bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:08:01
Kur’ani a lugga yana nufin karatu, Allah (s.w.t) yana cewa; “Idan muka karanta shi sai ka bi karatunsa”. Kur’ani; shi zance ne kuma littafi na Allah mai gajiyarwa ga wani ya zo da shi da Allah ya saukar da shi wahayi ga annabi (s.a.w) ta hannun Jibril (a.s) wanda aka rubuta a littafin mus’haf, da ya tabbata ta hanyar labarai mutawatirai wadanda ba yadda za a yi su zama karya, wanda kuma aka sanya karanta shi bauta ne ga Allah”.
Lambar Labari: 2
Mene ne kur’ani

Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zaba
B'arna ba ta zo masa daga gaba gareshi, kuma ba ta zo masa daga baya gareshi, Saukarwa ne daga Mai hikima Godadde .

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Ubangiji madaukaki ya ce: "Wannan kur’ani yana shiryar wa zuwa ga wacce ita ce mafi daidaito kuma yana yi wa muminai albishir…” .
Allah ya yi gaskiya, lallai wannan littafi ne wanda yake shiryarwa zuwa ga tafarki mafi daidaito, kuma hanya mafificiya a rayuwar mutum, yana kuma albishir ga muminai ga rayuwa mai sa’ada a nan gaba matukar sun tabbata a kan tafarkin daidai, kuma shi bishara ne na rayuwa madaukakiya, kamar yadda yake waraka ne ga cututtukan zuciya da dukkan abin da warwararsa ta yi wahala a rayuwa matukar sun koma zuwa ga littafin sun kuma kama gefensa mai tsarki.
Hakika kur’ani maganar Allah ce, wanda ya saukar da shi a kan manzonsa amintacce domin karfafar annabtar sa, kuma ambato, da waraka, da haske ga talikai, kuma madogara ta farko na shari’a gun musulmi.
Kur’ani littafi ne na duniya mai ilimi cikakke dawwamamme ga kowane dan Adam da zamani da wuri, kuma shi mai shiryarwa ne ga tafarki madaidaici. 
Kur’ani littafi ne da Allah ya saukar da shi domin amfana daga gareshi a hukunce-hukunce, da akida, da kyawawan dabi’u, da ilimomi daban-daban. A cikinsa akwai bayanin komai, kuma Allah (s.w.t) ya umarce mu da karanta shi, ta yadda ya ce: 
"Ku karanta abin da ya saukaka daga kur’ani” .
Kuma ya umarce mu da fahimtar ma’anarsa da karanta shi: 
"Shin ba sa ganin kur’ani ne da ya kasance daga wanin Allah da sun samu sabani mai yawa daga gareshi”. Nisa’i: 82.
"Ko kuma ka dada a kansa ka kuma karanta kur’ani karantawa”. Muzammil: 4.
Haka nan ya umarce mu da karanta shi da koyar da shi, da koyonsa, da kiyaye shi, da riko da shi, kamar yadda ya zo a hadisi sahihi mutawatiri: 
"Ni na bar muka nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana (a.s), matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba har abada”.
Sai dai mu abin takaici da muke gani yau shi ne yadda jama’a ta kauracewa kur’ani mai girma kamar yadda ya ke a wannan aya mai girma: 
Fadinsa mai girma: "Ya ubangiji hakika mutanena sun riki wannan kur’ani abin kauracewa”. Al-furkan: 30.
Sai kur’ani ya zama yana kai kukan mutane kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (a.s) ce: "Uku suna kai kara wajan Allah, masallaci da aka bari ba a salla a ciki, da malami tsakanin jahilai, da littafin da aka rataye har kura ta fada a kansa ba a karanta shi” .
Saboda haka yana daga larura kwarai mu zage damtse, mu rubuta littafi da zai sa mutane su karkata zuwa ga kur’ani da sunayensa da siffofinsa, da muhimmancin karanta shi, da ladan wanda ya karantar da shi da hardace shi, da fahimtar ma’anar kalmominsa da kiyaye ta.

Mene ne Kur’ani
 Kur’ani a lugga yana nufin karatu, Allah (s.w.t) yana cewa; "Idan muka karanta shi sai ka bi karatunsa”.
Kur’ani; shi zance ne kuma littafi na Allah mai gajiyarwa ga wani ya zo da shi da Allah ya saukar da shi wahayi ga annabi (s.a.w) ta hannun Jibril (a.s) wanda aka rubuta a littafin mus’haf, da ya tabbata ta hanyar labarai mutawatirai wadanda ba yadda za a yi su zama karya, wanda kuma aka sanya karanta shi bauta ne ga Allah”.

Littafi Game-duniya
Kur’ani littafi ne na duniya gaba daya, domin shiryar da halitta, kamar yadda annabtar Muhammad dan Abdullah take ne. Littafi ne da bai kebanta da wani maudu’i na musamman ba, domin littafi ne domin shiryar da dan Adam baki daya.
Babu wani abu da dan Adam yake bukata gare shi da ya shafi kamalarsa da shiriyarsa zuwa ga rabutar duniya da lahira sai da kur’ani ya lamunce magana kan hakan. Littafi ne wanda a cikinsa akwai labarin na farko da na karshe, yana kuma kunshe da:
1. Usuluddin da suke su ne ginshikan addinin musulunci da ya hada da tauhidi, da adalci, da annabci, da imamanci, da ranar lahira. Da kuma sauran mas’aloli kamar kaddara.
2. Tarbiyyar dan Adam da abin da yake yana kunshe da kyawawan dabi’u da tsarkake zuciya.
3. Dokokin shari’a da suke tsara rayuwar mutum da alakarsa a matsayinsa na shi kadai ko na zamantakewar iyali da ta ma’aikatu da kungiyoyi da alakokin da suka shafi kasa-da-kasa, ko tsakanin jama’u mabanbanta.

Dawwamar Kur’ani Mai Girma
Don haka ne muna iya cewa kur’ani shi littafi ne mai dawwama, yana cigaba har karshen zamani, rayayyen ne mai dawwama, kuma a cikinsa akwai bayanin duk abin da zai faru, amma ba mai sanin zurfinsa sai wadanda Allah ya tsarkake su (a.s).
Shi ne ma’aunin gane gaskiya da karya idan an saba, amma mu sani Allah ya yi bayani ta harshen annabinsa cewa Ahlul bait (a.s) su ne masanansa na asali, don haka idan an saba kan ma’anarsa ko manufarsa to abin da suka fada shi ne daidai, domin kur’ani yana da fuskoki daban-daban da zai iya daukar fassara mabanbanta.

Sunayen Kur’ani Da Siffofinsa
1. Sunayen Kur’ani Mai Girma
Allah madaukaki ya ambaci kur’ani a wajaje masu yawa da sunaye kamar haka:
1. Al’kur’ani
2. Alkitab
3. Alfurkani
4. Azzikr

2. Siffofin Kur’ani Mai Girma
1. Shiriya
2. Bayani
3. Gaskiya
4. Wa’azi
5. Haske
6. Abin da Allah Ya Nuna Wa Manzo
7. Waraka
8. Mafi Kyawon Zance
9. Bishara
10. Gargadi
11. Madaukaki
12. Barna Ba Ta Zo Masa
13. Basira
14. Mai Daukaka
15. Mai Daraja
16. Mai Girma
17. Warakar Kiraza
18. Mafi Gaskiyar Zance
A bisa hakika siffofin suna da dama kwarai sai dai mun takaita da wannan.

Fa’idojin Kur’ani
1. Kur’ani Dalilin Annabta
Daya daga fa’idojin kur’ani da ba ta da misali ita ce kasancewarsa dalili ne a kan annabtar manzo (s.a.w) domin hankali yana rusunawa a gaban wannan hakika ta kur’ani mai girma, kuma gaskiya da ba a iya guje mata.
Da yawa daga dalilan annabatar annabawan da suka gabata sun bice, ba domin komai ba sai don kasancewarsu sun takaita da wannan zamunan nasu ne, kamar sandar Musa (a.s) da taguwar Salihu (a.s). Amma mu’ujizar cikamakon annabawa (s.a.w) tana nan har karshen duniya da karewarta.
Kur’ani mu’ujiza ce babba domin 
1- Ya gajiyar da dukkan hankula su zo da kamarsa a fasaha, da hikima, da ilimi, da rashin karo da juna, da kuma rashin kosarwa.
2- Ya dawwama har yau ba tare da wani mai iya soke shi ba, ko kuma zuwa da wani kuskure da ya gano a cikinsa ba.
3- Ilimin yau ya kasa karyata abin da yake cikinsa duk da samun kwarewa a ilimi da cigaban da dan Adam bai taba samun kamarsa ba.
4- Kalubalen da ya yi har yau yana nan, ba tare da wani ya iya amsa wa wannan kulen ba.

2. Kur’ani Shi Ne Madogarar Shari’a Na Farko
Duk wani mai shar’antawa mai hikima dole ya kasance yana da wani kundin tsari da ya dogara da shi, to addinin musulunci da rahamar Allah da ludufinsa ya karfafe shi da mafi girman daukakar kundin tsarin dokoki wanda ya ke shi ne kur’ani da muke magana game da shi. Don haka ne dukkan musulmi suke komawa zuwa gare shi domin sanin hukunce-hukuncen Allah Madaukaki.
Kur’ani ya kunshi dokoki kamar haka: 
1- Dokokin da suka shafi akida da ibada.
2- Dokokin da suka shafi kyawawan dabi’u
3- Dokokin da suka shafi tsarin tafiyar da gida da al’amuran iyali, da kuma auratayya
4- Dokokin da suka shafi tsarawa da tafiyar da daula da alakar kasa-da-kasa
5- Dokokin da suka shafi walwala da arzutar duniya da lahira
6- Dokokin cinikayya da na tattalin arziki
7- Dokokin da suka shafi  tsaro
8- Dokokin da suka shafi  kisasi da na haddi
9- Dokokin da suka shafi tafiyar da al’amuran al’umma 
10- Dokokin da suka shafi likitanci domin shi kur’ani maganin warakar zuciya da badini ne kamar yadda yake magani ga cututtukan zahiri
11- Dokokin da suka shafi sulhu da kulla alkawura da kawancewa
Don haka ne ma ya zama Allah ya dauki nauyin kare shi daga dukkan canji ko gurbata har alkiyama ta tashi.
Gidan da kur’ani yake cikinsa tsari ne daga shaidan mai waswasi. Karanta shi a cikin gidaje yana halarto da mala’iku da yawaita arziki.

3. Kur'ani Mai Ceto Ne
Daga Ishak dan Galibi  ya ce: Abu Abdullah (a.s) ya ce: idan Allah ya tara mutanen farko da na karshe sai wani mutum ya zo mai kyawun fuska, sai muminai su duba ashe Kur'ani ne, sai su ce wannan namu ne, shi ne mafi kyawun abu da muka gani, idan ya je wajensa sai ya tsaya a daman al'arshi, sai Ubangiji ya ce: na rantse da girmana da daukakata! Zan girmama wanda ya girmama ka, kuma in wulakanta wanda ya wulakanta ka" .
Daga abil Jarud ya ce: "Abu Ja'afar ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ni ne farkon wanda zai zo wajen Allah (s.w.t) ranar kiyama da littafinsa da Ahlina (a.s) sannan sai al'ummata, sannan sai a tambaye su me suka yi da littafin Allah da Ahlina (a.s)" .
Daga Annabin karshe (s.a.w) ya ce: " Kur'ani sai ya yi tsammanin za a ba wa wani mutum fiye da abin da za a ba shi to hakika ya wulakanta abin da Allah ya girmama kuma ya girmama abin da Allah ya wulakanta" .
Daga Dalha dan Zaid daga Abu Abdullahi ya ce: "Wannan Kur'ani shi ne manarar shiriya kuma fitilar dare, sai mai neman ganewa ya yaye ganinsa kuma ya bude idanuwansa da kallo, domin tunani shi ne rayuwar zuciyar mai gani kamar yadda mai neman haskakawa yake haskakawa a cikin duhu" .
Daga Sama'ata ya ce: "Abu Abdullah (a.s) ya ce: ya kamata ga  Kur'ani idan ya wuce wata aya mai wata mas'ala ko tsoratarwa ya roki Allah alherin da yake nema kuma ya roki lafiya da kubuta daga wuta da azaba" .
Daga Sakuni daga Abu Abdullah (a.s), daga iyayensa (a.s) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan fitinu suka babaye ku kamar yankin dare mai duhu to sai ku yi riko da Kur'ani domin shi ne mai ceto kuma abin ba wa ceto, wanda ya sanya shi gabansa zai jagorance shi, wanda kuma ya sanya shi a bayansa zai kora shi wuta, kuma shi ne jagora da yake siryarwa zuwa ga alheri kuma littafi ne shi wanda a cikinsa akwai bayanin komai kuma shi ne rarrabewa ba wasa ba ne, kuma yana da zahiri da badini, zahirinsa hukunci ne, kuma badininsa sani ne, kuma zahirinsa da badinsa suna da zurfi, yana da taurari kuma a kan taurarinsa akwai wasu taurarin, kuma ba a iya kirge abubuwan mamakinsa kuma mamakinsa ba ya tsufa, acikinsa akwai fitulun shiriya, kuma manarorin hikima, kuma jagora ne na sani ga wanda ya san siffa.
To sai mai wartsake ganinsa ya bude ganinsa sosai, da shi ne wanda ya gajiya zai kubuta, kuma da shi ne wanda ya wahala zai tsira, hakika tunani rayuwar zuciyar mai gani ne kamar yadda mai neman haskakawa yake tafiya a cikin duhu da haske, sai ku yi riko da kyakkyawar mafita da kuma karancin sauraro" .

Kur'ani Alkawarin Allah
Daga Hariz daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Kur'ani alkawarin Allah ne kan halittarsa don haka ya kamata ga mutum musulmi ya duba alkawarinsa, kuma ya karanta ayoyi hamsin daga gareshi kowace rana" .
Daga zuhuri ya ce: na ji Ali dan Husain (a.s) yana cewa: ayoyin Kur'ani taskoki ne kuma duk sadda aka bude wata taska ya kamata ka duba a bin da yake cikinta" .
Daga Mu'ammar dan khallad daga Ali Rida (a.s) ya ce: na ji shi yana cewa: ya kamata ga mutum idan ya wayi gari ya karanta ayoyi hamsin bayan addu'ar salla" .
Daga Abdul'a'ala bawan aali Samu daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "idan akwai musulmi a gida da yake karanta Kur'ani to yana bayyana ga mutanen da suke sama kamar yadda taurari suke bayyana ga mutanen duniya" .
Daga abul kadah daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: "Imam Ali (a.s) ya ce: gidan da ake karanta Kur'ani kuma ake ambaton Allah mai girma a cikinsa to albarkarsa zata yi yawa kuma shedanu su guje shi kuma ya haskaka ga halittun sama kamar yadda taurari suke ga mutanen kasa, kuma gidan da ba a karanta Kur'ani a cikinsa kuma ba a ambaton Allah to albarkarsa zai ta yi karanci, kuma mala'iku su kaurace masa, shedanu su zo masa" .
Daga Abu Abdullah (a.s) daga babansa ya ce: "ya kasance yana hada mu sai ya umarce mu da ambaton Allah har sai rana ta bullo, sannan sai ya umarce mu da karatun Kur'ani, daga cikinmu akwai mai karantawa, wanda ba ya iya karantawa sai ya umarce shi da ambaton Allah, kuma duk gidan da ake karanta Kur'ani a cikinsa kuma ake ambaton Allah a cikinsa to albarkarsa zata yi yawa" .
Daga Lais dan Abu sulaim (yana dangana sanadinsa zuwa ga Annabi) ya ce: Annabi (s.a.w) ya ce: Ku haskaka gidajenku da karanta Kur'ani kada ku rike su kaburbura kamar yadda Yahudu da Nasara suka yi, suka yi salla a coci da wajen bauta suka bar gidajensu, ku sani idan aka yawaita karanta Kur'ani a cikin gida sai alherinsa ya yawaita kuma ma'abotansa su yalwata kuma ya haskaka ga mutanen sama kamar yadda taurari suke haskaka ga mutanen duniya" .
A cikin Iddatud'da'i ya zo daga Imam Ali Rida (a.s) zuwa ga Annabi (s.a.w) ya ce: "ku sanya wa gidajenku wani kaso na Kur'ani ku sani gidan da ake karanta Kur'ani ma'abotansa zasu yalwata kuma alherinsa zai yawaita kuma mazaunansa zasu dadu, idan kuwa ba a karanta Kur'ani ba sai ya kuntata ga ahlinsa, kuma alherinsa ya karanta, kuma mazaunansa su tawaya" .

Kur'ani Mu'ujizar Manzo Ce Madawwamiya
Kur'ani mu'ujiza ce rayayyiya madawwamiya domin shi littafi ne na sama (saukakke daga Allah) wanda shi kadai ne guda daya wanda Allah ya so ya wanzu cikin kariya daga dadi da ragi da canji duk da yawan masu neman gurbata shi da karya, domin ya kasance kundin tsari dawwamamme ga rayuwar 'yan'Adam har tashin kiyama matukar mutum yana rayuwa a bayan kasa, wannan kuwa saboda abin da yake dauke da shi ne na manyan koyarwa madaukaka wanda aiwatar da su yake samar da rabautar dan Adam da cigabansa.
Kur'ani littafi ne na ilimi da hukunce-hukunce da hakkoki da dokoki da kyawawan halaye da ladubba da siyasa da tattalin arziki kuma shi mu'ujiza ce madawwamiya kuma shi fasaha ne da ya keta fasahar larabawa masu manyan kasidu bakwai da aka rayata su a Ka'aba, ya yi musu kalubale amma suka kasa da zuwa da koda kwatankwacin sura daya ne, sai suka koma suna cire abin da suka rayata a Ka'aba saboda kunya da faduwa kasa warwas da gajiyawarsu a gaban Kur'ani mai girma. Da sun iya zuwa da koda sura daya da ba su dauki makamin yaki ba da zubar da jini wacce ta kashe mutanensu, kuma ta rusa girmansu, ta kawo musu yunwa da firgici da tsoro da kaskanci.
Wannan Kur'ani shi mu'ujiza ne mai tattare da dukkan abin da yake rabauta da jin dadin rayuwa da alheri da albarka, da yada aminci a duniya, kuma dayawa ruwayoyi sun zo game da falalar saninsa da koyonsa da kiyaye shi da aiki da shi da sauransu na daga abubuwan da suke kwadaitar da himmantuwa da shi, kuma mu a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki in Allah ya so.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
12 Rabi’ul awwal 1427 - 22 Parbardin 1385 - 11 Afrilu 2006

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: