bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:16:23
Idan mijin mace ya rasu, tsawon jiran ya danganta ko tana da ciki ko babu, idan ba ta da ciki, dole ta jira tsawon wata huxu da kwana goma. Haka kuma ba a la’akari da balagarta, ko daina hailarta, ko kuma an yi jima’i da ita a auren ko ba a yi ba
Lambar Labari: 203
4. IDDA
Idan mijin mace ya sake ta ko ya mutu, dole ne ta jira na wani qayyadadden lokaci kafin ta qara wani auren.
Idan mijin mace ya rasu, tsawon jiran ya danganta ko tana da ciki ko babu, idan ba ta da ciki, dole ta jira tsawon wata huxu da kwana goma. Haka kuma ba a la’akari da balagarta, ko daina hailarta, ko kuma an yi jima’i da ita a auren ko ba a yi ba, sunna sun tafi a kan cewa idan mace tana da ciki, tsawon iddarta na qarewa ne da zarar ta haife cikin, amma Shi’a sun tabbatar da wajabcin ko dai ta jira tsawon wata huxu da kwana goma ko tsawon lokacin da ta haihu, wanda ya fi tsawo daga biyun (mafi yawan kwanaki daga cikinsu) (أبعدالأجلين). (Ibid, 62 – 63 Riyad 11, 187).  Idan miji ya yi tafiya, sai ya rasu a tafiyar, sunna sun tafi a kan cewa iddarta na farawa daga ranar da ya rasu, amma Shi’a sun tafi a kan cewa iddarta na farawa daga lokacin da ta samu labarin rasuwar. (Sharhul Lum'a 5i 65 – 66 Riyad).
Tsawon lokacin iddar wacce aka saki ya danganta da yanayin da aka yi sakin da kuma ra’ayoyin malaman mazhabobi. Matar da ba a tara da ita ba, bayan da aka yi aure babu idda a kanta. Yarinya ‘yar qasa da shekara tara ba idda a kanta a ra’ayin Hanbali da Shi’a, amma Maliki da Shafi’i sun ce idan har ta yi girman da za a iya jima’i da ita, dole ta yi iddar wata uku; Hanafi kuwa cewa ya yi a kowane irin yanayi iddarta watanni uku ne.
A kowane yanayi dole sai ta yi iddar wata uku. Macen da ba ta haila dole ta yi iddar wata uku a fatawar sunna, amma Shi’a sun tafi a kan babu wata idda a kanta. Matar da take haila kuma ba ta da ciki dole ta yi idda ta tsawon tsarki uku bayan haila (Duhr) a fatawar Shi’a, maliki da shafi’i ko jini uku a fatawar Hanafi da Hanbali. Matar da ta isa yin haila amma ba ta yi ko ta kusa daina haila dole ta yi iddar watanni uku. Matar da take da ciki dole ta jira har sai ta haihu. (Fiqhu, 4, 540 – 52 Sharhul Lum'a 5i, 57 – 65 Riyad 11, 183 - 86).

5.  RANTSUWAR  QIN TAKAR MATA (ILA'I)!
Shi ne namiji ya rantse ba zai qara jima’i da matarsa ba kwata-kwata ko na wani qayyadadden lokaci da ya gota watanni huxu. Tun da shari’a ta hana namiji ya nisanci matarsa a kwanciya na tsawon watanni huxu, in har watanni huxun suka wuce, to tana da damar ta kai qara wajen alqali. Idan ya karya rantsuwar ta sa, to dole ya yi kaffara irin wacce shari’a ta tabbatar ga wanda ya karya rantsuwarsa. Idan kuwa ya dage a kan rantsuwarsa har watanni huxu suka cika, to matar na da damar kaiwa ga alqali domin ta fayyyace matsayin aurenta. Shi kuma alqali, bisa ra’ayin matar, zai umarci mijin ko dai ya koma ga matarsa ko ya raba auren. Idan aka umarci mijin da komawa ga matar amma ya qi, alqali na iya raba auren amma na kome, a nan Shi’a sun sava a kan alqali ba shi da ikon raba auren miji da matar a maimakon miji, sai dai yana da damar ya tilasta mijin, ta hanyar xauri da makamancinsu, don mijin ya zavi xayan biyun da alqali ya ba shi zavi, wato ya komar da ita ko ya sake ta. (Sharhul Lum'a 5i 160; Riyad 11, 123). Hanafi ya ce da zarar rantsuwar mijin ta tabbata, matar ta saku, sakin da ba kome a cikinsa, kuma ba sai mijin ya furta sigar sakin ba.(Fiqhu, 4, 485). Shi’a kuwa sun ce rantsuwar qin takar mace baya tabbata ga wacce ba ta san namiji ba.(Riyad 11, 122). Amma sunna sun qi hakan, sun qara da cewa idan mijin ya sake ta, to saki ne mara kome.

6. ZIHARI
Kafin zuwan musuluci larabawa nada wata xabi’a ta sakin mace da siga kamar haka: (ke a waje na tamkar bayan mahaifiya ta ce) wato sakin mace ta hanyar yin lafazin da zai danganta ta da muharrama, wannan ana kiran sa zihar. Duk da cewa qura’ani ya hana wannan (kur’an 33:4, 58:2). Idan mutum ya furta wannan kalmumi ga matarsa ko makamancisu ta hanyar danganta matarsa da duk wacce aurenta ya haramta gare shi, to matar tasa ta haramta gare shi. Sharuxxan zihar dai-dai suke da na saki, dan haka a Shi’a dole a samu shaidu biyu waxanda suka ji furucin.



Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: