bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:20:32
Sai alqali ya juya ga matarsa. ko dai ta fuskanci hukuncin zina (jefewa da dutse ) ko ta maimaita kalmomin nan sau huxu: (Na ranste da Allah qarya yake)
Lambar Labari: 204
7. LI’ANI
Li’ani shi ne: qin  karvar xan da matarsa ta haifa ko zargin ta, kuma Hanya ce da miji kan dauki matarsa zuwa ga alqali yana zarginta ko dai da barin addinin musuluci ko qin amincewa da zama uba ga xa ko `yar da matarsa ta haifa. Mijin zai furta wannan sigar sau huxu: 'Na rantse da Allah gaskiya na faxa game da abin da na ce a kan wannan matar' sai alqali ya ya ja hankalin mijin yayi qoqarin gamsar da shi hatsarin wannan zargin nasa. Idan ya tuba a kan kalaminsa, sai ayi masa hukuncin qazafi (bulala tamanin (80). Idan ya kafe a kan furucinsa, sai ya sa ke faxin wannan siga sau huxu: (la’anar Allah ta tabbata a kaina idan qarya nake yi).
Sai alqali ya juya ga matarsa. ko dai ta fuskanci hukuncin zina (jefewa da dutse ) ko ta maimaita kalmomin nan sau huxu: (Na ranste da Allah qarya yake). Alqali zai ja hankalita kan hatsarin rantsuwa da Allah a kan qarya. Idan duk da haka ta amince ba ta aikata abin da ya zarge ta ba, sai ta sake faxar waxannan kalmomin masu zuwa sau huxu. (fushin Allah ya tabbata a kaina idan gaskiya ya faxa). Idan kuwa ta qi furta waxannan kalmomi, to sai ta fuskanci hukunci zina.
Bayan waxannan rantse-rantse, mijin da matar sun haramta ga junnansu har abada, ba tare da ya sake ta ba ma. Idan mijin ya qi yarda da zama uban xan/`yar da ta haifa, to `yar ko xan ya zama kamar an haife shi ba tare da aure ba, idan kuwa mutumin ya yarda da hakan (ya janye rantsuwarsa) to dole ne ayi masa hukunci mai tsanani sakamakon qarya kuma xan na sa ne; a wajan `yan sunna kuma; a kan wannan tuba da uban ya yi, uban da ‘yar ko xan za su gaji juna, amma a fadin Shi’a; uban ba zai gaji xan ba. Sannan (duk da tuban da ya yi) har wala yau matar dai ta harmta ga mijin.(Sharhul Lum'a, 5i, 210 – 12, Riyad, 11, 217 – 18).

8. GADO (MIRASI)
Kamar yadda yake a shari'a mata da miji suna gadon juna amma sharaxin gado tsakanin su shi ne auren da suka yi ya zama sun yi shi a kan qa'ida (ingantaccen aure) ba wai kawai saduwar da suka yi ba.
Idan da mace za ta mutu ba tare da ta haihu ba mijinta zai gaji rabin dukiyarta, idan kuma tana da xa ko `ya ko kuma yara mijinta zai gaji xaya bisa huxu (kwata) na dukiyarta; Idan kuma mijin ne ya mutu ya bar matarsa kuma ba shi da xa ko `ya ko yara matarsa za ta gaji xaya bisa huxu (kwata) na dukiyarsa; Idan kuwa yana da xa ko `ya ko yara matar za ta gaji xaya bisa takwas (rabin kwata).  Matar da ta mutu ba ta da kowa (dangi) sai mijinta a nan mijinta zai gaji dukiyarta gaba xaya. Idan kuwa mijin ne ya mutu ba shi da kowa matar za ta gaji rabin dukiyarsa rabin kuma sai a sanya ta a cikin dukiyar musulmai ta gwamnati (baitul mali), amma banda a wajan wasu malamai biyu daga Shi’a domin sun ce matar za ta gaji dukiyar baki xaya.(Sharhul Lum'a, 5ii, 65 – 66 Riyad 11, 366).
Idan kuwa mata ne da shi ba mace xaya ba, za su raba dukiyar a tsakanin su. Mazhabobin sunna gaba xaya sun tafi kan cewa mijin na gadar komai da matarsa ta bari, ita ma macen haka.
Shi’a kuwa sun ce idan ba su haihu ba za ta gaji komai da ya bari amma banda qasa (fili, gona, lambu dss) duk da cewa za ta gaji duk abin da ake samu daga ribar qasa kamar gidaje bishiyoyi da sauran kayan amfani da suke tare da qasa. (Sharhul Lum'a, 5iii, 172 – 74 Riyad 11, 367).
Idan kuwa mace na cikin sakin da ba ta gama idda ba, sai ita ko mijinta wani ya mutu  lamarinsu xaya ne da waxanda suke da aure (yadda muka faxa a baya). Amma da ace sakin da ya yi mata irin sakin da babu kome ne, kuma ba rashin lafiya ce ta raba su ba, to babu gado a tsakaninsu amma idan a lokacin rashin lafiya suka rabu to suna da gadon juna ko da ba sakin kome ne ba. Idan da namiji zai saki matarsa lokacin da yake rashin lafiya sakin da babu kome (wato ba'ini) sai ta mutu kafin ta yi idda ba zai gaji komai daga dukiyarta ba, idan kuwa ace mijin ne ya mutu sakamakon rashin lafiyar, a nan an samu savani tsakanin mazhabobi a kan gadon. Hambaliyya sun ce matar za ta gaji mijin matuqar ba ta qara yin wani auren ba.
Hanafiyyawa sun ce: zata yi gado mutuqar tana cikin idda, malikiyawa sun ce zata yi gado ko da kuwa ta yi wani sabon auren, shafi'iyyawa kuwa suna da magana biyu, ta xaya ba ta da gado, ta biyu kwatankwacin abin da hanafiyyawa suka faxa. Shi'a kuma sun ce zata yi gado cikin shekara guda, idan ba ta yi aure ba. (Sharhul Lum'a, 5iii, 172 Riyad 11, 369).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: