bn Abi Xalib kuma ya fishi ilimin da iya alqalanci. Da duk an basu haka da fasadi ya yaxu, kuma za a rasa tsari a cikin al’amarin Addini, da addinin ya zama abin wasa kamar bol a hannun waxanda ba ma’asumai ba.
Amman riqo da hadisai biyu ko da sanadinsu ya inganta lallai tabbas basa nuna manufar cewa suna da haqqin shari’antawa, kai suna ma nuna wajabcin koyi da su ne, saboda suma suna dogara ne da sunnar Annabi mai girma, ba wai suna da haqqin sunnantawa ba ne.
Tabbas ya bayyana daga abin da Suyuxi ya ruwaito daga Umar bn Abdil Aziz ya kasance yana qudurce cewa Halifofi suna da haqqin sunnantawa, yake cewa: Hajib xan Kghalifa ya ce na ga Umar xan Abdul Aziz yana huxuba a lokacin da yake halifanci, sai ya ce: Tabbas abin da Manzon Allah (s.a.w) da abokansa biyu suka sunnanta shi ne Addinin da za mu yi riqo da shi mu kai gare shi, abin da wasunsu suka sunnanta kuwa za mu jinkirtar da shi. Ka dai ji.
A bisa dukkanin qaddarawa, tabbas Allah (SWT) bai fauwala al’amarin addininsa na shar’antawa da hukuntawa ga wata hanyar da ba ta wahayi ba, a kan haka ne ma Shaukani ya ke cewa: "Gaskiyar magana maganar Sahabi ba hujja bace, tabbas Allah (SWT) bai aiko wa wannan al’ummar kowa ba sai Annabinmu Muhammad (s.a.w), ba mu da kowa sai Manzo xaya, Sahabbai da waxandfa suka zo bayansu suma an xora musu bin shari’arsa da Qur’ani da Hadisi, duk wanda ya ce ana da wata hujja a cikin Addinin Allah ba su biyun nan ba, to tabbas ya faxi abin da bai tababta a cikin Addinin Allah ba, ya kuma tabbatar da shari’ar da Allah bai yi umarni da ita ba”.( )
Tabbas Qasxalani ya naqalto daga Ibnu Tin da waninsa cewa: Tabbas Umar ya yi istinbaxin haka daga taqririn Annabi: Wato tabbatarwar Manzon Allah (s.a.w) ga waxanda suka yi Sallah tare da shi a waxancan dararen, duk da yake ya qyamaci hakan don tsoron kar a farlanta musu. Bayan rasuwar Annabi (s.a.w) sai aka sami kaucewar tsoron farlantawar, sai hakan ya qarfafa a wajen Umar don saboda savanmi yana haifar da rarrabuwar kalma, kuma saboda haxuwa kan mutum xaya ya fi jawo nishaxi ga mafi yawan masu Sallah.( )
Akwai mulahaza a kan haka da farko dai; tabbas abin da ya faxa a qarqashin maganarsa  zai halattawa mtuane haxuwa kan liman xaya maimakon limamai da yawa, alhalin maganar da ake a kan yinta ne cikn jama’a ko limamin xaya ne ko limamai da yawa ne.
Mulahaza ta biyu; tabbas ma’anar maganarsa akwai hukunce-hukuncen da ba a sunnata su matuqar Annabi na raye saboda wasu dalilai, kamar tsoron wajabta musu sallar, amma xaixaikun mtuane suna da damar shar’anta su bayan mutuwar Annabi (s.a.w), ma’anar hakan shi ne buxe qofar shar’antawa sanadiyyar wasu, kevantattun dalilai har zuwa ranar qiyama, wannan masifa ce wacce bayanta ba wata masifa da wasa da Addini da buxe qofar tumvuke Addini.
HASASHE DON GUJEWA AIBIN BIDI’A
Daga nan ne bbas ina ganin da zan sa su a qarqashin Liman xaya da ya fi... madalla da wannan bidi’ar”.( )
Ko da wannan ba ta zama bidi’a ba duk da cewarsa: Ina ganin, da maganarsa da ya faxa a fili: Madalla da bidi’ar, to meye bidi’ar kenan?!
Idan wanda ya farar da tarawihi tun a farko kamar yadda Ibnu Abdil Barri ya faxa a Isti’ab da Suyuxi a cikin Tarikhul Khulafa da Muhammad bn Shihna a cikin Raudatul Manazir kamar yadda bayani ya gabata ba – xan bidi’a ba ne to waye xan bidi’a kenan.
Daga nan ne yunqurin fitar da sallar Tarawihi daga da’irar bidi’a ya bayyana da qoqarin shigar da ita cikin da’irar sunna, da fassara kalmomin Umar "Madalla da wannan bidi’ar” ta yadda ya zama tana savawa zahirinta, yanzu zamu faxi waxannan yunqure-yunquren da aka yi ga su:
1- Yunqurin da Ibnu Abil Hadid Al-Mu’utazili ya yi inda ya ce: Lafazin bidi’a yana da ma’ana biyu; a-: Abin da ya savawa littafin ALlah da Sunna, misalin Azumin ranar Babbar Sallah da ranakun yanyana nama, tabbas ko da za a ce masa azumi amma sai dai Shari’a ta hana. b-: Abin da nassi bai zo a kansa ba, nassi ya yi shirin bai yi magana a kansa ba, sai Musulmai suka yi shi bayan rasuwar Annabi (s.a.w).
Idan ana nufin cewa sallar tarawihi bidi’a ce da ma’anar farko, to ba za mu yarda da irin wannan tafsirin ba. maganar Umar: Tabbas bidi’a ce Hadisin ne da aka ruwaito kuma mashahuri, sai dai yana nufin bidi’a ce da tafsirin na biyu.( )
Ina ma dai ya kawo maganarsa kawai, ba tare da ya bayyana abin da ya qudurce ba, tabbas ma’anar farko ba ta cikin bidi’a, lallai savawa Qur’ani da Hadisi ba a ce masa bidi’a, ai sunansa ijtihadi maimakon bin nassi, don haka ma’anar bidi’a ta kevanta ne da ma’ana ta biyun da ya kawo, abin da ya ce: Tabbas kalmar da Umar ya faxa ita ce, domin bidi’a ita ce abin da aka qaga ba tare da an kwata ba, sallar Asham ma tana cikinta.
Bidi’a ba ita ce abin da aka qago shi a bisa yanayin da ya savawa wanda ya gabace shi ba, ballantana a ce bidi’a ita ce savawa littafin ALlah da Sunna.
Sannan a shafi na gaba ya ce: Shin bai halatta mutum ya qirqiro nafilfilin salloli kevantattu da wata kevantacciyar kaifiyya ba da adadin raka’p’in da aka kevance, hakan ba zai zama makaruhu ba, ba kuma zai zama haramun ba? tabbas ya shiga cikin abin da ya game ruwayar da ta zo a kan falalar Sallar nafila, sallar tarawihi ta halatta kuma Sunna ce, domin ta shiga cikin abin da ya zo na falalar Sallar Jama’a.
Ban san a kan wacce mazhabar Fiqhu yake wannan maganar ba?! Abin da Musulmai suka sani shi ne ibadojin wajibi da na mustahabbi shari’a ce ta ke faxan yadda ake yinsu, tabbas ma’anar ibada ta dogara ne a kan samuwar umarnin shari’a, idan umarnin shari’a ya tabbata a kan wajibci ko mustahabbanci, to abin da aka bada umarninsa ya zama ibada, in kuwa ba haka ba to bai zama ibada ba, umarnin shari’a yana shiga cikin asalin ibada da shakalinta da kamanninta.
Sai yadda shari’a ta tsayar da mutane a kai, asalinta da shakalinta da kamanninta, kamar yadda ba mutum ba shi da haqqin shar’anta asalin ibada ayyananniya, to haka ma ba shi da damar shar’anta kamanninta da shakalinta. Akwai tsammanin Ibnu Abil Hadid yana ganin cewa umarnin yin sallar nafila da abin da ya zo a kan falalar sallar jam’i sun isa su tabbatar da salla mai shakalin da bawa ya qirqiro, al’amarin ba haka ba ne, tabbas Hadisan falalar nafila da Hadisan falalar jam’i suna nuna ibadu ne masu kevantattun kamanni da suka gangaro daga wajen Annabi (s.a.w), kuma ake son Muminai su yi su kamar yadda Annabi (s.a.w) ya sunnata su.
Dakta Qardawi ya yi magana kan cewa ba a gaban kai a ibadu:
Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya ce: Tabbas ba yi suna yin maganganu ko ayyukan ibada kala biyu; Ibadun da addininsu yake gyaruwa da su, da al’adun da suke buqatarsu a duniyarsu, don haka ta hanyar bibiyar tushen shari’a za mu gane ibadun da Alah ya wajabta, ko yake son su umarni baya tabbata da su sai da shari’a, amman al’adu su ne abin da mutane suka saba yinsu a duniyarsu a cikin abin da suke buqata. Asali dai ba haramci sai abin da Allah (SWT) ya hana, hakan kuwa saboda umarni da hani sune shari’ar ALlah, ibada kuma ba makawa dole sai an yi umarni a kanta, duk abin da bai tabbata a nyi umarni a kansa ba, to ya za a yi hukuncin cewa an hana yinsa?
Don haka ne ma Ahmad da waninsa cikin malaman Fiqhu ma’abota Hadisi suke cewa: Tabbas asalin ibadu dai ba a yin gaban kai, ba a shar’antawa sai abin da Allah ya shar’anta, in ba haka ba, zai zama an shiga cikin ma’anar faxin Allah (SWT): (Ko suna da abokan tarayya ne da suka shar’anta musu abin da Allah bai yi umarni da shi a cikin Addini ba) ]( ).

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: