bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:38:04
da Jabir xan Abdullahi al’Ansari xayan sahabban bai’ar aqaba, da Hashir xan Abiwaqqas almirqal wanda ya buxe Jalula’, da Muhammad xan Halifa Abubakar xalibin Imam Ali (A.S)
Lambar Labari: 210
Yan Shi'a Na Farko cikin Sahabbai (Musulmai)
Su ne: Jundub xan Junadata, Abuzar algifari, da Ammar xan Yasir, da Salman alfarisi, da Miqdad xan Ammar xan Sa’alaba alkindi, da Huzaifa alyamani ma’abocin sirrin Annabi, da Khuzaima xan Sabit al’Ansari zusshahadatain, da Khabbab xan Arat alkhuza’i xayan waxanda suka sha azaba saboda Allah, da Sa'ad xan Malik, da Abu Sa’idul alkhuduri, da Abul Haisam xan Attihan al’Ansari, da Qais xan Sa'ad xan Ubbada al’Ansari, da Anas xan Alharxan Munbah xayan shahidai Karbala, da Abu Ayyubal Ansari, da khalid xan Zaid wanda Annabi ya nemi baquncinsa yayin da ya shiga Madina, da Jabir xan Abdullahi al’Ansari xayan sahabban bai’ar aqaba, da Hashir xan Abiwaqqas almirqal wanda ya buxe Jalula’, da Muhammad xan Halifa Abubakar xalibin Imam Ali (A.S) kuma xan renonsa, da Malikul Ashtar Annakha’i, da Malik xan Nuwaira wanda Khalid xan Walid ya kashe shi, da albarra’u xan Azib al’Ansari, da Ubayyu xan Ka’abu sayyidul qurr’a’u, da Ubbada bn Samit al’Ansari, da Abdullahi xan Mas’ud ma’abocin ruwan alwalar Manzon Allah (S.A.W) kuma xaya daga shugabannin masu qira’a, da Abul’aswad Addu’uli wato: Zalim xan Umair wanda ya assasa tubalin ilimin nahawu da umarnin Imam Ali (A.S), da Khalid xan Sa'id xan Abi Amir xan Umayya xan Abdusshams na biyar xin wanda ya musulunta, da Usaid xan Sa’alaba al’Ansari daga mutanen Badar, da Al’aswad xan Isa xan Wahab daga mutanen Badar, da Bashir xan Mas’ud al’Ansari daga mutanen Badar kuma daga waxanda aka kashe a waqi’ar yaqin Harra a Madina, da kuma Sabit xan Abu Fudhalatal Ansari daga mutanen Badar, da Haris xan Nu’uman xan Umayya al’Ansari daga mutanen Badar, da Rafi’u xan Khudaij al’Ansari daga shahidan Uhud bai balaga ba, amma Manzon Allah (S.A.W) ya ba shi izini. Da Ka’abu xan Umair xan Ubadatal Ansari daga mutanen Badar, da Sammak xan Kharasha Abu Dujanatal Ansari daga mutanen Badar, da Suhail xan Amrul Ansari daga mutanen Badar, da Atik xan Attihan daga mutanen Badar, da Sabit xan Ubaida al’Ansari daga mutanen Badar, da Sabit xan Huxaim xan Udayyil Ansari daga mutanen Badar, da Suhail xan Hanif al’Ansari daga mutanen Badar, da Abu Mas’ud Uquba xan Amru daga mutanen Badar, da Abu Rafi’i bawan Manzon Allah (S.A.W) wanda ya halarci dukkan yaqoqin Annabi (S.A.W) tare da Imam Ali (A.S), kuma daga waxanda suka yi bai’a biyu ta Aqaba da ta Ridwan kuma ya yi hijira biyu zuwa Habasha tare da Ja’afar da Madina tare da musulmi, da Abu Buraida xan Dinar al’Ansari daga mutanen Badar. Da Abu Umar al’Ansari daga mutanen Badar, da Abu Qatada Alharis xan Rib’i al’Ansari daga mutanen Badar, da Uquba xan Umari xan Sa’alaba al’ansarri daga mutanen Badar, da Qurza xan Ka’abul Ansari, da Basher xan Abdulmunzir al’Ansari xaya daga zavavvun bai’ar Aqaba, da Yazid xan Nuwaira xan Haris al’Ansari daga waxanda suka samu shaidar aljanna daga Annabi (S.A.W) da Sabit xan Abdullahil Ansari, da Jabala xan Sa’alaba al’Ansari, da Jabala xan Umair xan Aus al’Ansari, da Habib xan Badil xan Warqa’ul Khuza’i, da Zaid xan Arqam al’Ansari da ya halarci yaqi goma sha bakwai tare da Annabi (S.A.W), da kuma A’ayun xan Dhabi’a xan Najiya Attamimi, da Asbag xan Nabatat, da Yazid Al’aslami daga ma’abota Bai’ar Ridhwan, da Tamim bn Khuzam, da Sabit xan Dinar Abu Hamza Assumali ma’abocin addu’ar nan shahararriya, da Jundub xan Zuhair al’azdi, da Ja’ada xan Habira almahzumi, da Harisa xan Qudama attamimi, da Jubair xan Janab al’Ansari, da Habib xan Mazahir al’asadi, da Hakim xan Jabala al’abdi allaisi, da Khalid xan Abidujanata al’Ansari da Khalid xan Walid al’Ansari, da Zaid xan Suhan allaisi, da Alhajjaj xan Gariba al’ansari, da Zaid xan shurhabil al’Ansari, da Zaid xan Jibilatal tamimi, da Budail xan War’qa’ al’khuza’I, da abu Usman al’Ansari, da Mas’ud xan Malik al’asadi, da Sa’alaba abu Umratal Ansari, da Abuttufail Amir xan Wa’ila Allaisi, da Abdullahi xan Hizam al’Ansari shahidin Uhud, da Sa'ad xan Mansur assaqafi, da Sa'ad xan Haris xan Samadul Ansari, da Haris xan Umar Ansari, da Sulaiman xan Surad alkhuza’I, da Shurhabil xan Murratal Hamdani, da Shabib xan Rattul Namiri, da Sahal xan Umar ma’abocin Marbad, da Suhail xan Umar xan’uwan Sahal da aka ambata a baya, da Abdrrahaman alkhuza’i, da Abdullahi xan Kharash, da Abdullahi xan Suhail al’Ansari, da Ubaidullahi xan Al’azir, da Udayyi xan Hatim atta’I, da Urwa xan Malik Al’aslami, da Uquba xan Amiris Salami, da Umar xan Hilal Ansari, da Urwa xan Malik Al’aslami, da Uquba xan Amir Salami, da Umar xan Hilal Al’ansari, da Umar xan Ansa xan Aunil Ansari daga ma’abota Badar, da Hindu ‘Yar Abi Hala Al’asadi, da Wahabu xan Abdullahi xan Muslimi xan Junada, da Hani xan Urwa Al’muhiji, da Habira xan Nu’uman Alja’afi, da Yazid xan Qais xan Abdulllahi, da Yazid xan Hurit Al’ansari, da Ya’ala xan Umair Alnahadi, da Anas An Mudrik Alkhas’ami, da Amrul Abdi Allaisi, da Umaira Allaisi, da Alim xan Salma Attamimi, da Umair xan Haris Assalami, da Alba’u xan Alhaisami xan Jarir da Babansa Alhaisam daga jagororinn yaqi a yaqin da aka yi da Farisa a Zi-qar, da Aunu xan Abdullahil Azdi, da Ala’u xan Umar Ansari, da Nahshal xan Dhamratal Hanzali, da Almuhajir xan Khalid Almakhzumi, da Makhnaf xan Sulaim Al’abdi Allaisi, da Muhammad da Umair Attamimi, da Hazim xan Haabi Hazim Annajli, da Ubaid xan Attihan Al’ansari, wanda shi ne farkon wanda ya yi bai'a ga Annabi (S.A.W) a daren Aqaba, da Abu Fudhalatal Ansari, da Uwais Alqarni Al’ansari, da Ziyad xan Nadir Alharis, da Aiwad xan Alax Assulami, da Ma’azu xan Afara’ul Ansari, da Abdullahi xan Sulaim Al’abdi Allaisi, da Ala’u xan Urwatul Azdi, da Alqasim xan Uslaim Ala’bdi Allaisi, da Abdullahi xan Ruqayya Al’abdi Allaisi, da Munqiz xan Nu’uman Al’abdi Allaisi, da Haris xan Hassan Azzuhali, ma’abocin tutar Bakir xan Wa’il, da Bujair xan Dalja, da Ayazid xan Hujjiyya Attamimi, da Amir xan Qais Axxa’i, da Rafi’ul Gaxafani Al’ash’ja’i, da Salim xan Abi Ja’ad, da Ubaidillahi xan Abil Ja’ad, da Ziyad xan Abil Ja’ad, da Abbana xan Sa'id xan Asi xan Umayya xan Abudsshams daga jagororin yaqoqi lokacin Annabi (S.A.W), Kuma Xaya Daga Sahabban Imam Ali (A.S) na musamman, da Harmala xan Al’munzir Atta’i Abu Zubaida, dukkansu xari da talatin da Uku..
Wannan kaxan ke nan ko kuma misali ke nan na wasu daga Shi'a da muka kawo ba tare da wani tacewa ko zava ba, kawai na bi litattafan ilimin Rijal ne (na sanin tarihin majazen ruwayar hadisai) ne sai na kawo waxannan daga ciki, kuma waxannan litattafai masu zuwa sun kawo maganar shi’ancinsu.
Bayan mun lura da wannan jama’a ta farko daga Shi'a wasu lamura masu muhimmanci suna bayyana gare mu cewa a maganarmu wannan da zamu bujuro da ita ne gaban mai karatu wayayye mai bin gaskiya da ilimi. Domin kuwa da yawa a kan samu masu karatu da idanuwansu ba sa iya wuce abin da saxarori suka qunsa. Wani lokaci kuma yakan karanta amma ba ya son ya gaskata abin da yake karantawa tare da cikar sharuxxan ingancin abin da yake karantawa, kuma tare da samun nutsuwar rai ga abin da yake karantawa, sai dai wanil lokaci abin da rai da qwaqwallwa suka ginu a kansa tun yarinta, ta yada yakan kusa zama tamkar wani abu daga xabi’ar da xan’Adam ya tashi a kanta ne, sai ya kasance ya kasa barin abin da ya taso a kansa na aqida.
Bayanin ‘Yan Shi'a Na Farko
Waxannan kalamai da zan kawo zasu qunshi wani bayani ne game da nau’in Shi'a na farko kamar haka:
Na farko: Waxannan Shi'a da muka ambata duk da sun kasance suna ganin lamarin halifanci na Imam Ali (A.S) ne domin shi ne wajibi a yi masa biyayya saboda nassin shari'a gare shi, tare da wannan imanin nasu da cewa duk wanda ya wuce ya sha gabansa to ya xauki abin da ba nasa ba ne, da kuma qin da yawancinsu suka yi na qin bai’a ga halifa na farko da kuma riqonsu ga gidan Imam Ali (A.S) duk da haka ba a samu wani xaya daga cikinsu ya zagi wani daga sahabbai ba, ko kuma ya yi masa wani abu ta hanyar da take ba ta halatta ba, sun kasance ne dai kawai sun dage kan imaninsu da aqidarsu. Ga dukkan alamu lamarin zage-zage ya zo ne sakamakon wasu raddodi kan wasu ayyukan da suka gabata da zamu yi nuni kan haka nan gaba- duk da haka ba su riqi yin zagi ba ga hukumomi ko wata magana ta banza, domin sun san cewa haqqoqi ba sa iya dawo wa ta hanayr zagi, kuma zagi ba ya daga xabi’ar gwaraza, kuma nuna wani zalunci da aka yi ko kuma wani haqqi da aka qwace to wannan ba zagi ba ne, sai dai akwai wasu hanyoyi masu sauqi domin kai wa ga hadafi. Kuma Imam Ali (A.S) ya kwaxaitar da mabiyansa kan wannan tafarki mai sauqi kamar misalin abin da Nasar xan Muzahim ya ruwaito ya na cewa: Imam Ali (A.S) ya wuce wasu sahabbansa da suke tare da shi a cikin rundunar yaqi a Siffain sai ya ji suna zagin Mu’awiya da sahabansa, sai ya ce da xan Udayyi da kuma Umar xan Al’hamqi da wasu mutane: Ina qi muku ku kasance masu la’anta masu zagi, kuna masu zagi kuma masu barranta, amma dai da zaku siffanta ayyukansu munana ku ce: suna yin kaza da kaza, kuma sun aikata kaza da kaza da ya fi kyau, kuma ya fi yanke uzuri, da maimakon la’anar da kuke yi musu da kuma baranta daga gare su zaku ce: "Ya ubangjiji ka kare jininmu da nasu ka gyara tsakaninmu da tsakaninsu, ka shiryar da su daga vatansu har sai wanda ya jahilci gaskiya ya gane ta daga cikinsu, kuma wanda yake kan vata da qiyayya ya tsorata ya bari, da wannan ya fi soyuwa wajena kuma ya fi muku alheri. Sai suka ce: Ya Amirul muminin mun karvi wa’azinka kuma mun tarbiyyantu da ladabinka .
Wannan abu ya nuna mana cewa hanyar zagi hanya ce qasqantacciya ba ta da karimci, sannan kuma tafiyar da qarfi ne a banza da za a iya amfani da shi da kuma juya shi domin wani aiki mai kyau, haxa da cewa zagin ya na kawo muzantawa ga abubuwan da mai zagin yake tsarkakewa, don haka ne ma malamai suka harmta zagin gumaka idan ya kai ga zagin Allah suna masu amfana daga wannan faxin na Allah Maxaukaki:
"Kada ku zagi waxanda suke kiran wasu savanin Allah sai su zagi Allah bisa gaba ba tare da ilimi ba"
Don haka ne ma aka umarci Shi'a da tsarkake harsunansu daga zgin domin wannan ya fi nisantarwa ga mummuna kuma don haka ne ma muka ga da yawa daga masu talifofi masu ilimi suna qarfafa siffantuwar Shi'a na farko da wannan siffa ta gari tare da cewa suna tabbatar da aqidarsu ta fifita Imam Ali (A.S) a kan waninsa, daga cikinsu akwai:
a- Dakta Ahmad Amin:
Yana cewa: Irin wannan matsakaita xin su ne waxanda suke ganin Abubakar da Umar da Usman da dukkan waxanda suka goya musu baya sun yi kuskure domin sun yarda da halifofi ne tare da cewa sun san fifikon Ali (A.S) da kuma cewa ya fi su .
b- Ibn Khaldon ya na cewa:
Wasu jama’a daga sahabbai suna goyon bayan Ali kuma suna ganin shi ya cancanta fiye da waninsa, yayin da aka ba wa waninsa sai suka qi hakan, suka kuma ji takaici sai dai saboda sun riga sun kafu cikin addini da kuma kwaxayinsu a kan haxin kai, ba su daxa a kan haka ba sai ganawa da kuma qyama da jin takaici .
c- Ibn Hajar a littafin Isti’ab:
Yana faxa game da bayanin Ibn Xufail: Amir xan Wasila xan Kinana Allaisi Abux Xufail ya samu shekaru takwas daga rayuwar Annabi (S.A.W) kuma an haife shi a shekarar Uhud kuma ya mutu a shekara ta xari, ya na cewa: Shi ne qarshen wanda ya mutu daga waxanda suka ga Annabi (S.A.W) kuma ya ruwaito kusan hadisai huxu, ya kasance mai son Ali kuma daga sahabbansa a dukkan yaqoqinsa, kuma amintacce ne kuma ya na ganin fifikon shaihaini (Abubakar da Umar) sai dai ya na ganin Ali (A.S) ya fi su .


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: