bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:32:03
musulmi sakamakon biyayyarsu ga Manzo shi ne wannan kalma ta “La Ilaha illal-Lah”
Lambar Labari: 208
Tauidi A Ibada Akida Ce Ta Dukkan Musulmi.
Tauhidi da kadaita Ubangiji wani abu ne wanda ya hada dukkan annabawan da Allah ya tayar, domin kuwa dukkansu sun hadu a wajen kira ga wannan kalma guda daya, musamman Annabi Ibrahim (a.s) wanda dukkan addinai manya guda uku suke jingina kansu zuwa gareshi (wato Yahudanci, kiristanci da musulunci).
Sakamakon haka babu wani mutum wanda zai danganta kansa zuwa ga daya daga cikin wadannan addinai face ya yi imani da wannan kalma ta tauhidi, haka nan taken dukkan musulmi sakamakon biyayyarsu ga Manzo shi ne wannan kalma ta "La Ilaha illal-Lah” wato babu wani Ubangiji sai shi Allah madaukaki guda daya, wato shi ne kawai wanda ya cancanci a bauta masa, don haka dole ne kowane mutum ya mika wuyansa domin ibada zuwa gareshi.
Duk da yake musulmai suna da sabani a kan wadansu abubuwa a tsakaninsu, amma a kan wannan kalma dukkansu sun hadu a wuri guda cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah shi kadai, haka nan a da musulmi dukkansu sun tafi a kan imani da ceto daga waliyyan Allah da girmama kaburburansu, saboda haka a nan ba su da sabanin ra’ayi a kan hakan.
Ta haka ne har ya kasance yayin da mahajjata suka je aikin hajji sukan yi tasbaha da kasar kabarin Sayyidina Hamza shugaban shahidai. Haka halin musulmi ya kasance a wancan zamani har zuwa farkon karni na takwas a lokacin da wani mutum mai suna Ahmad Bn Taimiyya ya zo yayin da ya fara fito na fito da wasu akidun da muslmi suke a kai a wannan lokaci, wato yin imani da irin wadannan akidu yakan fitar da mutum daga cikin musulunci zuwa ga shirka. A matsayin misali Ibn Taimiyya ya yi da’awar cewa lallai akwai ceto a gobe kiyama, amma shirka ne mutum ya nemi ceton daga waliyyan Allah a nan duniya.
Saboda haka idan aka biyo mu a nan gaba kadan zamu dauki wadannan akidu na Ibn Taimiyya daya bayan daya mu yi bayani a kansu da matsayin kowane a mahangar Kur’ani da Sunnar Ma’aiki (s.a.w) Amma kafin wannan ba zamu iya boye bakin cikimmu ba a kan cewa Ibn Taimiyya ya zo da wadannan ra’ayoyi nasa ne a lokacin da musulmi suke cikin tsananin bukatuwa zuwa ga hadin kai sakamakon mawuyacin halin da suka samu kansu a cikin hare-haren kiristoci da Magul. Amma abin bakin ciki a wannan lokaci ne Ibn Taimiyya ya zo da irin wadannan ra’ayoyi masu raba kan musulmi.
Bincike a kan tarihin rayuwar Ibn Taimiyya da mawuyacin halin da musulmi suke a wannan lokaci domin daukar darasi a kan abin da ya faru a tarihi yana da muhimmancin gaske.
Farkon karni na hudu zuwa rabin karni na biyar bayan hijira, wani yanki ne mai hadari a cikin tarihin musulunci. A wannan lokaci ne manya-manyan mutane da suka yi wa musulunci aiki suka bayyana, kamar su Ibn Sina da Abu Raihan Biruni da Firdausi da Sahib Bn Ubbad Nizamul mulk Tusi da dai sauransu, wadanda suka taka rawa a fagagen ilimi da dama kamar adabi da abin da ya shafi siyasa da dai sauransu. Wanda sakamakon haka ne suka samu damar bayyanar da cigaban musulunci a idon duniya. Kamar yadda mutanen yammacin duniya suka ambaci wannan zamani da zamanin sake raya ilimi na musulunci.
Amma abin bakin ciki bayan shudewar wannan zamani sai ya kasance duniyar musulmi ta fuskanci rikice-rikicen siyasa da na akida wanda yake cike da duniyar musulmi a yau, sakamkon haka ne kuma aka manta da manyan mutane wadanda suka yi wa addini aiki a tarihin musulunci kuma tauraruwar da ke haskawa ta musulunci ta dushe.
Hadin Kan Kiristoci Da Masu Bautar Gumaka
Yammacin duniya kuwa mabiya addinin kiristanci wadanda ba su manta da cin nasarar musulmai da suka yi a kansu ba a Andulus, da yadda musulunci ya ci gaba a wannan nahiya, sai suka dauki aniyar daukar fansa yayin da suka fahimci cewa musulmi sun samu rauni a tsakaninsu sakamakon rikicin da yake faruwa a tsakaninsu na akida da siyasa. A sakamakon haka ne a shekarun karshen karni na biyar shugabanin cocin katolika da yake a Rom wanda kuma kusan shi ne shugaban kiristocin duniya (wato fof) ya yi umarni da kai wa musulmi hari a palasdin (wanda ita ce alkiblar musulmi ta farko) sakamakon haka ne dubban daruwan kiristocin duniya da suke zaune a yammacin duniya suka yo ca domin amsa kiran wannan shugaban kiristanci na duniya a wannan lokaci wato ya tayar musu da tsohuwar gabarsu da musulunci wanda yake addini na kadaita Allah madaukaki, ta yadda suka mai da Kudus wani wuri na kisan al’ummar musulmi, wato a yakin da ya shahara tsakanin musulmi da kiristoci ya dauki tsawon shekara 200 ana gwabzawa wanda ya janyo kisa da raunata dubban daruruwam al’ummar musulmi. Wannan yaki kuwa ya fara ne daga shekara ta 1095-1291.
Wani babban abin bakin ciki kuma shi ne bayan musulmi ba su warware da abin da suka hadu da shi a yakin Kods tsakaninsu da kiristoci ba sai kuma suka fuskanci wani babban abin bakin ciki da ya dara wannan, wannan karan kuwa Magul da jagorancin Cangiz suka kawo wa al’ummar muslmi hari ta yadda duk wani abin da suka hadu da shi a kasashen musulmi sai sun ga bayansa, ko kuma su kama matsayin bursunan yaki ko kuma a matsayin ganimar yaki. sannan bayan shekara hamsin da yin wannan ne jikan Cangiz mai suna Holako shi ma ya kai wa Bagdad hari wacce take cibiyar musulunci ce a wannan zamani ta yadda ya kashe dubban musulmi a wannan lokaci, a wannan lokaci ne ya kai karshen khalifancin Abbasiyawa, wannan kuwa ya faru ne a shekara ta (656BH) Bayan nan bai tsaya a nan ba kawai sai ya jagoranci rundunarsa zuwa garuruwan sham, wanda ya kai hari a garuwan Halab da Mausil inda ya Maimaita abin da ya yi a Bagdad, wannan kuwa ya faru ne a shekarun (657-660BH) a dai- dai wannan lokaci kuma Misra da Sham suna cikin fuskantar matsananci hare-haren kiristoci ta yadda wani lokaci rundunar kiristoci sukan yi gab da su shiga cikin Alkahira babban birnin Misra. Idan da mutuwar Babban sarki Magul wato Mungokan bai sanya ba Holako ya dawo baya ba zuwa Iran, da kuma shan kashin da kwamanda Holako ya gamu da shi a Palasdin wanda ya Maimaita abin da Jalut ya hadu da shi a Palasdin, to da a wannan lokacin ba a san makomar Misra ba.
Wannan hare-hare na Magul da suka yi ta kai wa duniyar musulmi a farkon karni na bakwai ya bai wa kiristocin yammacin duniya babbar damar da zasu ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Andulus wanda suke cibiyar musulunci a kasashen turai, don haka shekara ta 609-889H suka fara kai hare-harensu a kan Andulus domin mugun nufinsu na shafe duk wata alama ta musulunci a wannan nahiya. Abin da ba zamu wuce ba a nan sai mun tofa albarkacin bakinmu shi ne, a duk tsawon lokacin hukumar Magul, sarakunan kasashen turai sun kasance suna kai da kawo tsakaninsu da masarutar Magul, domin su yi taimakekiniya a kan gamawa da al’ummar musulmi. Bugu da kari ma matar Holako ta kasance kirista ce, haka nan kwamandansa a garuruwan Sham ya kasance kirista ne, wanda wannan yake kara tabbatar mana da taimakekeniya a tsakaninsu a kan gamawa da musulmi.
Haka nan sarakunan Magul wadanda suka gaji Holako duk sun kasance sun bi abin da Holako ya kasance yana yi na yakin musulmi: Aba khakan wanda yake da ne ga shi Holako wanda ya yi zamani a shekara ta (663-670BH) ya kasance ya auri ‘yar sarkin Rom wacce ita ce hedikwatar kiristoci a wannan zamani ta yadda ya hada kansa tare da sarakunan faransa da na Engila domin yaki da musulmi, ta haka ne suka kai hare-hare zuwa Sham da Misra wadanda suke garuruwa ne muhimmai na musulunci a wannan lokaci. Haka nan wanda ya fi Aba khakan muni shi ne dansa mai suna Argun wanda ya yi zamani tsakanin shekaru na (683-690Bh) ta yadda sakamakon shawarar da wazirinsa wanda yake Bayahude ne mai suna Sa’adu daula Abhari ya ba shi shawara a kan ya kai hari Makka ya mayar da dakin ka’aba wurin bautar gumaka, da haka ne ya ci gaba da tube manya-manyan shugabanni na musulmi da kashe wasu daga cikinsu da tanadar runduna wacce zai aiwatar da wannan mugun nufi na shi don ya kai hari zuwa garuruwan Hijaz, Amma abin farin cikin Allah madaukaki bai ba shi damar aiwatar da wannan manufa tasa ba, domin kuwa Argun sai ya kamu da rashin lafiya kuma aka kashe wannan wazirin nasa wanda yake Bayahude ne, da haka ne Allah ya kai karshen wannan fitina tasu.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: