bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:26:17
Sabida irin wannan munanan ayyuka Allah (SW) ya saukar da ayar la'ana ga Abu Lahab har zuwa ranar qiyama
Lambar Labari: 206


سورة المسد
SURATUL LAHAB/MASAD (sura ta 111)
Sura ce muhimmiya da ke nuna mana tarihi, lokacin da Manzo (SAW) ya fara kira zuwa ga imani da kalmatut tauhid, ya samu suka daga mutane daban daban daga ciki har da baffan sa Abi Lahab, domin Abdul Muxxalib ne baban sa (shi Aba Lahab) tarihi ya tabbatar cewa kusan tsara ne a shekaru da Manzo (SAW) da bambanci kaxan, ya na masa hassada sabida zavin da Allah (SW) ya yi masa, ya zamo mai cin dunduniyar Manzo (SAW) da cewa: xan uwa na ne na san shi qarya yake muku da sauran munanan kalamai ga fiyayyen halitta (SAW), bai gushe ba yana wannan cutarwa har sai da cuta ta ta halakar sa shi, haka ma matar sa ta daka ta tasa wacce take daga cikin bani umayya amma (yar uwar uwa) ce ga Mu'awiya, shi kuma Abi lahab xan bani Hashim ne.
Sabida irin wannan munanan ayyuka Allah (SW) ya saukar da ayar la'ana ga Abu Lahab har zuwa ranar qiyama.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
تَبَّتْ يَدَا أَبِي لَهَبٍ وَتَبَّ (1)
Hannayen abu Lahab sun tave shi ma ya halaka.
مَا أَغْنَى عَنْهُ مَالُهُ وَمَا كَسَبَ (2)
Dukiyar sa da abinda ya tara na dukiyar sa ta duniya ba zasu wadatar masa ga komai ba.
سَيَصْلَى نَارًا ذَاتَ لَهَبٍ (3)
Zai shiga wuta mai ruruwa (ma'abociyar balbali).
وَامْرَأَتُهُ حَمَّالَةَ الْحَطَبِ (4)
Da matar sa mai xaukar itace (xaukar itace na nufin annamimanci/gulma a isxilahin larabawan wannan lokaci).
Mai xaukan labarurruka tana yaxawa tsakanin mutane don vatanci ga Manzo (SAW).
فِي جِيدِهَا حَبْلٌ مِنْ مَسَدٍ (5)
A wuyan ta akwai giyar kaba (ma'ana kabar wutar jahannama kamar yadda masu fassara su ka faxa).
Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: