bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:36:02
amana ne ga jama’a mai zuwa, kuma daga cikin kiyaye wannan amana shi ne ka gaya musu cewa irin litattafanka na Sunnanci sun zo da wannan magana
Lambar Labari: 209
An wallafa litattafai masu yawa daga vangaren Sunna da Shi'a litattafai kusan guda ishirin da shida (A’ayanusshi’a, j 3, babul Gadir) kan lamarin Gadir, ba kuma ina son magana game da hadisin Gadir ba ne a nan game da jagorancin Imam Ali (A.S) da kuma shugabantar da shi a kan dukkan sahabbai, domin wannan lamari ne da aka yi bincike masu yawa kansa ta fuskancin masu bincike, sai dai ni a nan ina son tambayar Dakta Ahmad Shalbi ne wanda yake cewa hadisin Gadir bai zo ba sai a litattafan Shi'a, ina mai tambayarsa shin akwai jin wani abu mai nauyi a kansa da ya dame shi ne da yake jin takaicin mas'alar Gadir da ayyana Imam Ali (A.S) a matsayin halifan annabi kuma jagoran musulmi, shi da ire-iren sa na daga waxanda suke jifa da magana a kan iska, ka sani abin da yake kanka wanda ka sani na ilimi kana xauke da amana ne ga jama’a mai zuwa, kuma daga cikin kiyaye wannan amana shi ne ka gaya musu cewa irin litattafanka na Sunnanci sun zo da wannan magana daga madogarar su. Idan ka kasance kuma ba ka karatu ne, ko kuma kana karatu amma ba ka son ka sani to abin da ya fi maka shi ne kai shiru sai Allah ya ragwanta maka fiye da ka yi wannan lamari bisa jahilci ko kuma bisa vangaranci.
Kuma haka nan wanda yake cewa: Maula a wannan hadisi tana nufin xan ammi shi ma kamar Dakta Shalbi yake, domin dogaro da cewa tana daga cikin ma’anonin ta, kuma ni ba zan tsaya yi wa wannan raddi ba, sai dai ina cewa ne: Allah ka kiyaye mana hankulanmu daga shafewa. wannan ba komai ba ne sai xaya daga misalan wuraren da Annabi ya yi nuni da falalar Imam Ali (A.S) kuma waxannan wurare suna da yawa ba tare da sun qarfafa mutane a kan Ali (A.S) ba, kuma ba tare da sun tura su ga sanin cewa shi ne wasiyyin Annabi ba, wanda yake Kur'ani ya sanya shi xaya daga cikin masu shugabanci na gaba xaya bayan Allah da manzon sa. Sannan kuwa ba makawa ne musulmi su yi biyayya ga abin da ya zo musu na ma’anar Shi’anci da muke faxa cewa Annabi (S.A.W) ne farkon wanda ya dasa shukar sa, kuma ya girmama ya yaxu tun a lokacin rayuwar sa, ya yi ‘ya’ya, har ma da wasu mutane da aka san su da shi’ar Ali, waxanda suke a gefen sa, suna masu nuni da shiryarwa a kan hakan, kuma da sannu zamu kawo sunayen na farko daga cikin sahabban da aka san su da Shi’anci da biyayya da miqa jagoranci ga Ali (A.S).
 


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: